Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Imam Mahadi (A.S) Allah ya gaggauta bayyanarsa yana cewa: “Kuma Kowane mutum daga cikinku ya yi aiki da abin da zai kusanta da shi zuwa ga soyayyarmu, kuma ya nisanci abin da zai kusantar da shi ga kinmu da fushinmu”(1).

1.Imaninmu Game Da Sani Da Nazari Kan Samuwar Allah

Mun yi imanin cewa saboda baiwar da Allah ya yi mana ta karfin tunani da kuma kyautar hankali, to ya umarce mu da mu yi tunani a kan halittarsa mu kuma yi duba a cikin a alamomin ayyukansa, mu yi la’akari a cikin hikimarsa da kuma kyautata tafiyar da al’amuranSa a ayoyinsa a cikin duniya baki daya da kuma a kawukanmu, Allah Madaukaki yana cewa: “Zamu nuna musu ayoyinmu a sasannin duniya da kuma a kawukansu har sai ya bayyana gare su cewa hakika Shi gaskiya ne”. Surar Fussilat: 53. Kuma Ya zargi masu bin iyayensu -a akida- da fadinsa: “Suka ce mu dai kawai muna bin abin da muka samu iyayenmu a kai ne, ashe koda ma iyayen nasu sun kasance ba su san komai ba”. (Surar Bakara: 170). Kamar kuma yadda ya zargi wadanda suke bin zato kawai da shaci-fadi cikin duhu da cewa: “Ba komai suke bi ba sai zato”. Surar An’am: 116
A hakika mu abin da muke yin imani da shi shi ne cewa; Hankulanmu su ne suke wajabta mana yin tuntuntuni kan halittu da sanin mahallicin duniya, kamar yadda suke wajabta mana yin tunani a kan kiran wanda ya yi da’awar annabta da kuma mu’uijzarsa, kuma bai inganta ba -a hankalce- a yi koyi da wani a cikin wadannan al’amuran komai matsayinsa da darajarsa.
Abin da ya zo a cikin Kur’ani na kwadaitarwa a bisa tuntuntuni da bin ilimi da sani ya zo ne don karfafa wannan `yanci na dabi’ar halitta ta hankali da ra’ayoyin ma’abota hankali suka ginu akansu, ya kuma zo ne don fadakar da mutane abin da aka halitta su a kansa na sani da hankaltuwa da tunani da kuma fadada tunani da fuskantarwa zuwa ga abin da hankula suke hukunci da shi.
Ba daidai ba ne -a irin wannan hali- mutum ya yi wa kansa saki-na-dafe a kan al’amuran Akida, ko kuma ya dogara da wasu mutane masu tarbiyyantarwa kan wata akida ko wasu mutanen daban. Ya wajaba ne a kansa ya karfafa kan yin bincike ya yi tunani ya yi nazari ya yi bincike a kan asasin shika-shikan Akidarsa (2) wadanda ake kira shika-shikan Addini wadanda mafi muhimmancinsu su ne:
1. Kadaita Allah
2. Annabci
3. Adalci
4. Imamanci
5. Tashin kiyama.
Duk wanda ya yi koyi da iyayensa ko kuma wasunsu a imani da wadannan shika-shikan to lalle ya ketare iyaka ya fandare daga hanya madaidaiciya, kuma ba zai taba zama abin yi wa uzuri ba har abada.
A takaice dai mu muna da’awar abubuwa biyu ne:
Na Farko: Wajabcin bincike da neman sani a kan shika-shikan akida, bai halatta ba a yi koyi da wani a cikinsu ba.
Na Biyu: Wannan wajabcin wajabci ne na hankali kafin ya zamanto na shari’a, wato saninsa bai samo asali daga nassosin addini ba duk da ya inganta a karfafe shi da su bayan hankali ya tabbatar da shi. Kuma ba komai ake nufi da ma’anar wajabcin hankali ba sai riskar hankali ga larurar sani da kuma lizimtar yin tunani da kokarin bincike a cikin shika-shikan Addini.

2. Imaninmu Game Da Koyi Da Wani A Rassan Al’amuran Addini

Amma rassan al’amuran Addini su ne hukunce-hukuncen shari’a wadanda suka shafi ayyuka, su bai wajaba ba a yi nazari da ijtihadi a kansu ba, wajibi ne a cikin rassan hukunce-hukucen addini idan ba laruran Addini ne ba ne kamar wajabcin salla, da zakka, da azumi, da hajji, mukallafi ya yi dayan al’amura uku a cikinsu:-
Ko ya yi ijtihadi (3) ya yi bincike a kan dalilan hukunce-hukunce idan yana cikin masu iya yin hakan, ko kuma ya zama mai ihtiyadi idan zai iya yin ihtiyadi(4), Ko kuma ya yi koyi da mujtahidin da ya cika sharudda. Ya kasance wanda zai yi koyi da shi mai hankali ne, Adali, mai kare kansa, mai kiyaye Addininsa, mai saba wa son ransa, mai bin umarnin Ubangijinsa.
Duk wanda ba mujtahidi ba ne, kuma ba mai yin ihtiyadi ba, kuma bai yi koyi da mujtahidin da ya cika sharudda ba, to dukkan ayyukan ibadarsa batattu ne ba za a karba daga gare shi ba, koda kuwa ya yi salla, ya yi azumi, ya yi ibada duk tsawon rayuwarsa, sai dai idan aikinsa ya dace da ra’ayin wanda yake yi wa koyi kuma ya yi sa’ar cewa ya yi aikin nasa ne da nufin bauta ga Allah (S.W.T).

3. Imaninmu Game Da Ijtihadi

Mun yi Imanin cewa: ljtihadi a rassan hukunce-hukuncen shari’a wajibi ne kifa’i (5) da ya doru a kan dukkan musulmi a zamanin boyuwar Imam, wato ya wajaba a kan musulmi a kowane zamani. Sai dai idan wadanda suka wadatar sun dauki nauyin yi, to ya saraya daga kan sauran musulmai, sai su wadatu da wanda ya dauki nauyin yin hakan kuma ya kai ga matsayin ijtihadi kuma ya cika sharuddan, sai su yi koyi da biyayya gareshi, su koma masa a cikin al’amuran hukunce-hukuncen Addininsu.
A kowane zamani wajibi ne musulmi su duba kansu su gani, idan sun sami wanda ya sadaukar da kansa a tsakaninsu ya kai ga matsayin Ijtihadi wanda babu mai samunsa sai mai babban rabo, kuma ya kasance ya cika sharuddan da ya cancanci a yi koyi da shi a dogaro da fatawarsa, sai su wadatu da shi su yi koyin da shi, su koma gare shi domin sanin hukunce-hukuncen Addininsu. Idan kuwa ba su sami wanda yake da wannan matsayin ba to ya wajaba a kan kowane daya daga cikinsu ya kai ga matsayin Ijtihadi, ko kuma su shirya wanda zai dukufa domin kai wa ga wannan matsayi a tsakaninsu, tunda ba zai yiwu ba dukkansu su dukufa domin neman wannan al’amari ko kuma zai yi wahala, Kuma bai halatta ba su yi koyi da wanda ya mutu na daga cikin mujtahidai.
Ijtihadi: Shi ne nazarin dalilan shari’a domin samun sanin hukunce-hukuncen shari’ar da shugaban manzanni (S.A.W.) Ya zo da ita kuma ba ta sakewa ko canzawa da canzawar zamani da kuma halaye.
“Halal din Muhammad (S.A.W) halal ne har zuwa ranar Tashin kiyama, haramun dinsa kuma haramun ne har zuwa ranar Tashin kiyama.
Dalilan shari’a su ne: Kur’ani mai girma, da Sunna, da Ijma’i, da Hankali kamar yadda yake dalla-dalla a littattafan Usulul fikihu.
Samun matsayin Ijtihadi kuwa yana bukatar sani mai yawa da ilimi wandanda ba sa samuwa sai ga wanda ya dage ya yi kokari ya cire nauye-nauyen da suke a kansa ya bayar da kokarinsa domin samunsa.

4. Imaninmu Game Da Mujtahidi

Abin da muka yi imani da shi game da mujtahidi wanda ya cika sharudda cewa shi wakilin Imami (A.S) ne a halin boyuwarsa, kuma mai hukunci, shugaba cikakke, abin da yake ga Imami (A.S) na koma wa zuwa gareshi a al’amura da hukunci a tsakanin mutane yana gare shi kuma duk wanda ya ya yi raddi gareshi tamkar mai raddi ne ga Imam (A.S) wanda kuma ya yi wa imami raddi to ya yi wa Allah, wannan kuwa yana matsayin shirka da Allah ne kamar yadda ya zo a hadisi daga Imam Sadik (A.S).
Shi Mujtahidin da ya cika sharudda ba wai makoma ba ne na mutane a fatawa kawai ba, shi yana da jagoranci na gaba daya, sai a koma zuwa gare shi a hukunci da raba gardama da shari’a, wannan duk yana daga cikin abubuwan da suka kebance shi, bai halatta ba ga wani ya dauki nauyinsu sai da izininsa, kamar yadda bai halatta ba a yi haddi ko ladadtarwa sai da umarninsa da hukuncinsa.
Kuma ana komawa gare shi a kan dukiyoyin da suke hakkokin Imam ne da suka kebance shi. Wannan matsayin ko shugabanci na gaba daya imami ne ya bayar da shi ga mujtahidin da ya cika sharudda domin ya zama wakilinsa mai maye gurbinsa a lokacin fakuwarsa, shi ya sa ma ake cewa da shi “Na’ibin Imam”.

Fasali Na Farko

5. Imaninmu Game Da Ubangiji Madaukaki (S.W.T)

Mun yi imani cewa Allah Madaukaki daya ne makadaici babu wani abu kamarsa, magabaci ne bai gushe ba kuma ba ya gushewa, Shi ne na farko kuma Shi ne na karshe, Masani, Mai hikima, Adali, Rayayye, Mai iko, Mawadaci, Mai ji, Mai gani. Ba a siffanta Shi da abin da ake siffanta halittu da shi, shi ba jiki ba ne, kuma ba sura ba ne, ba jauhar (6) ba ne kuma ba ard (7) ba ne, ba Shi da nauyi ko sako-sako, ba Shi da motsi ko sandarewa, ba Shi da guri ba Shi da zamani kuma ba a nuni zuwa gare Shi, kamar yadda babu kini gare Shi, babu kama, babu kishiya, babu mata gare Shi, babu da, babu abokin tarayya, kuma babu wani tamka gare Shi. Gannai ba sa riskarSa Shi kuwa yana riskar gannai.
Duk wanda ya ce ana kamanta shi da halittarsa, kamar ya suranta fuska gare Shi da hannu da idaniya, ko cewar Yana saukowa zuwa saman duniya, ko yana bayyana ga ‘yan aljanna kamar wata ko kuma makamantan wannan, to yana matsayin wanda ya kafirce da Shi ne wanda ya jahilci hakikanin mahaliccin da ya tsarkaka daga nakasa, kai dukkan abin da muka bambance shi da tunanin kwakwalwarmu da sake-saken zukatanmu a mafi zurfin ma’anarsa, to shi abin halitta ne kamarmu, mai komawa ne zuwa gare mu, kamar yadda ya zo daga Imam Bakir (A.S), mamakin kyawun wannan bayani mai hikima! Mamakin wannan abin nema na ilimi mai zurfi!`.
Haka nan ana kirga duk wanda ya ce yana nuna kansa ga halittunsa ranar kiyama a cikin kafirai (8) koda kuwa ya kore masa kamantuwa da jiki, batun baka ne kawai, kuma irin masu wannan da’awa sun sandare ne a kan zahirin laffuzan Kur’ani ko hadisai, kuma suka karyata hankulansu suka yi watsi da su, suka kuma kasa yin amfani da aiki da zahiri gwargwadon yadda nazari da dalilai da ka’idojin aron kalma, da kuma ka’idojin aron ma’anar kalma suke.

6. Imaninmu Game Da Kadaita Allah (S.W.T)

Mun yi imani cewa ya wajaba a kadaita Allah ta kowace fuska kamar yadda ya wajaba a kadaita shi a zatinSa, kuma mun yi imani da cewa shi kadai ne a zatinsa da wajabcin samuwarsa, kamar yadda muka yi imani da kadaita shi a siffofi da cewa siffofinsa su ne ainihin zatinsa kamar yadda bayani zai zo game da hakan. Mun kuma yi imani da cewa ba shi da kama da shi a siffofinsa, shi a ilimi da kudura ba shi da tamka, a halittawa da arzutawa ba shi da abokin tarayya, a cikin kowace kamala ba shi da kini.
Haka nan wajibi ne a kadaita Shi a bauta, bai halatta a bauta wa waninsa ba ta kowace fuska, kamar yadda bai halatta ba a hada Shi da wani abu a nau’o’in ibada, wajiba ce ko wadda ba wajiba ba, a salla ne ko kuma waninta na daga ibadoji. Duk wanda ya yi shirka ya hada wani da Shi a ibada to Shi Mushiriki ne, kamar wanda yake riya a ibadarsa yake neman kusanci zuwa ga wanin Allah (S.W.T), hukuncinsa da wanda yake bauta wa gumaka daya ne babu bambanci a tsakaninsu.
Amma ziyartar kaburbura da kuma gudanar da bukukuwa ba sa daga cikin nau’in neman kusanci da wanin Allah a ibada kamar yadda wasu daga masu son suka ga tafarkin Shi’a Imamiyya suke rayawa suna masu jahiltar hakikanin al’amarin, shi ba komai ba ne sai wani nau’i na aiki domin samun kusanci zuwa ga Allah (S.W.T) ta hanyar kyawawan ayyuka, kamar neman kusanci gare shi ta hanyar gaishe da maras lafiya, da kai jana’iza, da ziyartar ‘yan’uwa na Addini, da kuma taimakon talaka.
Don zuwa gaishe da maras lafiya Shi a kan kansa kyakkyawan aiki ne wanda mutum kan samu kusanci da Allah ta hanyarsa, ba neman kusanci da maras lafiyar ba ne da zai sanya aikinsa ya zama bauta ga wanin Allah (S.W.T) ko kuma shirka a bautarSa. Haka nan sauran kyawawan ayyuka irin wadannan wadanda suka hada da ziyartar kaburbura, da gudanar da bukukuwa, da kai janaza da kuma ziyartar ‘yan’uwa.
Amma kasancewar ziyartar kaburbura da bukukuwan Addini suna daga kyawawan ayyuka a shari’a wannan al’amari ne da ya tabbata a fikihu, ba nan ne wajan tabbatar da shi ba. Abin da muke so mu yi bayani a nan shi ne; gudanar da irin wadannan ayyuka ba ya daga cikin irin nau’o’in shirka da Allah kamar yadda wasu suke rayawa, ba kuma bautar imamai ba ne, sai dai abin da ake nufi shi ne rayar da al’amuransu, da kuma sabunta tunawa da su, da kuma girmama alamomin Addinin Allah a tare da su “wannan, duk wanda Ya girmama alamomin Addinin Allah to lalle wannan yana daga cikin ayyukan takawar zukata”. Surar Hajj: 32.

7. Imaninmu Game Da Siffofin Ubangiji (S.W.T)

Mun yi imani cewa daga cikin siffofinsa akwai siffofi tabbatattu na hakikanin kamala da ake kira siffofin jamal da kamal, wato kyawu da kamala, kamar ilimi, da iko, da wadata, da nufi, da rayuwa, wadanda suke su ne ainihin zatinSa, su ba siffofi ba ne da suke kari a kan zatinSa, kuma ba komai ne samuwarsu ba sai samuwar zatin Allah, kudurarsa ta fuskacin rayuwarsa ita ce ainihin rayuwarsa, rayuwarsa ita ce kudurarsa, Shi mai kudura ne ta fuskacin kasancewarsa rayayye, kuma rayayye ta fuskacin kasancewarsa mai kudura, babu tagwayantaka (biyuntaka) a siffofinSa da samuwarsa, haka nan yake a sauran siffofinsa na kamala.
Na’am siffofinsa sun sassaba a ma’anoninsu ne ba a hakikaninsu da samuwarsu ba, domin da sun kasance sun sassaba a samuwarsu, da an sami kididdigar ubangiji, kuma da ba a sami kadaitaka ta hakika ga ubangiji ba, wannan kuwa ya saba wa Akidar Tauhidi.
Tabbatattun siffofi na idafa (9) kuwa, kamar halittawa, da arzutawa, da gabatuwa, da kuma samarwa, duk suna komawa ne a bisa hakika zuwa ga siffa guda ta hakika, wato siffar nan ta tsayuwa da al’amuran halittarsa, ita siffa ce guda daya wacce ake fahimtar irin wadannan siffofi daga gareta gwargwadon tasirori da kuma la’akari daban-daban.
Amma siffofin da ake kira salbiyya -korarru- wadanda ake kiransu da siffofin Jalal, dukkansu suna komawa ne zuwa kore abu daya, wato kore kasancewarsa mai yiwuwar samuwa (10) ba wajibin samuwa ba, abin da yake nufin kore jiki, da sura, da motsi, da rashin motsi, da nauyi, da rashin nauyi, da makamantansu, wato dai kore dukkan nakasa. Sannan kuma kore kasancewarsa ba wajibin samuwa ba yana tabbatar da kasancewarsa wajibin samuwa, wajabcin samuwa kuwa yana daga cikin siffofi tabbatattu na kamala, don haka siffofin Jalala korarru a karshe suna komawa ne ga siffofin kamala tabbatattu, Allah (S.W.T) kuwa makadaici ne ta kowace fuska, babu yawantaka a zatinSa, babu kuma hauhawa a hakikaninsa makadaici sidif.
Abin mamaki ba zai kare ba ga maganar wanda yake da ra’ayin cewa siffofi tabbatttu suna komawa ne zuwa ga siffofi salbiyya, saboda ya kasa gane cewa siffofin Allah su ne ainihin zatinsa, sai ya yi tsammanin cewa siffofi tabbatattu suna komawa zuwa korewa ne domin ya samu nutsuwar imani da kadaitakar zati da rashin kididdigarsa, amma sai ya fada cikin abin da yake mafi muni saboda sanya ainihin zati wanda shi ne ainihin samuwa, kuma tsantsar samuwa wanda ba shi da wata nakasa ko wata fuska ta siffar yiwuwar samuwa. Sai ya sanya shi ya zama aininin rashi kuma tsantsar korarre (11), Allah ya kiyayye mu daga tabewar wahamce-wahamce da kuma zamewar duga-dugai.
Kamar yadda mamaki ba ya karewa ga wanda yake da ra’ayin cewa siffofinSa na subutiyya -tabbatattu- kari ne a kan zatinSa, ya yi imani da kididdigar zatin Allah wajibin samuwa, da samuwar ababan tarayya (12) gareshi, ko kuma wannan magana tasa ta kai shi ga imani da hauhawar zatinsa madaukaki.
Shugabanmu Amirul Muminin (A.S) ya ce:
Cikar tsarkake wa gareshi kuwa shi ne kore siffofi (n halitta) gare Shi(13), saboda shaidawar dukkan abin siffantawa cewa ba shi ne siffar ba, da kuma shaidawar kowace siffa cewar ba ita ce abin siffantawar ba, don haka duk wanda ya siffanta Allah (da irin wadancan siffofi) to ya gwama Shi, wanda ya gwama Shi kuwa ya tagwaita Shi, wanda ya tagwaita Shi kuwa ya sanya Shi sassa-sassa, wanda ya sanya shi sassa-sassa kuwa to lalle ya jahilce Shi, wanda kuwa ya jahilce shi zai yi nuni gareshi, duk wanda kuwa ya nuna shi ya iyakance shi, wanda kuwa ya iyakance shi to ya kididdiga shi, wanda ya ce: A cikin me yake? To ya tattaro shi a wani wuri, wanda ya ce: A kan me yake? To ya sanya shi ba ya wani wurin(14).

8. Imaninmu Game Da Adalcin Allah

Mun yi imani cewa yana daga siffofin Allah madaukaki tabbatattu na kamala cewa shi adali ne ba azzalumi ba, ba ya take hakki a shari’arsa ba ya zalunci a hukuncinsa, yana saka wa masu biyayya kuma yana da hakkin hukunta masu sabo, ba ya kallafawa bayinsa abin da ba zasu iya ba, kuma ba ya yi musu ukuba fiye da abin da suka cancanta.
Kuma mun yi imani cewa Ubangiji ba ya barin aikata abu mai kyau matukar ba wani abin da zai hana aikata shi, kuma ba ya aikata mummuna saboda Shi mai kudura ne a kan ya aikata kyakkyawa ko ya bar mummuna, tare da cewa yana da sani game da kyawun kyakkyawa da kuma munin mummuna, da wadatuwarSa ga barin kyakkyawan da kuma aikata mummunan, babu wani kyakkyawan (aiki) da aikata shi zai cutar da Shi balle ya bar shi, babu kuma wani mugun aiki da yake bukatarsa balle ya aikata shi, tare da cewa shi mai hikima ne ba makawa aikinsa ya kasance ya dace da hikima kuma a bisa tsari mafi kamala.
Idan har da zai aikata zalunci da kuma mummunan aiki to da al’amarin hakan ba zai rabu da daya daga cikin surorin nan hudu ba:
1. Ya kasance ya jahilci al’amarin bai san cewa mummuna ba ne.
2. Ko kuma ya kasance ya san da shi amma an tilas ta shi a kan aikata shi, ya kuma gajiya ga barin aikata shi.
3. Ko kuma ya kasance yana sane da shi ba a kuma tilasta shi ya aikata shi ba, bai kuma gajiya ga barin sa ba, sai dai yana bukatar aikatawa.
4. Ko kuma ya kasance yana sane da shi, ba a kuma tilasta shi ba, ba ya kuma bukata gareshi, sai al’amarin ya takaita ke nan a kan cewa aikisa ya zama bisa sha’awa da wasa.
Dukkan wadannan surori sun koru ga Allah domin suna tabbatar da nakasa gare shi, alhali Shi tsantsar kamala ne, saboda haka wajibi ne mu hukunta cewa shi tsarkakke ne daga zalunci da kuma aikata abin da yake mummuna.
Sai dai kuma wasu sashen musulmi sun halatta wa Allah (S.W.T) aikata mummuna, suka halatta cewa zai iya azabtar da masu biyayya, ya kuma shigar da masu sabo aljanna kai hatta kafirai ma, kuma suka halatta cewa yana iya dora wa bayinsa abin da ya fi karfinsu da abin da ba zasu iya ba, tare da haka kuma ya azabtar da su a kan ba su aikata ba. Kuma suka halatta zalunci da danne hakki, da karya da yaudara ga Allah madaukaki, da kuma aikata aikin da babu wata hikima, da manufa, da maslaha, da fa’ida, da hujjar cewa shi: “Ba a tambayar sa a kan abin da yake aikatawa amma su ana tambayar su”. Surar Anbiya: 23.
Da yawa daga cikin irin wadannan da suka suranta Shi a kan wannan Akida tasu batacciya da cewa Shi, Azzalumi ne, Ja’iri, mai wauta, mai wasa, makaryaci, mai yaudara, da yake aikata mummunan aiki yana barin kyakkyawa, Allah ya daukaka ga aikata wadannan abubuwa daukaka mai girma, wannan shi ne kafirci tsantsansa(15).
Kuma Allah Madaukaki yana cewa: “Kuma Allah ba ya nufin zalunci ga bayi”. Surar Mumin: 23. “Kuma Allah ba ya son barna”. Surar Bakara: 31. “Kuma ba mu halitta sammai da kasa da abin da ke tsakaninsu muna masu wasa ba”. Surar Dukhan: 205. “Kuma ban halicci aljani da mutum ba sai don su bauta mini”. Surar Zariyat: 56. Da sauran ayoyi masu girma, tsarki ya tabbata gareka ba ka halicci wannan don barna -rashin manufa- ba

9. Imaninmu Game Da Hawan Hukunci A Kan Baligi

Mun yi imani cewa Allah (S.W.T) ba ya kallafa wa bayinsa aiki sai bayan ya tabbatar musu da hujja a kansu, kuma ba ya kallafa musu sai abin da zasu iya aikatawa, da abin da zasu iya masa, da abin da suka sani, domin yana daga zalunci kallafa aiki ga ajizi, da jahili maras takaitawa wajan neman sani.
Amma shi kuwa Jahili mai takaitawa wajan neman sanin hukunce-hukunce, shi wannan abin tambaya ne wajan Allah, kuma abin yi wa azaba ne a kan takaitawarsa da sakacinsa, domin ya wajaba a kan kowane mutum ya nemi sanin abin da yake bukata gareshi a sanin hukunce-hukuncen shari’a.
Kuma mun yi imani cewa: Babu makawa Allah madaukaki ya kallafa wa bayinsa ayyuka ya kuma sanya musu shari’o’in abin da yake na maslaharsu da alherinsu da rabautarsu ta har abada, ya kuma gargade su ga barin abin da yake akwai barna da cutuwa a kansu da mummunan karshe gare su, koda kuwa ya san cewa su ba zasu bi Shi ba, domin wannan tausasawa ce da kuma rahama ga bayinSa domin su suna jahiltar mafi yawancin maslaharsu da hanyoyin samunta a nan duniya da kuma lahira. Suna kuma jahiltar da yawan abubuwan da zasu jawo musu cutarwa da tabewa, Shi kuwa Ubangiji Shi ne Mai Rahama mai Jin kai, kuma Shi kamala ne tsantsa wanda kuma shi ne ainihin zatinSa da yake mustahili ne ya rabu da shi har abada.
Ba ya janye wannan tausasawa da wannan rahama domin kasancewar bayinsa sun bujire wa bin sa, sun ki bin abubuwan da ya yi umarni da abubuwan da ya hana.

10. Imaninmu Game Da Hukuncin Allah Da Kuma Kaddara

Mujabbira (16) sun tafi a kan cewa Allah (S.W.T) shi ne yake aikata ayyukan halittu, sai ya zamanto ya tilasta mutane a kan aikata sabo duk da haka kuma ya yi musu azaba, kuma ya tilasta su a kan aikata abin da ya yi umarni tare da haka ya ba su lada, domin sun tafi a kan cewa ayyukansu tabbas ayyukanSa ne, ana dai danganta ayyukan ne garesu saboda rangwame domin su ne mahallin ayyukan Ubangiji. Asalin wannan kuwa domin su sun yi inkarin sababi na dabi’a tsakanin abubuwa(17), suna ganin Allah madaukaki ne yake aikata komai bisa hakika.
Sun yi musun wannan sababi ne saboda tsammanin cewa hakan shi ne ma’anar kasancewar Ubangiji mahalicci, wanda ba Shi da abokin tarayya, amma duk wanda yake fadin irin wannan magana ta su kuwa hakika ya danganta zalunci ga Allah, Shi kuwa ya tsarkaka daga hakan.
Mufawwada (18) (kuma sun yi imanin cewa Allah ya sallama ayyuka ne ga halittu, ya janye kudurarsa da hukuncinsa da kuma kaddarawarsa daga gare su, da la’akari da cewa; danganta ayyukan gare shi yana nufin dangata nakasa gare shi ne, kuma halittu suna da nasu sababan na musamman duk da cewa dukkansu suna tukewa ne zuwa sababi guda daya na farko wanda shi ne Allah (S.W.T). Duk wanda yake fadin irin wannan magana ta su kuwa, hakika ya fitar da Allah daga mulkinSa ya kuma yi shirka da shi da halittunSa.
Abin da muka yi imani da shi a nan muna masu biyayya ga abin da ya zo daga lmamanmu tsarkaka da suke cewa al’amari ne tsakanin al’amura biyu, al’amarin da irin wadannan masu jayayya daga malaman ilimin sanin Allah suka kasa fahimtarsa, wasu kuma suka takaita, wasu kuma suka zurfafa, babu wani daga cikin masana ilimi da ma’abuta falsafa da ya fahimce shi sai bayan karnoni masu yawa.
Ba abin mamaki ba ne ga wanda bai tsinkayi hikimar Imamai (A.S) dangane da al’amari tsakanin al’amura biyu ba, ya yi tsammanin cewa wannan magana ta al’amari ne tsakanin al’umara biyu tana daga abin da malaman falsafa na turai na wannan zamani suka gano, alhali kuwa Imamanmu sun rigaye su tun kafin karnoni goma da suka wuce.
Imam Sadik (A.S) ya fada yana mai bayanin hanyar nan matsakaiciya da cewa: “Babu Tilastawa kuma babu fawwalawa sai dai al’amari ne tsakanin al’amuran guda biyu.
Wannan kalma ta girmama! ma’anarta ta zurfafa! A takaice abin nufi shi ne; hakika ayyukanmu a bangare guda ayyukanmu ne bisa hakika kuma mu ne sababinsu na dabi’a kuma suna karkashin ikonmu da zabinmu, a daya bangaren kuma suna karkashin kudurar Allah ne kuma suna cikin karkashin mulkinsa, domin Shi ne mai ba da samuwa mai bayar da ita, bai tilasta mu a kan ayyuka ba ballantana ya zama ya zalunce mu idan ya yi mana azaba a kan sabo, domin muna da iko da kuma zabi a kan abin da muke aikatawa. Kuma bai fawwala mana samar da ayyukanmu ba ballantana ya zamanto ya fitar da su daga karkashin ikonsa ba, al’amarin halittawa da hukuntawa da umarni duka nasa ne, kuma shi mai iko ne a kan komai kuma masani da bayinsa.
Ta kowane hali, imaninmu shi ne hukuncin Allah da kaddarawarsa sirri ne daga asiran Allah (S.W.T) duk wanda ya iya fahimtarsa yadda ya dace ba tare wuce gona da iri ba ko kuma takaitawa ba, to wannan ya yi, in ba haka ba, bai wajaba a kansa ba ya kallafawa kansa fahimta da zurfafawa a cikinsa (19) ba, domin gudun kada ya bata, akidarsa ta lalace, domin wannan yana daga al’amura masu zurfi, kai yana daga mafi zurfin bahasosin falsafa wadanda ba mai gane so sai daidaikun mutane, kuma duga-dugan da yawa daga malaman ilimin akida sun zame, kallafa wa kai fahimtarsa, kallafa wa mutum maras ilimi mai zurfi ne da abin da yake sama da ikonsa.
Saboda haka ya wadatar mutum ya yi Imani da shi a dunkule kawai yana mai biyayya ga fadin Imamai tsarkaka (A.S) cewa; shi wani al’amari ne tsakanin al’amura biyu, babu tilastawa babu kuma fawwalawa a cikinsa, kuma shi ba ya daga cikin shika-shikan akida ballantana kudurcewa da shi dalla-dalla da zurfafawa su zama wajibi ko ta halin kaka.

11. Imaninmu Game Da Bada

“Bada” ga mutum; shi ne wani sabon ra’ayi ya bayyana gare shi wanda a da can bai kasance yana da wannan ra’ayin ba, wato ya canja niyyarsa da ya yi a kan wani aiki da ya kasance yana nufin aikata shi domin faruwar wani abu gareshi da zai sanya canji a ra’ayinsa da saninsa, sai ya canja niyya sai ya bar aikata shi bayan da can yana nufin ya aiwatar da shi, wannan kuwa ya faru ne sakamakon jahiltar maslaha da kuma yin nadama a kan abin da ya gabata.
“Bada” da wannan ma’anar mustahili ne ga Allah (S.W.T) domin kuwa yana daga jahilci ne da nakasa, wannan kuwa ya koru ga Ubangiji, kuma Shi’a Imamiyya ba su yarda da shi ba. Imam Sadik (A.S) ya ce: “Wanda ya yi da’awar cewa canji cikin wani abu ya faru ga Allah (S.W.T) game da wani abu canji irin na nadama, to a gurinmu wannan ya kafirta da Allah mai girma”. Kuma ya ce: “Wanda ya raya cewa wani abu na canjin ra’ayi ya faru ga Allah wanda ya kasance bai san shi ba jiya to ka barranta daga gareshi”.
Sai dai kuma akwai wasu hadisai da aka ruwaito daga Imamanmu wadanda suke kusan nuni da ma’anar “Bada” kamar yadda ta gabata, kamar yadda ya zo daga Imam Sadik (A.S) cewa: “Wani abu bai taba bayyana ba ga Allah kamar yadda ya bayyana gareshi game da Isma’ila dana”. Don haka ne wadansu daga marubutan musulmi suka danganta Bada ga Shi’a Imamiyya da waccan ma’ana domin suka ga mazhaba kuma tafarki na Ahlul Baiti (AS), suka sanya wannan daya daga abubuwan da suke suka da aibata shi’a da shi.
Sahihiyar magana a nan ita ce, mu muna fadi kamar yadda ubangiji ya fada a littafinsa ne cewa: “Allah yana shafe abin da ya so kuma yana tabbarwa kuma Ummul kitab a gunsa take ”. Surar Ra’ad: 39.
Abin nufi shi ne cewa Allah (S.W.T) na iya bayyanar da wani abu ta harshen Annabinsa ko waliyyinSa ko kuma a zahiri saboda wata maslaha da ta sanya bayyanawar, sa’annan daga baya sai ya shafe shi ya zama ba abin da ya bayyana da farko ba, kamar yadda ya faru a kissar Annabi Isma’il (A.S) yayin da mahaifinsa Annabi Ibrahim (A.S) Ya ga yana yanka shi a mafarki. A nan sai ma’anar maganar Imam Sadik (A.S) ta zama cewa: Babu wani abu da ya bayyana ga Allah (S.W.T) a kan wani abu kamar yadda ya bayyana gare shi a kan Isma’ila dansa yayin da ya dauki ransa kafin rasuwar Imam Sadik (A.S) domin mutane su san cewa shi Isma’ila ba Imami ba ne, bayan a zahiri ya riga ya bayyana cewa shi ne Imami bayansa saboda shi ne babban dansa.
Wani abu da yake kusa da ma’anar “Bada” shi ne shafe hukunce-hukuncen shari’o’in da suka gabata da shari’ar Annabinmu Muhammadu (S.A.W) da kuma shafe wasu daga cikin hukunce-hukuncen da Annabinmu (S.A.W) ya zo da su.

12. Imaninmu Game Da Hukunce-Hukuncen Addini

Mun yi imani cewa Ubangiji ya sanya hukunce-hukunce wajibai da haram da sauransu daidai da maslaha da alheri ga bayinSa a cikin ayyukansu, abin da maslaharsa ta zama tilas sai ya sanya shi wajibi, wanda kuma cutarwar da take tare da shi ta kai matuka sai ya haramta shi, wanda kuwa maslaharsa a garemu ta zama mai rinjaye ya soyar da shi - mustahabbi- a garemu.
Wannan kuwa yana daga adalcinsa da kuma tausasawarsa ga bayinsa, kuma babu makawa ya zamanto yana da hukunci a kan kowane al’amari, babu wani abu daga cikin abubuwa da zai zamanto ba shi da hukuncin Allah a kansa koda kuwa hanyar saninsa ta toshe garemu. Kuma hakika yana daga mummuna ya zama ya yi umarni da abin da yake akwai barna a cikinsa, ko kuma ya hana abin da yake akwai maslaha a cikinsa. Sai dai wasu daga daga cikin musulmi suna cewa: Mummunan abu shi ne abin da Ubangiji ya hana kawai, kyakkyawa kuwa shi ne abin da ya yi umarni da shi, babu wata maslaha ko cutuwa a cikin ayyukan su a kan-kansu, wannan magana kuwa ta saba wa hukuncin hankali.
Kamar yadda suka halatta wa Allah ya aikata mummuna ya yi umarni da abu wanda akwai cutarwa a cikinsa, kuma ya hana abin da yake akwai maslaha a cikinsa. Hakika ya gabata cewa wannan magana akwai ketare iyaka mai girma a cikinta, ba domin komai ba sai domin lizimta danganta jahilci da gazawa ga Allah (T.A.U.K).
A takaice dai abin da yake ingantacce a yi imani da shi, shi ne : Ubangiji madaukaki ba shi da wata maslaha ko amfani a cikin kallafa mana wajibai da hana mu aikata haram, maslahar wannan duk tana komawa zuwa garemu ne, babu wata ma’ana wajen kore maslaha ko barna game da ayyukan da aka yi umarni da su ko hani ga barin su, domin Allah ba ya hani kara zube don wasa, kuma shi mawadaci ne ga barin bayinsa.

Fasali Na Biyu

13. Imaninmu Game Da Annabci

Mun yi imani da cewa annabci aiki ne na Allah kuma jakadanci ne na ubangiji (S.W.T) da yake bayar da shi ga wanda ya so ya kuma zaba daga bayinsa na gari da masoyansa kammalallu a mutumtakarsu, sai ya aika su zuwa ga sauran mutane domin shiryar da su ga abin da yake da amfani da maslaha garesu duniya da lahira, tare kuma da nufin tsaftace su da tsarkake su daga daudar miyagun dabi’u, da munanan al’adu, da koya musu hikima, da ilimi, da bayyana musu hanyoyin rabauta da alheri, domin ‘yan’adamtaka ta kai ga kamalarta da ta dace da ita, ta daukaka zuwa ga daraja madaukakiya a gidajen duniya da lahira.
Kuma mun yi Imani cewa ka’idar tausasawa -kamar yadda bayaninta zai zo- ta wajaba ga Allah mahalicci mai ludufi ga bayinsa, ya aiko manzanninsa ne domin su shiryar da dan Adam, da kuma isar da sakon kawo gyara, kuma su zamanto jakadun Allah kuma halifofinSa. Kamar yadda muka yi imani da cewa Allah madaukaki bai ba wa mutane hakkin ayyana Annabi ba ko tsayar da shi -takara- ko zabensa. Ba su da wani zabi a kan haka, domin al’amarin dukkan wannan yana hannun Allah ne, domin “Shi ne mafi sanin inda zai sanya sakonSa”. Surar An’am Aya ta 124.
Kuma ba su da wani hukunci a kan wanda Allah zai aiko shi a matsayin mai shiryarwa, mai albishir ko mai gargadi, ko kuma su yi hukunci kan abin da ya zo da shi na daga hukunce-hukunce, da sunnoni, da shari’a.

14. Imaninmu Game Da Cewa Annabci Tausasawa Ne

Mutum halitta ne mai iyakoki mai ban al’ajabi, mai sarkafaffun gabobi a halittarsa, da dabi’arsa, da ruhinsa, da kuma hankalinsa, kai hatta ma a kowane daya daga cikin mutane. Dabi’ar fizguwa zuwa ga fasadi sun tattara a cikinsa, kamar yadda dabi’ar motsarwa zuwa ga aikata alheri da gyara suka tattara a cikinsa , ta wata fuskar kuma an halitta shi a kan dabi’u (20) daban-daban kamar son fifita wani a kansa, da sha’awa, kuma an halitta shi a kan son rinjaya da mamayar waninsa, da kwadayin rayuwar dauniya, da adonta, da kawarta, da tarkacenta, kamar yadda Madaukaki yake cewa:
“Hakika mutum yana cikin hasara”. Surar Asri: 2. “Hakika mutum yana dagawa. Don kawai ganin ya wadata”. Surar Kalam:6-7. “Hakika rai mai umarni da mummuna ce”. Surar Yusuf: 53. Da sauran ayoyi makamantan wadannan da suke bayyanawa a sarari da nuni ga irin yadda ran mutum yake kunshe da dabi’u da kuma sha’awa.
Husumar cikin zuciya da take cikin ran mutum ba ta gushewa tsakanin hanakali da dabi’u, duk wanda hankalinsa ya yi galaba a kan dabi’arsa to yana daga cikin mafi kololuwar matsayi masu shiryarwa a ‘yan’adamtakarsu, kuma su ne kammalallu a ruhinsu. Amma wandanda kuwa dabi’arsu ta rinjaye su, to lalle suna daga cikin masu hasarar matsayi, masu ci baya a ‘yan’adamtaka, masu gangarawa zuwa ga matsayin dabbobi.
Mafi tsananin abokan gabar rai su ne zuciya da rundunarta, saboda haka ne muke samun mafi yawancin mutane sun dulmuye a cikin bata, suna nesa da shiriya ta hanyar bin sha’awace-sha’awace da amsa kiran zuciya: “Kuma mafi yawan mutane ba zasu zama muminai ba koda kuwa ka yi kwadayin haka”. Surar Yusuf: 103. Saboda gazawar mutum da rashin tsinkayonsa game da abubuwan da suke kewaye da shi, da asiran abubuwan da suke kewaye da shi, da ma wadanda suke bullowa daga cikinsa shi kansa, ba zai iya sanin dukkan abin da zai cutar da shi ko ya amfane shi ba shi da kansa, kuma ba zai iya sanin abin da zai kai shi ga samun sa’ada ko tsiyacewa ba, shin a kan abin da ya kebantu da shi ne shi kadai, ko kuwa wanda ya shafi ‘yan Adam baki daya da kuma al’ummar da take kewaye da shi. Shi bai gushe ba yana jahiltar kansa kuma yana kara jahilci ko kuma kara gane jahilcinsa duk yayin da iliminsa game da halittu na dabi’a da sauran samammu (21) na binciken ilimi ya karu ba.
Saboda haka mutum a tsananin bukatarsa ta son kai wa ga darajar sa’ada yana bukatar wanda zai dora shi a kan hanya mikakkiya bayyananniya zuwa ga shiriya, domin rundunar hankali ta karfafa da hakan, kuma ya iya yin galaba a kan abokin gabarsa yayin da ya shiga fagen faman gwabzawa tsakanin rundunar hankali da na zuciya. Saudayawa bukatar wanda zai kama hannunsa zuwa ga alheri da gyara tana kara tsananta ne yayin da zuciya take yaudarar sa ta hanyar nuna masa kyawun fandarewarsa, sai ta nuna masa abin da yake mummuna cewa kyakkyawa ne ko kuma kyakkyawa cewa mummuna ne, ta kuma rikita wa hankali tafarkinsa zuwa ga gyara, da sa’ada, da ni’ima, a lokacin da shi ba shi ¬da masaniyar da zai bambance dukkan abin da yake mai kyau mai amfani da kuma wanda yake mummuna mai cutarwa. Koma kowane mutum ya sani cewa yana cikin wadannan gwagwarmayar dauki-ba-dadi ko ya sani ko bai sani ba sai dai wanda Allah ya kare shi.
Saboda haka abu ne mawuyaci ga mutum masanin ilimin zamani ya kai kansa ga dukkan tafarkunan alheri da amfani, da kuma sanin dukkan abin da zai amfane shi ko ya cutar da shi a Duniya da Lahira, ballantana kuma jahili. Al’amarin ya kebance shi ne ko kuma ya shafi al’umma da yake zaune a cikinta ne, kuma ba ya iya kai wa ga wannan masaniyar koda kuwa ya hada kai ya yi taimakekeniya da sauran mutane da ke tare da shi, kuma koda kuwa sun hadu sun yi bincike ko sun yi tarurruka da zama daban-daban da kuma shawarwari.
Don haka ne ya zama wajibi Ubangiji ya aiko da Annabawa da Manzanni a cikin mutane domin rahama da tausasawa gare su. “Manzo daga cikinsu yana karanta musu ayoyinSa yana tsarkake su kuma yana koya musu littafi da hikima”. Surar Juma’a: 2. Domin su yi wa mutane gargadi game da abin da yake da cutarwa gare su, da yi musu albishir da abin da yake da alheri, da gyara, da sa’ada, a gare su.
Tausasawar Allah ga bayinSa wajibi ce domin tana daga cikin tsantsar kamalarSa, shi mai tausasawa ne ga bayinSa, mai yawan baiwa, mai karimci, idan kuwa har ya zamanto a wani guri da ya dace akwai bukatar ya kwarara kyautarSa da tausasawa, to babu makawa ya kwararo tausasawarSa domin babu rowa a farfajiyar rahamarSa, babu tawaya a kyautarSa da karimcinSa.
Ma’anar wajibi a nan ba yana nufin cewa wani zai umarce shi da aikata haka ba, sai ya wajabta a kan Allah madaukaki ya bi shi, Allah ya daukaka ga haka daukaka mai girma! Ma’anar wajibci a nan tana daidai da ma’anar fadinka da kake yi cewa shi wajibin samuwa ne wato ba zai taba yiwuwa a kore masa samuwa ko a raba shi da ita ba.

15. Imaninmu Game Da Mu’ujizar Annabawa

Mun yi imani da cewa yayin da Ubangiji (S.W.T) yake sanya wa bayinsa mai shiryarwa ko manzo, to babu makawa ya sanar da shi gare su ya kuma nuna musu shi a ayyane. Wannan kuwa ya takaita ne a kan sanya musu wani dalili da kuma kafa musu hujja a sakon domin cika tausasawarsa da kuma kammala rahamarsa. Kuma wannan dalilin dole ya kasance ya zo daga mahaliccin halittu mai juya al’amuran samammu , wato ya zama abin da ya gagari kudurar dan Adam, sai ya sanya shi a hannun shi Manzon mai shiryarwa domin a san shi da shi, kuma mai shiryarwa zuwa gare shi, wannan dalili shi ake kira mu’ujiza saboda kasancewarsa ya gagari dan Adam ya gudanar da irinsa, ko kuma ya zo da misalinsa.
Kamar yadda babu makawa ga Annabi ya zo da mu’ujiza ya bayyana ta ga mutane domin ya kafa musu hujja, haka nan babu makawa wannan mu’ujizar ya bayyanar da ita ta yadda za ta gagari malamai da kuma kwararrun zamaninsa ballantana sauran mutane, tare kuma da danganta wannan mu’ujizar da da’awar Annabci daga shi mai mu’ujizar saboda ta kasance dalili a kan da’awarsa.
Idan irin wadancan kwararru suka gaza zuwa da irinta sai a sani cewa ta fi karfin ikon dan Adam, kuma ta keta al’ada, daga nan sai a san cewa ma’abocinta yana sama da kudurar dan Adam, kuma yana da alaka da mai juya al’amuran samammu. Idan wannan ya tabbata ga mutum -bayyanar mu’ujiza wadda ta saba wa al’ada- ya kuma yi da’awar Annabci da sako, to sai ya zamanto abin gaskatawar mutane ga kiran da yake yi tare da yin imani da sakon nasa da bin maganarsa da umarninsa, sai wanda zai gaskata shi ya yi imani da manzancinsa da kaskan da kai ga umarninsa, wanda zai yi imani da shi ya yi, wanda kuma zai kafirce masa ya kafirce.
Wannan shi ne abin da ya sa muka ga cewa mu’ujizar kowane Annabi ta dace da abin da ya shahara a zamaninsa na ilimi da fasaha, mu’ujizar Annabi Musa ita ce sanda wanda take hadiye sihiri da abin da suke yin baduhunsa saboda kacancewar sihiri a zamaninsa shi ne fannin fasaha da yake mashahuri, yayin da sandan ya zo sai dukan abin da suke aikatawa ya baci, suka san cewa wannan abu ya fi karfinsu, kuma yana saman fannin fasaharsu, kuma dan Adam ya gajiya ya kawo shi, kuma kwarewa da ilimi sun gajiya a gabansa(22).
Haka nan mu’ujizar Annabi Isa (A.S) ita ce warkar da makafi da masu baras, da rayar da matattu, saboda shi ya zo ne a lokacin da likitanci ne yake ya yadu a tsakanin mutane, kuma akwai malamai likitoci da suke da kwarewa mai girma, sai iliminsu ya kasa gogayya da abin da Isa (A.S) ya zo da shi(23).
Mu’ujizar Annabinmu madawwamiya ita ce Kur’ani mai girma mai gajiyarwa -ga waninsa na daga fasahohi- da balagarsa da fasaharsa a lokacin da balagar magana ta kasance ita ce fanni sananne, ma’abota ilimin balaga da azancin magana su ne kan gaba a tsakanin mutane da kyawun bayaninsu da daukakar fasaharsu, sai Kur’ani ya zo musu kamar tsawa, ya dimautar da su, ya fahimtar da su cewa su ba zasu iya fito na fito da shi ba. Don haka suka sallama masa rinjayayyu bayan sun gaza gasa da shi, suka ma gaza isa ga kurar da ya tile su da ita ya wuce ya bar su(24).
Ya kuma kalubalance su da su kawo sura goma suka kasa, yayin da muka ga sun gajiya sai muka ga sun koma fada da shi da takobi maimakon harshe, sai muka san cewa lallai Kur’ani wani abu ne na mu’jiza da ya zo daga Muhammad dan Abdullahi hade da da’awar manzanci, sai muka san cewa ya zo ne da gaskiya kuma ya gasgata shi.

16. Imaninmu Game Da Ismar (25) Annabawa

Kuma mun yi imani da cewa Annabawa ma’asumai ne dukkaninsu, haka nan Imamai (A.S), sai dai mun saba da wasu daga cikin musulmi a kan haka don su ba su wajabta isma ga Annabawa ballantana ga Imamai (A.S).
Isma: lta ce tsarkaka daga aikata zunubi da sabo kananansu da manyansu da kuma kubuta da tsarkaka daga mantuwa koda kuwa hankali bai kore aukuwar haka daga Annabi ba, kuma wajibi ne ya tsarkaka hatta daga dukkan abin da yake zubar da mutunci kamar cin abu a kwararo a tsakanin mutane, ko kuma kyalkyala dariya da sauti mai girma, da dukkan aikin da ake munana yin sa a tsakanin mutane.
Dalilin da ya sa Isma ta zama wajibi shi ne: Da ya halatta ga Annabi ya aikata sabo, ko kuma ya yi kuskure, ko ya yi mantuwa, ko kuma wani abu makamancin wannan ya auku daga gare shi, da sai ya zamanto imma dai ya wajaba a yi masa biyayya a aikin da ya yi na sabo ko kuskure, ko kuwa bai wajaba ba, idan har ya wajaba to da mun halatta aikata sabo da dogaro da rangwame daga Allah, kai mun wajabta ne ma, wannan kuwa abu ne batacce na larurin Addini da na hankali, idan kuwa biyayya gare shi ba ta wajaba ba a kan haka, to kuwa wannan ya kore Annabcin da babu makawa tana tare da wajabcin biyayya har abada.
Ta kowane hali dai aiki ko zance ya zo daga gareshi da ya zama muna tunanin sabo ne ko kuskure, sai ya zama ba wajibi ba ne a bi shi a cikin kowane abu, sai fa’idar aiko Annabawa ta zamanto ta tafi haka nan, sai Annabin ya zama kamar sauran mutane da maganarsa ba ta da wata kimar da za a dogara a kanta da’iman, kamar yadda biyayya gare shi ba za ta zama tilas ba, babu kuma nutsuwar zuciya da maganganunsa da ayyukansa baki daya.
Wannan kuwa dalili ne a kan cewa Isma tana tare da Imami, domin kaddarawar cewa shi zababbe ne daga Allah (S.W.T) don shiryar da bayi a matsayin halifan Annabi, kamar yadda zamu yi karin bayani a fasalin Imamanci.

17. Imaninmu Game da Siffofin Annabi

Mun yi imani da cewa, kamar yadda ya wa.jaba Annabi ya zamanto ma`asumi, haka nan ya wajaba ya zamanto mai siffantuwa da mafi kamalar siffofin dabi’a da hankali wadanda mafifitan su, su ne jarumtaka, da iya tafiyar da al’amuran mutane, da shugabanci, da hakuri, da karfin kwakwalwa da hazikanci, har ya zamanto babu wani daga cikin mutane da zai yi kusa da shi a kan haka, domin ba don haka ba, da bai inganta ba ya zamanto yana da shugabanci a kan dukkan halittu baki daya ba, ko ya zamanto yana da karfin tafiyar da al’amuran duniya dukkaninta ba.
Haka nan wajibi ne ya zamanto mai tsarkin haihuwa dan halas, amintacce, mai gaskiya, wanda yake tsarkakakke daga dukkan miyagun dabi’u kafin aiko shi saboda zukata su nutsu da shi, rayuka kuma su karkata zuwa gareshi, kuma domin ya cancanci wannan matsayi mai girma daga Ubangiji.

18. Imaninmu Game Da Annabawa Da Littattafansu

Mun yi imani a dunkule da cewa dukkan Annabawa da Manzanni a kan gaskiya suke, kamar yadda muka yi imani da ismarsu da tsarkinsu, musanta Annabcinsu kuwa da zaginsu da isgili da su yana daga kafirci da zindikanci, domin yin haka yana nufin karyata Annabinmu wanda ya ba da labari game da su da kuma gaskiyarsu.
Wadanda aka san sunayensu da shari’o’insu kamar Annabi Adam (A.S) da Annabi Nuhu (A.S) da Annabi Ibrahim (A.S) da Annabi Dawud (A.S) da Annabi Sulaiman (A.S) da Annabi Musa (A.S) da Annabi Isa (A.S) da sauran Annabawan da Kur’ani ya ambace su a sarari, ya wajaba a yi imani da su a ayyane, duk kuwa wanda ya karyata daya daga cikinsu to ya karyata su baki daya, kuma ya karyata Annabcin annabinmu a kebance.
Haka nan ya wajaba a yi imani da littattafansu da abin da aka saukar musu. Amma Attaura da Injila da suke hannayen wadanda aka canza su daga yadda suka sauka saboda abin da ya auku gare su na daga canje-canje da sauye-sauye, na daga kari da ragi bayan zamanin Annabi Musa da Annabi Isa (A.S), saboda wasan da ma’abuta son rai da kwadayi suka yi da su, wadanda ake da su yanzu mafi yawancinsu ko ma dukkansu kagaggu ne da aka farar a zamanin mabiyansu bayan wucewarsu (A.S).

19. Imaninmu Game Da Musulunci

Mun yi imani cewa Addini a wajan Allah kawai shi ne musulunci, kuma shi ne Shari’ar Ubangiji ta gaskiya wacce take Shari’ar karshe, kuma ita ce mafi kamala kuma mafi dacewa ga sa’adar dan Adam, ita ce ta fi kunsar maslaharsu ga al’amuran duniya da lahirarsu, kuma mai dacewa ga wanzuwa duk tsawon zamani ba ta canjawa ba ta sakewa kuma mai kunshe da dukkan abin da dan Adam yake bukata daga tsarin rayuwar daidaiku da zamantakewar jama’a da na siyasa. Da yake Shari’ar musulunci ita ce ta karshe, kuma ba ma jiran wata shari’a da za tazo ta yi gyara ga dan Adam da ya rigaya ya dulmuya cikin zalunci da fasadi, to babu makawa wata rana ta zo da Addinin musulunci zai yi karfi har ya game rayuwa da adalcinsa da dokokinsa.
Da an dabbaka Shari’ar musulunci da dokokinta a bayan kasa daidai wa daidai yadda ya dace to da aminci ya game ‘yan Adam kuma da rabauta ta game su, kuma da sun kai kololuwar abin da dan Adam yake mafarkinsa na daga walwala, da izza, da yalwa, da annashuwa, da kyawawan dabi’u, kuma da zalunci ya kau daga duniya, soyayya da ‘yan’uwantaka sun yadu a tsakanin mutane, talauci da fatara sun kau gaba daya.
Idan a yau muna ganin halin ban kunya da kaskanci da ya samu wadanda suke kiran kansu musulmi, to domin ba a aiwatar da addinin musulunci ba ne a bisa hakika kamar yadda yake a nassinsa da ruhinsa suke tun daga karni na farko, kuma muka ci gaba a cikin wannan hali mu da muke kiran kanmu musulmi, daga mummunan hali zuwa mafi muni har zuwa yau din nan da muke ciki. Ba riko da musulunci ko aiki da shi ne ya jawo wa musulmi wannan mummunan cibaya ba, sai dai ma akasin haka, wato kangare wa koyarwar musulunci, da tozarta dokokinsa, da yaduwar zalunci, da ketare haddi daga bangaren Sarakunansu da talakawansu, da kebantattu da kuma baki dayansu. Wannan kuwa shi ne abin da ya lahanta yunkurin cigabansu, ya raunana karfinsu, ya ruguza tsarkin ruhinsu, ya jawo musu bala’i da halaka har Allah (S.W.T) ya halakar da su saboda zunubansu. Allah madaukaki yana cewa:
“Wannan kuwa domin Allah bai kasance yana canja wata ni’ima da ya ni’imtar da ita ga wasu mutane ba face sai sun canja abin da yake ga kawukansu”. Surar Anfal 53.
Da fadinsa “Kuma wannan ita ce sunnar Allah a halittunsa cewa tabbas masu laifi ba sa cin rabauta”. Surar Yunus: 17.
Da fadinsa madaukaki: “Kuma Ubangijinka bai kasance mai halakar da alkaryu ba bisa zalunci alhali mutanenta suna masu gyara”. Surar Hudu: 117.
Da fadinsa: “Kuma haka nan kamun Ubangijinka yake idan ya kama alkarya alhali tana azzaluma lalle kamunsa mai radadi ne mai tsanani”. Surar Hudu: 102.
Ta yaya ake sauraron Addinin musulunci ya tayar da al’umma daga dogon baccinta, alhali kuwa shi a wajanta kamar tawada ce a kan takarda da ba a aiki da mafi karanci daga koyarwarsa. Hakika imani, da amana, da gaskiya, da tsarkin niyya, da kyautata mu’amala, da sadaukarwa, da kuma cewa musulmi ya so wa dan’uwansa musulmi abin da yake so wa kansa, da makamantansu, tun farkon assasa Addinin musulunci musulmi sun yi bankwana da su tun da can har zuwa yau. Kuma duk sanda zamani ya ja gaba sai mu same su suna kara rarraba jama’a-jama’a da kungiya-kungiya, suna kifuwa da goggoriyo a kan duniya, suna ta fagamniya a cikin duhu, sashensu na kafirta sashe da wasu ra’ayoyi gagara fahimta, ko kuma a kan wasu al’amura da babu ruwansu a ciki, suka shagaltu ga barin asasin Addini da maslaharsu da maslahar al’ummarsu, da fadawa cikin jayayya game da halittar Kur’ani ko rashin kasancewarsa abin halitta, da batun narkon azaba da Raja’a, da kuma cewa aljanna da wuta halittattu ne a halin yanzu ko kuma za a halicce su ne nan gaba.
Makamantan wadannan gardandamin wadanda suka rike musu wuya, wasunsu suka kafirta wasu, babu abin da suke nunawa sai kaucewar musulmi daga madaidaicin tafarki zuwa ga halaka da karewa. Fandarewa ta karu tare da shudewar zamani, har Jahilci da bata suka mamaye su, suka shagaltu da abu maras kima, da camfe-camfe, da surkulle, da wahamce-wahamce, da kuma yake-yake, da jayayya, da alfahari, sai suka fada a cikin halakar da ba ta da iyaka. A yau yammacin Turai wayayye, fadakakke, babban sanannen makiyin mlusulunci, ya samu damar mulkin mallaka a kan wani yanki da yake na musulmi, su kuwa sun yi zamansu cikin gafala da rafkanwa yadda har ya iya jefa su cikin mummunan halin da Allah ne kadai ya san iyakarsa da lokacin karewarsa. Allah madaukaki yana cewa: “Kuma Ubangijinka bai kasance yana halakar da alkaryu ba bisa zalunci alhali mutanenta suna masu gyara”. Surar Hudu: 117.
A yau da kuma gobe musulmi ba su da wata mafita sai koma wa kawukansu su yi wa kansu hisabi a kan sakacin da suka yi, su yi yunkurin gyara kawukansu da zuriyoyi masu zuwa, ta hanyar ba su koyarwar Addininsu mai inganci domin su gusar da zalunci da ja’irci tsakaninsu. Da haka ne kawai zasu tsira daga wannan halaka mai girma, kuma babu makawa bayan nan su cika duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci kamar yadda Allah (S.W.T) ya yi musu alkawari. Kuma kamar yadda ake saurare daga addininsu da yake shi ne cikon addinai da ba a kaunar wani gyara na duniya ko lahira sai da shi(26).
Babu makawa wani Imami ya zo ya kakkabe wa musulunci abin da aka lillika masa na daga bidi’o’i da bata kuma ya tserar da ‘yan Adam, ya kubutar da su daga abin da suka kai matuka gareshi na daga fasadi gama-gari, da zalunci mai dorewa, da kiyayya mai ci gaba, da izgili da kyawawan dabi’u da ruhin ‘yan’adamtaka, Allah ya gaggauta bayyanarsa ya saukake mafitarsa.

20. Imaninmu Game Da Mai Shara’anta Musulunci

Mun yi imani da cewa ma’abocin sakon Addinin Musulunci shi ne Annabi Muhammadu dan Abdullahi, kuma shi ne cikamakon Annabawa, shugaban Manzanni, kuma mafificinsu baki daya, kamar yadda shi ne shugaban ‘yan Adam baki daya. Babu wani mai falala da ya yi daidai da shi, babu wani da ya yi kusa da shi a karimci, babu wani mai hankali da zai yi kusa da shi a hankali, babu wani kamarsa a kyawawan dabi’u: “Lalle kai kana kan manyan dabi’u masu girma”. Surar Kalam: 4. Wannan kuwa tun farkon samuwar dan Adam har zuwa ranar tashin kiyama(27).

21. Imaninmu Game Da Kur’ani Mai Girma

Mun yi imani cewa Kur’ani wahayin Ubangiji ne, kuma abin saukarwa daga Allah madaukaki a harshen AnnabinSa mai daraja, a cikinsa akwai bayanin komai, shi ne mu’ujiza madawwamiya wacce ta gagari dan Adam ya zo da kamarta a balaga, da fasaha, da azanci, tare da abin da ya kunsa na daga hakika da ilimomi madaukaka, jirkita, ko canji, ko karkacewa, ba sa bujuro masa(28), Kur’anin da yake hannunmu wanda ake karantawa shi ne wanda aka saukar wa Annabi (S.A.W), duk kuma wanda ya yi da’awar sabanin wannan to shi mai kage ne, mai kawo rudu, kuma mai rikitarwa, kuma ba a kan shiriya yake ba, domin shi Kur’an zancen Allah ne “Wanda karya ba ta zo masa ta gaba gare shi ko kuma ta bayansa”. Surar Fusilat: 42.
Daga cikin dalilan da suke tabbatar da mu’ujizarsa akwai cewa, duk sadda zamani ya cigaba, ilimomi da fannoni suka dada cigaba, Kur’ani yana nan daram a kan danyantakarsa da zakinsa, da daukakar manufofinsa, da abin da ya kunsa na tunani, babu wani kuskure da yake bayyana daga cikinsa dangane da tabbatattun matsayi na ilimi, kamar yadda ba ya taba kunsar wani warwara game da hakika da yakini na falsafa, sabanin littattafan da malamai da manyan masanan falsafa komai matsayin da suka kai kuwa a fagen ilimi da kuma amfani da kwakwalwa da tunani suka rubuta, sai ka samu wani abu na kuskure a cikinsu da tuntube. Kuma Kur’ani yana nan daram duk sadda aka samu cigaba a sababbin bincike na ilimi da sababbin ra’ayoyi. Kurakurai suna bayyana hatta a rubuce-rubucen manyan masana falsafar Yunan kamar su Sakrato, da¬ Aplato, da Arasto, da duk wadanda suka zo daga bayansu suka yi musu shaida da cewa su ne iyayen ilimi da kuma fifiku na tunani da amfani da kwakwalwa.
Kuma mun yi imani da wajabcin girmama Kur’ani mai girma da daukaka shi a cikin magana ko a aiki, bai halatta ba a najasta koda kalma guda a cikinsa wadda ake dauka cewa ita yanki ce daga cikinsa, da kuma nufin cewa daga cikinsa take, kamar yadda bai halatta ba ga wanda ba shi da tsarki ba ya taba kalmominsa ko harrufansa: “Babu mai shafarsa sai wadanda suke tsarkakakku”. Surar Waki’a: 79. Shin sun kasance suna da babban kari ne kamar janaba, ko haila, ko jinin biki, da makamantansu, ko kuma karamin kari koda ma barci ne, sai dai idan sun yi wanka ko alwala kamar yadda bayani ya zo dalla-dalla a cikin littattafan fikihu.
Haka nan bai halatta ba a kona shi ko wulakanta shi ta kowace fuska da abin da yake wulakanci ne a ganin mutane, kamar jefar da shi, ko sanya masa kazanta, ko shurinsa da kafa, ko sanya shi a wuri wulakantacce, Idan da wani zai wulakanta shi da gangan, ko tozarta shi, da aikata daya daga cikin wadannan abubuwan da muka ambata da makamantansu, to shi yana daga cikin masu karyata Addinin musulunci da alamominsa masu tsarki, kuma shi abin hukuntawa ne da fita daga Addini da kafircewa ga Ubangijin talikai.

22. Hanyar Tabbatar Da Gaskiyar Addinin Musulunci

Idan muka yi jayayya da wani a kan ingancin Addinin musulunci zamu iya kayar da shi ta hanyar tabbatar masa da mu’ujizarsa dauwamammiya wato Kur’ani mai girma kamar yadda ya gabata game da kasancewarsa gagara badau. Haka nan Kur’ani shi ne hanyar gamsar da kawukanmu yayin da kokwanto ya fara zo mana, saboda irin wadannan tambayoyi da kokwanto ba makawa su taso ga mutum mai ‘yanci a tunani yayin karfafa akidarsa ko tabbatar da ita.
Amma shari’o’in da suka gabata kamar Yahudanci da Kiristanci, ba mu da wata hujja ko hanyar da zamu gamsar da kanmu, ko kuma mu gamsar da mai tambaya game da ingancinsu, domin su wadannan addinan ba su da sauran wata mu’ujiza da ta rage garesu, abin da mabiyan wadannan addinan suke nakaltowa na daga abubuwan mamaki da mu’ujizozi da suke danganta su ga annabawan da suka gabata, su ababan tuhuma ne a kan haka. Kuma babu wani abu da yake cikin littattafan addinan da suka gabata da yake hannunmu a wannan zamani wadanda ake danganta su ga annabawan, kamar Attaura da Injila, da ya dace ya zama mu’ujiza madawwamiya da zai iya zama hujja yankakkiya, kuma dalili mai gamsarwa idan ba musulunci ne ya gasgata da ita ba.
Sai dai mu musulmi ya inganta ne a garemu mu gaskata annabacin ma’abota shari’un da suka gabata, domin bayan gaskatawarmu da Addinin Musulunci, to ya wajaba a kanmu mu gaskata dukkan abin da ya zo da shi. Kuma a cikin abin da ya zo da shi akwai gaskata annabcin wasu daga annabawan da suka gabata kamar yadda ya gabata a baya.
Don haka musulmi ya wadatu ga barin bincike game da ingancin shari’un da suka gabata, domin gaskatawa da shi gasgatawa ne garesu, kuma imani da shi imani ne da manzannin da suka rigaya da annabawa magabata, don haka bai wajaba ba a kan musulmi ya yi wani bincike game da gaskiyar mu’ujizar annabawa ma’abota wadancan shari’o’i, domin abin kaddarawa shi ne ya riga ya yi imani da ita ta hanyar imani da musulunci kuma wannan ya isar.
Na’am, idan da mutum zai yi bincike game da Addinin musulunci ingancinsa bai tabbata gareshi ba, to dole ne a kansa kamar yadda hankali ya wajabta neman sani da ilimi ya yi bincike game da Addinin Kiristanci domin shi ne Addinin karshe kafin Musulunci, idan ya bincika Addinin Kiristanci bai gamsu ba, to sai kuma ya dukufa a kan Addinin da ya gabace shi wato Yahudanci. Haka nan dai zai yi ta binciken addinan da suka gabata har sai ya kai ga yakini da ingancin addinan da suka gabata, ko kuma rashin ingancinsu sai ya yi watsi da su baki daya.
Sabanin wanda ya tashi a Addinin Yahudanci ko kuma Kiristanci, shi Bayahude imaninsa da Addininsa ba zai wadatar da shi ga barin binciken Addinin Kiristanci da Addinin Musulunci ba, dole ne a kansa ya yi bincike a bisa wajabcin hankali ga neman sani. Haka nan kirista ba zai isu da imani da Almasihu (A.S) ba, wajibi ne ya yi kokari wajen sanin Musulunci da ingancinsa, ba zai samu uzuri ba da gamsuwa da addininsa ba, ba tare da bincike ba. Domin Yahudanci da Kiristanci ba su kore shari’ar da zata zo bayansu mai shafe su ba. Annabi Musa (A.S) bai ce babu Annabi bayansa ba, haka ma Annabi Isa (A.S) ya yi bushara da zuwan Annabin da zai zo bayansa(29).
Ta yaya zai halatta ga Kiristoci da Yahudawa su gamsu da akidojinsu, su dogara da Addininsu kafin su yi bincike game da ingancin shari’ar da ta biyo bayansu, kamar Kiristanci dangane da Yahudanci, ko musulunci dangane da Kiristanci da Yahudanci. Wajibi ne a bisa hukuncin hankali su yi bincike game da shari’ar da ta zo daga bayansu, idan ingancinta ya tabbata gare su to sai su canja zuwa gare ta su bar Addininsu, idan kuwa ba haka ba to ya dace a bisa hukuncin hankli su wanzu a kan Addininsu na da, su kuma karkata zuwa gareshi
Amma musulmi kamar yadda muka riga muka fada idan har ya yi imani da Musulunci, to ba ya bukatar ya yi bincike game da addinan da suka gabaci Addininsa da kuma wadanda ake da’awa bayansa. Wadanda suka gabata dai domin shi ya yi imani da su, to don me kuma zai bukaci dalili ko hujja game da su, sai dai kawai ya yi hukunci da cewa ita shafaffiya ce da Shari’ar Musulunci, don haka bai wajaba ya yi aiki da hukunce-hukuncensu ko littattafansu ba. Amma wadanda ake da’awarsu daga baya kuwa dalili shi ne, saboda Annabin Musulunci Muhammad (S.A.W) ya ce: “Babu wani Annabi bayana”. Kuma shi Mai gaskiya ne kuma Amintacce. “Kuma shi ba ya magana a kan son rai, ba wani abu ba ne face wahayi da aka yi masa”. Surar Najmi: 3-4. Don haka saboda menene zai bukaci dalili a kan ingancin da’awar Annabcin da aka yi da’awarsa daga baya idan har mai da’awar ya yi da’awa.
Na’am yana wajaba a kan musulmi -ya yi bincike bayan tsawon lokaci tsakaninsa da ma’abocin sako (S.A.W), da sabanin mazhabobi da ra’ayoyi, da kuma samuwar kungiyoyi- ya yi bincike, ya bi hanya mafi dacewa wajen isar da shi ga sanin ainihin hukunce-hukuncen da aka saukar na shari’a, domin shi musulmi an kallafa masa aiki da dukkan hukunce-hukuncen da aka saukar na shari’a kamar yadda suka zo. Sai dai kuma ta yaya zai san cewa ita ce shari’ar da aka saukar kamar yadda take, alhali musulmi sun sassaba jama’a-jama’a, sun rarraba, babu salla guda daya, babu ayyukan ibada da aka yi ittifaki a kansu, ayyuka ba su zama daidai iri daya ba a cikin dukkan mu’amala. Don haka yaya zai yi? Ta wace irin hanya zai yi salla? Da wane ra’ayi zai yi aikin ibada da mu’amalarsa, kamar aure, da saki, da gado, da saye da sayarwa, da tsayar da haddi, da diyya da sauransu?
Kuma bai halatta gare shi ba ya bi ra’ayin iyaye ko ya koma ga abin da zuriyarsa da mutanensa suke a kai ba, sai dai ma babu makawa ya zama yana da yakini shi da kansa tsakaninsa da Allah (S.W.T), domin a nan babu wani boye-boye da nuku-nuku, ko sassauci, ko bangaranci. Na’am babu makawa ya samu yakinin cewa ya bi hanyar da ya yi imani da cewa zai sauke nauyin da yake kansa tsakaninsa da Allah, ya kuma tabbatar da cewa ba za a yi masa azaba a kai ba, Allah kuma ba zai zarge shi a kan bin ta da aiki da ita ba, bai halatta ba zargin mai zargi ya dame shi a kan tafarkin Allah “Shin mutum yana tsammanin za a bar shi haka nan ne sakaka kawai”. Surar Alkiyama: 36.
“Lalle shi mutum a game da kansa mai gani ne”. Surar Alkiyama: 14. “Lalle wannan fadakarwa ce, don haka ga wanda ya so ya kama hanya zuwa ga Ubangijinsa”. Surar Muzzammil 19.
Farkon abin da mutum zai tambaya shi ne; Shin ya kama tafarkin Zuriyar Gidan Manzon Allah ne ko kuwa tafarkin wasu daban? Idan ya kama tafarkin Ahlul Baiti (S.A.W) shin tafarkin Imamiyya Isna Ashariyya masu bin Imamai sha biyu shi ne ingantaccen tafarki ko kuma tafarkin wadansu daga bangarori daban-daban? Idan kuma tafarkin Ahlussunna ya kama to da wa zai yi koyi, daga cikin mazhabobi hudun ne ko kuma daga wasu mazhabobin daban da suka rushe? Haka nan tambayar zata yi ta zo wa wanda yake da ‘yanci a tunani da zabi har sai ya kai ga wata gaskiya a bar dogaro.
Saboda haka bayan wannan ya wajaba a kanmu mu yi bayani game da Imama, mu yi bincike a kan abin da yake biye da ita a akidar Imamiyya Isna Ashariyya.

Fasali Na Uku

23. Imaminmu Game Da Imamanci

Mun yi imani cewa Imamanci yana daga cikin Usuluddin wadanda imani ba ya cika sai da kudurcewa da su, kuma bai halatta a yi koyi da iyaye da dangi da malamai a cikinta ba komai girmansu da darajarsu kuwa, abin da yake wajibi shi ne, a nemi sani, a yi bincike game da shi, kamar yadda ya wajaba a yi a kan Tauhidi da Annabci.
A takaice, sauke nauyin da yake kan baligi da aka wajabta masa, ya dogara ne a kan imani da imamanci tabbatarwa ko korewa, koda mun kaddara cewa imamanci ba ya cikin shika-shikan addini da ba ya halatta a yi koyi a cikinsu, duk da haka ya wajaba a yi imani da ita ta fuskacin cewa; sauke nauyin da Allah ya dora wa baligi ya wajaba a hankalce, kuma dukkaninsu ba sanannu ba ne a yanke, saboda haka wajibi ne mu koma wa wanda muka san mun sauke nauyin da yake kanmu ta hanyar biyayya gareshi, ko ya zamanto imami (A.S) a mazhabar imamiyya, ko waninsa a wasu mazhabobin.
Kamar yadda muka yi imani da cewa annabci tausasawa ce daga Allah, kuma ba makawa a kowane zamani ya kasance akwai imami mai shiryarwa da zai maye gurbin annabi a ayyukansa na shiryar da ‘yan Adam, da dora su a kan abin da yake maslaha a Sa’adar Duniya da Lahira, kuma biyayyar da Annabi ya cancanta daga mutane baki daya shi ma ya cancance ta, domin tafi da al’amuransu da maslaharsu, da tabbatar da adalci a tsakaninsu, da gusar da zalunci da ketare iya daga cikinsu. A bisa wannan asasin Imamanci ya zamanto ci gaban aikin Annabci, dalilin da yake wajabta aiko da annabawa da manzanni shi ne yake wajabta sanya Imami bayan Manzo (S.A.W).
Saboda haka ne muke cewa: Imamanci ba ya taba yiwuwa sai da nassi daga Allah a bisa harshen Annabi, ko kuma a bisa harshen Imamin da ya gabata. Imamanci ba zabin kowa ba ne a tsakanin mutane, ba al’amarinsu ba ne da idan suka so zasu nada wanda suke son nadawa, ko kuma su ayyana wanda suka so ayyanawa ya zama Imami a gare su, ko kuma a duk lokacin da suka so barin ayyanawar sai su bari su zama haka nan ba tare da Imami ba. Ya zo cewa: “Duk wanda ya mutu bai san Imamin zamaninsa ba to ya mutu mutuwa irin ta jahiliyya” kamar yadda haka ya tabbata daga Manzon Allah (S.A.W) a hadisi ingantacce.
A kan haka bai halatta ba wani zamani daga zamanoni ya kasance ba tare da imami da yake wajibi a yi masa biyayya ba, wanda yake ayyananne daga Allah (S.W.T), shin mutane sun ki ko ba su ki ba, sun taimake shi ko sun ki taimakon sa, sun yi masa biyayya ko sun ki yi masa biyayya, yana rayuwa a cikinsu ne ko kuwa yana boye ne daga idandunan mutane, domin kamar yadda ya inganta Annabi (S.A.W) ya boyu daga ganin mutane kamar yadda ya boyu a cikin kogo da shinge, haka nan yake game da imami (A.S), kuma a hankalce babu bambanci tsakanin gajeriyar boyuwa ko mai tsawo(30).
Madaukaki ya ce: “Kuma ga kowace a’lumma akwai mai shiryarwa”. Surar Ra’ad: 8. Da kuma fadinsa: “Kuma babu wata al’umma face sai mai gargadi ya zamanto a cikinta”. Surar Fadir: 22.

24. Imaninmu Game Da Ismar Imami

Mun yi Imani da cewa wajibi ne ga Imami ya zama katangagge daga dukkan munanan ayyuka da alfasha, na zahiri da na badini, daga yarinta har zuwa mutuwa, da gangan ko da rafkanwa, kamar yadda annabi yake. Haka nan wajibi ne ya zama katangagge daga rafkanwa, da kuskure, da mantuwa, domin Imamai su ne masu kare shari’a, masu tsayar da ita, halinsu tamkar halin Annabi ne. Dalilin da ya hukunta mana imani da ismar annabawa kuwa, shi ne ainihin dalilin da ya hukunta mana imani da ismar Imami ba tare da wani bambanci ba.
Ba wani abu ba ne a wajan Allah
Ya sanya duniya a cikin abu daya

25. Imaninmu Game Da Siffofin Imami

Mun yi imani cewa imami kamar yadda annabi yake, wajibi ne shi ma ya zama mafificin mutane a siffofin kamala, kamar jarumtaka, da karimci, da kame kai, da gaskiya, da adalci, da tafi da al’amura, da hankali, da hikima, da kuma kyawon dabi’u, dalilinmu na wajabcin samuwar wadannan siffofi ga Annabi shi ne dalilinmu na wajabcin siffantuwa da wadannan siffofi ga imami.
Amma game da iliminsa kuwa, shi yana samun ilmi da hukunce-hukuncen Ubangiji da dukkan saninsa ta gurin Annabi ne, ko kuma daga Imamin da ya gabace shi, Idan kuwa aka sami wani sabon abu, to babu makawa ya san shi ta hanyar ilhama da karfin kwakwalwar da Allah ya cusa masa, idan ya mai da hankalinsa a kan wani al’amari yana so ya san hakikaninsa to ba ya kuskure, kuma ba ya bukatar hujjoji na hankali a kan haka ko koyarwar malamai, duk da yake iliminsa yana iya karuwa, shi ya sa Annabi (S.A.W) a addu’arsa yake cewa: “Ubangiji ka kara mini ilimi”(31).
Na ce: Ya tabbata a ilimin sanin halayyar dan Adam cewa kowane mutum yana da wata sa’a ayyananniya ko wasu awowi a rayuwarsa da yakan san wani abu da kansa ta hanyar kaifin fahimta wanda shi a kan kansa wannan reshe ne na ilhami, saboda abin da Allah ya sanya masa na karfin yin haka. Wannan karfi yana sassabawa da sabawar mutane a karfinsa da rauninsa, da yawansa da karancinsa. Sai kwakwalwar mutum ta kai ga sani da ilimi ba tare da ya bukaci wani tunani ba, ko kawo mukaddima da hujjoji na hankali, ko kuma koyawar malamai ba, kuma saudayawa mutum yakan sami irin haka a kan kansa a rayuwarsa, Idan kuwa al’amarin haka yake to ya halatta mutum ya kai ga kololuwar daraja da kamala a karfin tunaninsa na sanin ilhami, wannan kuwa abu ne da masana falsafa na da, da na yanzu suka tabbatar da shi.
Karfin ilhama a gun imami ana cewa da ita “kuwwa kudsiyya” wato karfi daga Allah, da take mafi kamalar kololuwar darajar ilhama, sai mai wannan siffa a kowane lokaci a kuma kowane hali ya so ya san wani abu sai ya san shi ba tare da mukaddima ba ko koyarwar wani malami, sai ya koma wa wannan abin jahiltar domin saninsa sai ya san shi tare da taimakon wannan karfi da Allah ya ba shi, sai ilimi da wannan abu ya bayyana gareshi tamkar yadda bayyanar surar abu take bayyana a tsaftataccen madubi.
Wannan kuwa abu ne bayyananne a tarihim Imamai (A.S), su a wannan fage kamar Annabi suke ba su taba yin tarbiyya ko neman ilmi a hannun kowa ba, ba su koyi karatu a gurin wani malami ba tun daga farkon rayuwarsu har zuwansu shekarun balaga, karatu ne ko kuwa rubutu, bai tabbata ba cewa daya daga cikinsu ya shiga gurin koyon rubutu ko ya yi almajiranci a hannun wani malami a kan wani abu, duk kuwa da cewa suna da matsayin ilimi da ba a iya kintatawa, kuma ba a taba tambayar su wani abu ba face sun ba da amsarsa a lokacin da aka tambaya, ba a taba jin kalmar ban sani ba daga bakinsu, ko kuma jinkirta ba da amsa har sai sun yi nazari ko tunani ko makamancinsu, alhali kuwa ba zaka taba samun wani daga cikin manyan malaman fikihu ba sai ka ji an ambaci wanda ya tabiyyatar da shi ya koyar da shi, da kuma wadanda ya karbi ruywaya ko ilimi a hannunsu, da kuma dakatawarsu a wasu mas’aloli ko kokwantosu a mafi yawa daga ilimomi, kamar yadda yake a kowane zamani da kowane guri.

26. Imaninmu Game Da Biyayya Ga Imamai

Mun yi imani da cewa Imamai su ne “Ulul’amri” Shugabannin da Allah ya yi umarni a yi musu biyayya, kuma su masu ba da shaida ne a kan mutane, kuma su ne kofofin Allah kuma tafarki zuwa gareshi, masu shiryarwa zuwa gare shi, su ne taskar iliminsa, masu fassara wahayinSa, rukunan TauhidinSa, ma’ajiyar saninSa, don haka suka kasance aminci ga mazauna bayan kasa, kamar yadda taurari suke aminci ga mazauna sama kamar yadda ya zo daga Manzon Allah (S.A.W).
A wani hadisin yana fada: “Misalinsu a cikin wannan al’umma tamkar jirgin Annabi Nuhu (AS) ne wanda ya hau shi ya tsira, wanda kuwa ya dakata ya bar shi to ya nutse ya halaka. Kuma ya zo a Kur’ani mai girma “Su sai dai bayin Allah ne ababan girmamawa, ba sa rigonsa da magana, kuma su da umarninsa masu aiki ne”. Surar Anbiya: 26-27. Kuma su ne wadanda Allah ya tafiyar masu da dauda ya tsarkake su tsarkakewa.
Mu mun yi imani da cewa umarninsu umarnin Allah ne, haninsu hanin Allah ne, biyayya gare su biyayya ce gare shi, saba musu kuma saba masa ne, kuma Soyayya gare su soyayya ce gare shi, kiyayya gare su kiyayya ce gare Shi, bai halatta ba a mayar musu domin mai mayarwa gare su tamkar mai mayarwa ga Allah ne, kuma ya wajaba a mika wuya gare su da biyayya ga umarninsu, da riko da maganganunsu.
Saboda haka mun yi imani da cewa hukunce-hukuncen Shari’ar Ubangiji ba sa samun shayarwa sai daga ruwansu, kuma bai halatta a karbe ta ba sai daga garesu, kuma nauyin da aka dora wa baligi ba ya sauka daga kansa ta hanyar komawa ga waninsu. Kuma mukallafi ba ya samun nutsuwa da cewa ya bayar da wajibin da aka dora masa sai ta hanyarsu. Su kamar jirgin ruwan Annabi Nuhu (A.S) ne duk wanda ya hau ya tsira, wanda kuwa ya jinkirta ya bar su ya dulmuye a cikin wannan ambaliyar da take makale da igiyoyin ruwan rikitarwa, da bata, da da’awoyi, da jayayya.
Bahasin imamanci game da tabbatar da cewa su ne halifofi na shari’a kuma masu shugabanci da izinin Allah a wannan zamanin ba shi ne muhimmi ba, wannan al’amari ne na tarihi da ya wuce, kuma tabbatar da shi ba zai sake dewo mana da zamanin da ya wuce na tarihi ba, ko kuma ya dawo musu da hakkinsu da aka kwace na tafi da hukuncin Allah na shari’a ba.
Abin da yake muhimmi shi ne abin da muka ambata na wajabcin komawa zuwa garesu wajan karbar hukunce-hukuncen shari’a, da kuma sanin abin da manzo (S.A.W) ya zo da shi kamar yadda ya zo da shi ta fuska ingantacciya.
Karbar hukunce-hukunce daga masu ruwaya da kuma Mujtahidan da ba sa sha daga daddadan ruwan mashayarsu, kuma ba sa neman haskakawa daga haskensu, nisanta ne daga tafarkin daidai a Addini. Kuma baligi ba ya taba samun nutsuwar cewa ya sauke nauyin takalifin da ya hau kansa daga Allah, domin tare da samun irin wannan sabanin ra’ayoyi a tsakanin jama’ar musulmi dangane da hukunce-hukuncen shari’a, sabanin da ba a sa ran dacewa a kansa, to fa babu wata dama ga baligi ya zabi mazhabar da ya ga dama ko ra’ayin da ya zaba, dole ne ya yi bincike har ya kai ga hujja tabbatacciya tsakaninsa da Allah (S.W.T) wajen ayyana mazhaba kebantacciya, wacce ya hakikance cewa da ita ce zai isa zuwa ga hukunce-hukuncen Allah, kuma cewa da ita ne zai sauke wa kansa nauyi da aka farlanta, domin abin da ake da yakinin wajabcinsa yana lizimta wajabcin samun yakinin sauke nauyinsa.
Dalili tabbatacce da yake nuna wajabcin koma wa Ahlul Baiti (A.S) da kuma cewa su ne ainihin wadanda za a koma gare su a kan hukunce-hukunce bayan Annabi (S.A.W) sun hada da fadinsa (S.A.W): “Hakika Ni na bar muku abin da idan har kuka yi riko da shi ba za ku taba bata ba har abada bayana, Assakalaini, dayansu ya fi dayan girma; su ne littafin Allah igiya mikakkiya daga sama zuwa kasa, da kuma Zuriyata Ahlin gidana, ku saurara ku ji, ku sani cewa su ba masu rabuwa da juna ba ne har su riske ni a tafki”(32).
Ka zurfafa tunaninka game da wannan hadisi mai girma zaka samu abin da zai gamsar da kai ya kuma girgizaka a wannan hadisin a ma’anarsa a fadinsa (S.A.W): “Matukar kun yi riko da su ba zaku taba bata ba a bayana har abada” abin da ya bar mana su ne sakalaini tare, ya kuma sanya su abubuwa guda biyu, bai wadatu da riko da daya ba, ba tare da dayan ba, da riko da su ne ba zamu taba bata ba har abada. Duba kuma ma’anar fadinsa (S.A.W) cewa: “Ba zasu taba rabuwa ba har sai riske ni a tafki” da nunin cewa wanda ya raba tsakaninsu bai yi riko da su a hade ba to ba zai taba samun shiriya ba har abada, don haka ne suka zama su ne; “Jirgin ruwan tsira” kuma “Aminci ga mazauna kasa” da duk wanda ya bar su, to ya nutse a cikin guguwar bata ba kuma zai amintu daga halaka ba, fassarar wannan da ma’anar soyayya gare su ba tare da riko da maganganunsu da bin tafarkinsu ba, gudu ne daga gaskiya da ba abin da yake kaiwa ga hakan sai bakin ra’ayin jahiliyya, da gafala daga tafarki madaidaici a fassarar bayanan zancen Larabci mai fasaha.

27. lmaninmu Game Da Son Ahlul Baiti (A.S)

Madaukaki ya ce: “Ka ce ni ba na rokon ku wani lada a kansa sai dai soyayyar dangi na kusa kawai”. Surar Shura: 23. Mun yi imani cewa bayan wajabcin riko da Ahlul Baiti (A.S), wajibi ne a kan kowane musulmi ya dabi’antu da sonsu da kaunarsu domin a ayar da aka ambata an takaita abin da ake nema daga mutane da nuna soyayyar makusantansa (A.S). Ya zo ta hanyoyi masu yawa da cewa; Son su alamar imani ne kin su kuma alamar munafinci ce, kuma duk wanda ya so su ya so Allah da manzonsa, wanda kuma ya ki su, to ya ki Allah da Manzonsa (S.A.W).
Hakika son su wajibi ne daga laruran addini da ba ya karbar jayayya ko kokwanto. Domin dukkan musulmi sun hadu a kan hakan duk da sabanin mazhabobinsu da ra’ayoyinsu, in ban da kadan daga wasu jama’a da aka dauke su a matsayin masu gaba da Zuriyar Manzon Allah wadanda aka sanya musu sunan “Nawasib” wato wadanda suka kulla gaba a kan Zuriyar Annabi (S.A.W), don haka ne ma ake kirga su a cikn masu inkarin abin da yake wajibi na addinin musulunci tabbatattu, wanda kuma yake karyata larurar Addini ana kirga shi a cikin masu karyata ainihin sakon musuluncin koda kuwa a zahiri ya yi furuci da kalmar shahada, saboda haka ne kin Ahlul Baiti (A.S) ya zama daga alamomin munafunci son su kuwa ya zama daga alamomin imani kuma don haka ne kinsu ya zama kin Allah (S.W.T) da manzonsa (S.A.W).
Kuma babu shakka Allah (S.W.T) bai wajabta son su ba sai don su sun cancanci soyayya da biyayya ta bangaren kusancin su da Allah da manzonsa, da tsarkinsu, da nisantar su ga shirka da sabo, da kuma dukkan abin da yake nisantarwa daga karimcin ubangiji da yardarsa. Ba zai taba yiwuwa ba a suranta cewa; Ubangiji ya wajabta son wanda yake aikata sabo ko kuma wanda ba ya bin sa, domin shi ba shi da wata kusanci ko abotaka da wani, mutane a gurinsa ba komai ba ne sai bayi ababan halitta masu matsayi daya, kadai mafificinsu a gurin Allah shi ne mafi tsoronsu gareshi. Duk wanda ya wajabta son su a kan mutane baki daya to babu makawa ya zamanto mafi takawarsu, kuma mafi darajarsu baki daya, ba don haka ba, da waninsa ya fi cancantar wannan soyayyar, kuma da ya kasance kenan Allah yana fifita wasu mutane a kan wasu a wajabcin so da biyayya haka nan kawai ko da wasa ba tare da cancanta ko daraja ba.

28. Imaninmu Game Da Imamai (A.S)

Mu ba mu yi imani ga Imamanmu (A.S) da abin da ‘Yan gullat (33) da ‘Yan Hululiyya (34) suka yi ba, “Kalmar da take fita daga bakunansu ta girmama”. Surar Kahf 5. Imaninmu game da su shi ne cewa su mutane ne kamarmu, suna da abin da yake garemu, kuma abin da ya hau kanmu ya hau kansu, sai dai kawai su bayin Allah ne ababan girmamawa, Allah ya kebance su da karamarsa, kuma ya so su da soyayyarsa, domin suna da karamarsa, kuma ya ba su wilayarsa, domin su suna kan mafi daukakar daraja da ta dace da dan Adam na daga ilimi, da takawa, da jarumta, da karimci, da kamewa, da dukkan kyawawan dabi’u mafifita, da siffofi abin yabo, kuma babu wani dan Adam da zai yi kusa da su a kan abin da aka kebance su da shi.
Da wannan ne suka cancanci su zamo Imamai masu shiryarwa kuma makoma bayan Annabi a cikin duk abin da yake na addini na bayani da shar’antawa, da kuma abin da ya kebanta da Kur’ani na daga tafsiri da tawili.
Imaminmu Ja’afar Assadik (A.S) Ya ce: “Duk abin da ya zo muku daga gare mu daga abin da ya halatta bayi su siffanta da shi, ba ku kuma san shi ba, ba ku fahimce shi ba, to kada ku yi musun sa, ku mayar da shi gare mu, amma abin da ya zo muku daga garemu wanda bai halatta bayi su siffantu da shi ba, to ku yi musun sa kada ku mayar da shi zuwa gare mu.

29. Imaninmu Game Da Cewa Imamanci Sai Da Nassi

Mun yi imani cewa lmamanci tamkar Annabci ne ba ya kasancewa sai da nassi daga Allah madaukaki a harshen Manzonsa, ko harshen lmamin da ya aka sanya shi ta hanyar nassi idan yana son ya yi wasiyya da lmamin bayansa, hukuncin lmamanci a nan tamkar hukuncin annabci ne ba tare da wani bambanci ba, mutane ba su da ikon wani hukunci a kan wanda Allah ya ayyana mai shiryarwa ga dukkan mutane, kamar yadda ba su da hakkin ayyana shi, ko kuma kaddamar da shi, ko zabensa, domin mutumin da yake da tsarki da karfin daukar nauyin lmamanci baki daya, da kuma shiryarwa ga ‘yan Adam gaba daya, wajibi ne kada a san shi sai da shelantawar ubangiji, kuma ba a ayyana shi sai da ayyanawarsa.
Mun yi imani cewa Annabi (S.A.W) ya yi wasiyya da halifansa kuma shugaban talikai bayansa, sai ya ayyana dan amminsa Aliyyu Dan Abi Dalib Amiri ga musulmi, kuma amini kan wahayi, lmami ga halittu, ya ayyana shi a gurare da dama, kuma ya nada shi, kuma ya karba masa bai’a a kan shugabancin muminai ranar Gadir yana mai cewa: “A saurara a ji! Duk wanda na kasance shugabansa ne to wannan Ali shugabansa ne, Ya ubangiji! ka so wanda ya so shi, ka ki wanda ya ki shi, Ka taimaki wanda ya taimake shi, ka tozarta wanda ya tozarta shi, kuma Ka juya gaskiya tare da shi duk inda ya juya’’.
Daga cikin wuraren farko da ya yi wasiyya da imamancin-sa akwai fadinsa yayin da ya kira danginsa makusanta ya ce: “Wannan shi ne dan’uwana, kuma wasiyyina, kuma halifana a bayana, ku ji daga gareshi ku bi shi”. A yayin nan kuma shi yana yaro bai balaga ba. Kuma ya maimaita fadinsa da yawa da cewa: “Kai a gare ni tamkar matsayin Haruna ga Musa ne, sai dai babu Annabi a bayana”. Da sauran ruwayoyi da ayoyi masu girma da suke nuni da tabbatar shugabanci na gaba daya gare shi kamar ayar:
"Kadai cewa Allah shi ne majibancinku da Manzonsa da Wadanda suka yi imani wadanda suke ba da zakka suna masu ruku’u". Surar Ma’ida: 55. Wannan ta sauka ne game da shi yayin da ya yi sadaka da zobe yana cikin ruku’u. Wannan dan littafin ba zai iya bin diddigin dukkan abin da ya zo na daga ayoyin Kur’ani da ruwayoyi ko bayaninsu ba game da wannan maudu’i(35).
Sannan shi ma ya yi wasiyya da Imamancin Imam Hasan da Imam Husain (AS), shi kuma Husain (A.S) ya yi wasiyya da imamancin dansa Aliyyu Zainul Abidin (AS), haka nan dai Imami ke bayar da wasiyyar imamin da zai zo bayansa har zuwa kan na karshensu kamar yadda zai zo.

30. Imaninmu Game Da Adadin Imamai


Adadi

AI- kunya

Suna

Lakabi

haihuwa

Rasuwa

1

Abul Hasan

Aliyyu

Murtadha

Shekara 23 K.H

Shekara 40 H

2

Abu Muhammad

Hasan

Zakiyyi

Shekara 2 H

Shekara 50 H

3

Abu Abdullah

Husain

Shahid

Shekara 3 H

Shekara 61 H

4

Abu Muhammad

Ali

Sajjad

Shekara 38H

Shekara 95 H

5

Abu Ja’afar

Muhammad

Bakir

Shekara 57 H

Shekara 114 H

6

Abu Abdullah

Ja’afar

Sadik

Shekara 83 H

Shekara 148 H

7

Abu Ibrahim

Musa

Kazim

Shekara 128 H

Shekara 183 H

8

Abul Hasan

Aliyyu

Ridha

Shekara 148 H

Shekara 203 H

9

Abu Ja’afar

Muhammad

Jawad

Shekara 195 H

Shekara 220 H

10

Abul Hasan

Aliyyu

Hadi

Shekara 212 H

Shekara 254 H

11

Abu Muhammad

 Hasan

Askari

Shekara 232 H

Shekara 260 H

12

Abul Kasim

Muhammad

Mahdi

Shekara 256 H

….. 


Imam Al-Mahadi (AS) Shi ne Hujja a zamaninmu kuma boyayyen da ake sauraro, Allah ya gaggauta bayyanarsa ya saukaka mafitarsa, zai zo domin ya cika duniya da adalci bayan an cike ta da zalunci.

31. Abin da Muka Yi Imani Da Shi Game Da Mahadi (A.S)

Hakika albishir da bayyanar imam Mahadi (A.S) daga ‘ya’yan Fadima (A.S) a karshen zamani domin ya cika duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci ya tabbata daga Annabi (S.A.W) ta ruwayoyi masu yawa, kuma dukkan musulmi duk da sabanin mazahabobinsu sun ruwaito hadisai game da shi.
Fikirar samuwar imam mahadi (A.S) ba wani sabon abu ba ne da Shi’a suka kago shi saboda iza su da yaduwar zalunci ya yi zuwa gare shi, har suka yi mafarkin bayyanar wani wanda zai zo ya tsarkake kasa daga daudar zalunci, kamar yadda wasu masu neman kawo rikici da rudani marasa adalci suka raya. Ba don tabbatar akidar Mahadi (A.S) daga Annabi (S.A.W) ba, ta yadda dukkan musulmi suka san ta kuma ta kafu a zukatansu suka yi imani da ita, da masu da’awar mahadiyyanci a karnonin farko kamar kaisaniyya, da Abbasawa, da wasu daga Alawiyyawa, da sauransu, ba su iya yaudarar mutane ba ta hanyar samun dama da amfani da wannan akida wajen neman mulki da shugabaci, domin sun sanya da’awar mahadiyyancinsu ta karya ta zama hanyar tasiri a kan jama’a gaba daya da kuma shiga rayukan jama’a.
Mu tare da Imaninmu da ingancin Addinin musulunci, kuma cewa shi ne cikamakon addinan Ubangiji, kuma ba ma sauraron wani Addini da zai zo domin gyara dan Adam, hada da abin da muke gani na yaduwar zalunci da yawaitar fasadi a duniya, ta yadda ba zaka iya samun masakar tsinke ba ga adalci da gyara a kasashen duniya, tare da kuma abin da muke gani a fili na nesantar musulmi daga addininsu, da kuma ajiye hukunce-hukuncen musulunci da dokokinsa a gefe guda a dukkan kasashen musulmi, da kuma rashin lizimtuwarsu da koda daya daga dubban hukunce-hukuncensa, amma duk da haka ba makawa mu saurari budi da farin ciki da dawowar Addinin musulunci da karfinsa da iyawarsa wajan gyara wannan duniyar da ta dulmiya cikin takurawar zalunci da fasadi.
Sannan kuma ba zai yiwu ba musulunci ya dawo da karfinsa da jagorancinsa a kan dan Adam baki daya ba, alhalin yana kan wannan halin da yake ciki a yau da gabanin yau na daga sabanin mabiyansa a dokokinsa da hukunce-hukuncensa da ra’ayoyinsa game da shi, tare da wannan hali da suka samu kansu a ciki a yau da ma kafin yau na bidi’o’i da canje-canje a dokokinsa, da bata a cikin da’awoyinsu.
Na’am ba zai yiwu ba Addini ya koma ga karfinsa sai dai idan mai gyara babba ya jagorance shi, yana hada kansu, yana kuma rushe abin da aka raba masa na daga bidi’o’i da bata, tare da taimakon Ubangiji da ya sanya shi shiryayye mai shiryarwa, wanda yake da matsayi mai girma na Shugabanci na gaba daya, da kuma iko mai sabawa al’ada, domin ya cika duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci.
A takaice; Dabi’ar yanayin fasadi a duniyar dan Adam ta kai matuka a baci da kuma zalunci, duk da kuwa imani da ingancin wannan addini da cewa shi ne cikamakon addinai, wannan al’amari ya hukumta sauraron mai wannan gyara domin tseratar da duniya daga abin da take ciki. Saboda haka ne dukkan bangarorin musulmi suka yi imani da wannan sauraron, kai har da ma wadanda ba musulmi ba, sai dai kawai bambancin da yake tsakanin mazhabar Imamiyya da waninta shi ne, ita mazhabar imamiyya ta yi imani cewa wannan mai gyaran mutum ne ayyananne wanda aka haife shi a shekarar hijira ta 256, kuma bai gushe ba yana raye, kuma shi dan imam Hasan Askari ne mai suna “Muhammad” (A.S). Wannan kuwa saboda abin da ya tabbata daga Annabi (S.A.W) da kuma imamai (A.S) game da alkawarin zuwansa, da haihuwarsa, da boyuwarsa. Bai halatta ba Imamanci ya yanke a wani zamani daga zamuna koda kuwa Imami ya kasance boyayye ne, domin ya bayyana a ranar da Allah ya yi alkawari, wanda kuma wannan yana daga cikin asiran Ubangiji da babu wanda ya san su sai shi.
Kuma rayuwarsa da wanzuwarsa ba komai ba ne sai mu’ujiza ce da Allah ya sanya domin ba ta fi mu’ujizar kasancewarsa imami ga mutane yana dan shekara biyar ba a ranar da mahaifinsa ya koma zuwa ga Ubangiji Madaukaki, kuma ba ta fi Mu’ujizar Annabi Isa (A.S) girma ba da ya yi magana da mutane yana cikin shimfida yana jariri, kuma aka aike shi Annabi ga mutane.
Tsawon rayuwa fiye da dabi’a fannin likitanci bai musanta shi ba, kuma ba ya ganinsa mustahili, sai dai shi likitanci bai kai matsayin da zai iya kara tsawon rayuwar mutum ba. Idan kuwa likitanci ya gajiya a kan haka to Allah mai iko ne a kan komai. Kuma tsawaita rayuwar Annabi Nuhu (AS) da wanzuwar Annabi Isa (AS) ya faru kamar yadda Kur’ani ya bayar da labari, idan kuwa mai shakka ya yi shakku game da abin da Kur’ani ya ba da Iabari game da shi, to sun yi hannun riga da Musulunci.
Yana daga abin mamaki musulmi ya tsaya yana tambaya game da yiwuwar haka alhalin yana da’awar imani da Littafi Mabuwayi.
Daga cikin abin da ya zama dole mu ambace shi a nan shi ne cewa; sauraron ba yana nufin musulmi su nade hannayensu game da al’amuran da suka shafi Addininsu ba ne, da kuma abin da ya wajaba na taimakonsa, da jihadi a tafarkinsa, da riko da hunkunce-hukuncensa, da yin umarni da kyakkyawa da hani da mummuna. Musulmi har abada abin kallafawa ne da aiki da abin da ya sauka na daga hukunce-hukuncen Shari’a, kuma ya wajaba a kansa ya yi kokarin sanin su ta fuska ingantacciya, kuma wajibi ne a kansa ya yi umarni da kyakkyawa, kuma ya yi hani da mummuna gwargwadon daidai yadda zai iya “Dukkanku makiyaya ne kuma kowannenku abin tambaya ne game da abin kiwonsa.” Saboda haka bai halatta gareshi ba ya takaita wajibansa don yana jiran mai kawo gyara Imam Mahadi (A.S), wanda yake mai shiryarwa da aka yi albishir da shi, domin wannan ba ya saryar da takalifin da aka kallafa, ba ya jinkirta aiki, ba ya sa mutane su zama karazube kamar dabbobi.

32. Imaninmu Game Da Raja’a (Komowa Duniya)

Abin da Mazhabar Ja’afariyya Imamiyya ta tafi a kansa da riko da abin da ya zo daga Ahlul Baiti (A.S) Shi ne cewa; Allah (S.W.T) zai komo da wasu mutane daga cikin wadanda suka mutu zuwa duniya a bisa kamanninsu da suka kasance a kai, sai ya daukaka wasu ya kuma kaskantar da wasu, ya dora masu gaskiya a kan marasa gaskiya, ya kuma saka wa ababan zalunta daga azzalumai, wannan kuwa zai faru ne yayin bayyanar Mahadi (A.S).
Ba mai dawowa sai wanda darajarsa ta imani ta daukaka ko kuma wanda ya kai kololuwa a barna, sannan sai su sake mutuwa, daga baya kuma sai tashin kiyama, sai kuma samun sakamakon abin da suka cancance shi na kyakkyawan sakamako ko kuma azaba, kamar yadda Allah ya kawo a cikin Kur’ani mai girma game da burin da wadanda suka komo din wadanda suka sami fushin Allah suke yi domin a dawo da su dawowa ta uku ko sa gyara ayyukansu: “Suka ce Ya Ubangijinmu ka matar da mu sau biyu kuma ka rayar da mu sau biyu, to mun yi furuci da zunubanmu, shin akwai wata hanyar fita”. Surar Mumin: 11.
Na’am Kur’ani ya zo da yiwuwar komowa zuwa duniya hadisai da dama sun zo daga Ahlul Baiti (A.S) game da hakan, kuma mabiya Ahlul Baiti sun yi ittifaki a kan haka in ban da ‘yan kadan daga cikinsu da suka yi tawilin abin da ya zo game da Raja’a da cewa, ma’anarta ita ce komowar hukuma da umarni da hani a hanuun Ahlul Baiti (A.S), da bayyanar lmamin da ake sauraro ba tare da komowar wasu ayyanannu mutane ba ko rayar da matattu.
Batun Raja’a kuwa a gurin Ahlussunna yana daga cikin abin ki da imani da shi ya munana, kuma marubutansu a ilimin sanin maruwaitan hadisai suna kirga imani da raja’a abin suka ga mai ruwaya, kuma aibi gare shi da yake wajabta kin ruwayarsa da jefar da ita, tayiwu suna kirga ta a matsayin kafirci da shirka ne ko ma tafi muni, don haka wannan yana daga cikin mafi girman abubuwan da suke sukan Shi’a da aibata su da shi.
Babu shakka wannan wata barazana ce da kungiyoyin Musulmi a tsawon zamani suke amfani da ita domin sukar sashensu, kuma ba mu ga wani abu da zai janyo wannan ba, domin imani da Raja’a ba ya rushe imani da tauhidi ko Annabci, yana ma kara inganta su ne, domin Raja’a dalili ne a kan kudurar Allah cikakkiya kamar yadda tashin kiyama da tayar da matattu suke. Raja’a tana daga cikin abubuwan da suka saba wa al’ada wacce ya inganta ta zama mu’ujiza ga Annabinmu Muhammad (S.A.W) da Alayensa, kuma ita tamkar mu’ujizar rayar da matattu ce da ta kasance ga Annabi Isa (A.S), kai ta fi ta ma, domin ita tana kasancewa ne bayan matattun sun zama rididdigaggu. “Ya ce wanene zai rayar da kasusuwa alhali suna rididdigaggu? Ka ce wannan da ya fare su tun karon farko shi ne zai rayar da su, kuma shi masani ne da dukkan halittu”. Surar Yasin: 79-87.
Amma wanda ya soki Raja’a kuwa bisa dalilin cewa tana daga cikin “Tanasuhi(36)”, wannan saboda bai fahimci bambanci tsakanin “Tanasuhi” da tayar da matattu da jikkunansu na ainihi ba ne, ita Raja’a wani nau’i ne na tayar da matattu da jikinsu ne, domin ma’anar Tanasuhi ita ce: Ciratar wata rai daga wani jiki zuwa wani jikin daban da ba na farko ba. Wannan kuwa ba ita ce ma’anar tayar da matattu da jikkunansu na ainihi ba, ma’anarta ita ce; komo da ainihin jikin da siffofinsa na kashin kansa da suka kebantu da shi, haka nan ma Raja’a take. Idan kuwa da “Raja’a” “Tanasuhi” ce, to rayar da matattu ta hannun Annabi Isa (A.S) ma ya zama “Tanasuhi” ne, haka ma tayar da matattu da komo da ainihin jikkunansu ya zama “Tanasuhi’’ ke nan.
Saboda haka babu abin da ya rage sai tattaunawa game da “Raja’a” ta fuska biyu.
(1) Na farko: Cewar ita mustahiliya ce.
(2)Na biyu: Karyata hadisan da suka zo game da ita.
(1)A bisa kaddarawar cewa tattaunawar guda biyu daidai ne, to yin imani da ita ba a daukarsa a matsayin kyamar da masu gaba da Shi’a suka mayar da ita, kuma da yawa daga cikin abubuwan da suke mustahilai ne wasu bangarorin musulmi suka yi imani da su, ko kuma wadanda sam ingantaccen nassi bai tabbata ba game da su, amma ba su wajabta kafirtawa da fitarwa daga Musulunci ba. Akwai Misalai masu dama a kan hakan, kamar imani da yiwuwar rafkanwa ga Annabi (S.A.W) ko kuma aikata sabo, da kuma imani da rashin farko ga Kur’ani, da kuma batun narkon azaba, da kuma imani da cewa Annabi bai yi wasiyya da halifa a bayansa ba.
Kuma wadannan munakashoshi biyu ba su da wani asasi na inagnci, amma batun cewa raja’a mustahili ce mun riga mun kawo cewa ita nau’i ce na tayar da matattu da jikkunansu, sai dai cewa tayarwa ce a nan duniya, kuma dalilin yiwuwar ta shi ne dalili a kan yiwuwar tashin kiyama. Kuma babu wani dalili a kan cewa dole ta zama abin mamaki, sai dai kawai mu ba mu saba da ita ba ne a rayuwarmu ta wannan duniya, ba mu san kuma sabubbanta da abubuwan da suke hana ta ba da zasu sanya yin ikrari da ita ko mu kore ta. Tunanin mutum ba ya saukake masa yarda da abin da bai saba da shi ba cikin sauki, kamar wanda yake mamakin tayar da matattu yana mai cewa: “Wanene zai rayar da kasusuwa alhali suna rididdigaggu”. Aka ce masa: “Wannan da ya fare su tun karon farko shi ne zai rayar da su, kuma shi masani ne da dukkan halittu”. (Yasin: 78-79)
Na’am a kan makamancin wannan da ba mu da dalili na hankali a kai na tabbatar da shi ko kore shi, ko kuma mu ka raya rashin samuwar dalili, to a nan ya zama dole a kanmu mu koma wa nassosin Addini wadanda suke su ne tushen wahayin Ubangiji. Kuma abin da zai tabbatar da yiwuwar Raja’a ga wasu matattu a duniya ya zo a Kur’ani kamar dai mu’ujizar Annabi Isa (AS) ta rayar da matattu: “Kuma Ina warkar da Wanda aka haifa makaho kuma Ina rayar da matattu da izinin Allah”. Surar Ali Imran: 49.
Da kuma fadin Ubangiji: “Ta yaya Allah zai rayar da wadannan bayan mutuwarsu, sai Allah ya matar da shi Shekara dari sannan ya tayar shi”. Surar Bakara: 259.
Da kuma ayar da ta gabata da take cewa: “Suka ce Ya ubagijinmu Ka matar da mu sau biyu”. Surar Mumin: 11. Ma’anar wannan ayar ba zata yi daidai ba, ba tare da komowa duniya bayan mutuwa ba, duk da wasu daga masu tafsiri sun kallafa wa kawukansu yin tawilin da ba zai kashe kishirwa ba, kuma ba zai tabbatar da ma’anar ayar ba.
(2) Tattaunawa ta biyu:- Ita ce da’awar cewa hadisai game da Raja’a kagaggu ne, ba ta da asasi, domin Raja’a tana daga cikin al’amuran da suke na larura da suka zo daga Ahlul Baiti (A.S) na hadisai mutawatirai.
Bayan wannan, ashe ba ka yi mamakin shahararren marubucin nan mai da’awar sani Ahmad Amin a Littafinsa na Fajrul Islam, da yake cewa; “Yahudanci ya bayyana a cikin Shi’anci ta hanyar imani da Raja’a”. Don haka ni nake cewa masa: “Ashe kenan Yahudanci ma ya bayyana a Kur’ani saboda batun Raja’a”. Kamar yadda ya gabata game da ayoyin Kur’ani mai girma da suka ambaci Raja’a.
Kuma zamu kara masa da cewa: A hakika babu makawa wasu akidun Yahudanci da Kirintanci su bayyana a cikin da dama daga akidu da hukunce-hukuncen musulunci, domin Annabi mai girma (S.A.W) ya zo yana mai gaskata Shari’o’i da suka gabata, duk da yake an shafe wasu daga hukunce-hukuncensu. Don haka bayyanar Yahudanci da Kiristanci a wasu abubuwan da musulunci ya yi imani da su ba aibu ba ne cikin musulunci, wannan idan har an kaddara cewa Raja’a tana daga akidojin Yahudawa kenan kamar yadda wannan marubucin yake da’awa.
Ko yaya dai, Raja’a ba tana daga cikin shika-shikan musulunci ba ce da ya wajaba a kudurce ta da yin bincike a kanta, imaninmu da ita bi ne ga hadisai ingantattu da suka zo daga Ahlul Baiti (A.S) wadanda muka yi Imani da kubutarsu daga karya, kuma tana daga cikin al’amuran gaibi da suka ba da labari game da ita, kuma aukuwarta ba mustahili ba ne.

33. Imaninmu Game Da Takiyya

An ruwaito daga Imam Sadik (A.S) a sahihin hadisi cewa: “Takiyya addinina ce kuma addinin iyayena ce”. Da kuma “Duk wanda babu takiyya gare shi babu Addini gare Shi”. Haka nan takiyya ta kasance taken Ahlul Baiti (A.S) wajen kare kai daga cutar da su da kuma mabiyansu, da kare jininsu, da kawo gyara ga halin da musulmi suke ciki, da kuma hada kansu. Takiyya ba ta gushe ba a matsayin alama da ake sanin shi’a da ita tsakanin sauran bangarori na al’ummu, kuma dukkan mutum idan ya ga alamun hatsari ga ransa ko ga dukiyarsa saboda yarda da abin da ya yi imani da shi, ko kuma bayyanar da shi a sarari, to babu makawa ya boye, ya kiyaye a guraren hatsarin, wannan kuwa abu ne da dabi’ar hankali take hukunci da shi. Kuma sannanen abu ne cewa Shi’a da lmamansu sun sha nau’o’in jarrabawa da matsa lamba na tsawon zamani da babu wata jama’a da ta sha irinta. Wannan al’amari ya tilasta su a mafi yawan lokutansu su yi amfani da takiyya, suna masu boye wa masu sabani da su, da kuma barin bayyanarwa, da suturta akidunsa, da ayyukan da suka kebanta da su, saboda abin da yake biyo bayan hakan na daga cutuwa a addini da duniya, wannan shi ne ya sanya suka bambanta da takiyya, aka kuma san su da ita.
Takiyya tana da hukunce-hukunce ta fuskacin wajabcinta da rashin wajabcinta daidai gwargwado sassabawar wuraren tsoron cutuwa da aka ambata a babobinta a littattafan fikihu. Ita ba wajiba ba ce a kowane hali, takan iya zama halal, ko saba mata ya zama wajabi ne a wasu halaye, kamar idan bayyana gaskiya da fitowa da ita sarari ya zama taimako ne ga Addini, da hidima ga Musulunci, da jihadi a tafarkinsa, to a wannan hali dukiya ba komai ba ce, kuma ba za a fifita rai ba. Takiyya tana iya zama haram a ayyukan da sukan iya kai wa ga kashe rayuka masu alfarma, ko yada karya, ko barna a Addini, ko cutarwa mai tsanani a kan musulmi ta hanyar batar da su, ko kuma yada zalunci da ketare haddi a tsakaninsu.
A kowane hali dai, takiyya a gun Shi’a ba ta mayar da su wata kungiyar asiri, domin aiwatar da rushe-rushe da ruguje-ruguje kamar yadda wasu daga cikin makiyan Shi’a marasa fahimtar al’amura suke surantawa, kuma suka ki dora wa kansu nauyin fahimtar ra’ayi ingantacce. Kamar yadda ba ta sanya Addini da hukunce-hukuncensa su zama wani sirri daga asiran da bai halatta a bayyana su ga wanda ba ya imani da su ba, al’amarin bai zama haka ba, alhalin littattafan mazhabar Imamiyya da rubuce-rubucensu na fikihu, da hukunce-hukunce, da bahasosin akida, sun cika gabas da yamma, sun ma wuce yadda ake tsammani daga kowace al’umma da take da wani addini.
Wadanda suke son aibata shi’a sun samu damar amfani da akidarmu ta takiyya, suka sanya ta daga abubuwan da suke sukan su da ita, kamar dai ba sa iya kashe kishirwar gabarsu sai da fille wuyayensu da takubba, da tumbuke asalinsu gaba dayansu a wadancan zamunan da suka gabata, da ya isa a ce wannan dan shi’a ne ya gamu da ajalinsa a hannun makiyan Ahlul Baiti (A.S) na daga Umayyawa, da Abbasawa, da kuma Usmaniyawa. ldan sukan mai son suka ya dogara ne da abin da yake raya rashin shar’ancinsa a addini, to mu sai mu ce masa:
Na Farko: Mu masu biyayya ne ga Imamanmu (A.S) kuma muna bin shiriyarsu ne, kuma su ne suka umarce mu da ita suka wajabta ta a kanmu a lokacin bukata, ita tana daga addini a wajensu, kuma ka ji fadin Imam Sadik (A.S) da yake cewa: “Duk wanda babu takiyya gare shi babu Addini gare Shi.”
Na biyu: Shar’anta ta kuma ya zo a Kur’ani mai girma, da fadarsa madaukaki: “Sai dai wanda aka tilasta shi alhalin zuciyarsa kuwa tana nutse da imani”. Surar Nahli: 106. Wannan aya ta sauka ne game da Ammar Dan Yasir da ya fake da bayyana kafirci saboda tsoron makiyan Musulunci. Da kuma fadinsa madaukaki: “Sai dai in kuka ji tsoron su don kariya”. Surar Ali Imran: 28. Da kuma fadinsa: “Kuma wani mutum daga mutanen fir’auna yana mai boye Imaninsa Ya ce”. Surar Gafir: 28.

Fasali Na Hudu

Abubuwan Da Ahlul Baiti Suka Tarbiyyantar Da Mabiyansu

Shimfida:
Ahlul Baiti (AS) sun sani tuntuni cewa hukumarsu ba za ta taba dawowa garesu a rayuwarsu ba, kuma su da shi’arsu zasu ci gaba da zama a karkashin shugabannin da ba su ba, wadanda suke ganin wajabcin kawar da su da dukkan wata hanyar takurawa da tsanantawa.
Don haka a bisa dabi’a suka riki “Takiyya” addini kuma dabi’a garesu, su da mabiyansu, matukar zata kare masu jininsu kuma ba zata munana wa wasu ko addini ba, saboda su iya wanzuwa a cikin wannan rutsitsi mai ruruwar fitina mai ingizawa ga kiyayya da Ahlul Baiti (AS).
Don haka ya zama tilas suka koma ga koya wa mabiyansu hukunce-hukuncen Shari’ar musulunci, da kuma fuskantar da su fuskantarwa ta Addini ta gari, da kuma sanya su kan hanya ta tafarkin zamantakewa da jama’a mai amfani, domin su zama misalai na musulmi na gari masu adalci.
Wannan dan littafi ba zai iya kawo dukkan bayanai game da tafarkin Ahlul Baiti (A.S) ba, akwai littattafan hadisai masu girma da suka dauki nauyin yada ilimin addini, sai dai ba laifi mu yi nuni da wasu da suke kama da babin akida cikin abin da ya shafi tarbiyyantarwarsu ga shi’arsu da tarbiyyar da zata kai su ga shiga cikin al’amuran zamantakewar al’umma mai amfani, suke kuma kusantar da su zuwa ga Allah madaukaki, suke kuma tsarkake zukatansu daga daudar zunubai da laifuffuka, kuma suke mayar da su adalai masu gaskiya. Kuma magana ta gabata game da takiyya da take daya daga tarbiyya mai amfani ta zamantakewarsu, kuma zamu ambaci sashen abin da ya shafe mu na wadannan ladubban a nan.

34. Imaninmu Game Da Addu’a

Annbin Allah (S.A.W) Ya ce: “Addu’a makamin Mumini ce, kuma jigon Addini ce, kuma hasken sammai da kasa ce”. Shi ya sa ta zama daga siffofin shi’a da suka kebantu da su, hakika sun wallafa abin da ya kai gomomi na manya da kananan littattafai game da falalarta da ladubbanta, da kuma addu’o’in da aka rawaito daga Ahlul baiti (A.S). Kuma an rabuta abin da manzo da Ahlul Baiti (A.S) suke gurin cim masa na kwadaitarwa a kan yin addu’a a cikin wadannan littattafai. Har ma ya zo daga garesu cewa: “Addu’a ita ce mafifciyar ibada”. Da kuma cewa: “Mafi soyuwar aiki a bayan kasa a gun Allah madaukaki ita ce addu’a”. Kuma ya zo cewa: “Addu’a tana mayar da kaddara da bala’i”. Da kuma cewa: “Addu’a waraka ce daga dukkan cuta”.
Kuma ya zo game da Amirul Muminin Ali Dan Abi Dalib (AS) cewa, ya kasance mutum ne ma’abocin addu’a, hakan nan ya kamata shugaban masu Tauhidi kuma shugaban mabiya Ubangiji ya kasance. Kuma addu’o’insa sun zo kamar yadda hudubobinsa suke a matsayin alama daga almomin balagar magana da fasaharta kamar addu’ar Kumail Bn Ziyad wacce ta kunshi ilimin sanin Ubangiji da fuskantarwar Addini, da kuma abin da ya dace ya zamanto madaukakin tafarki ga musulmi na gari.
Hakika addu’o’in da suka zo daga Annabi (S.A.W) da Ahlul Baiti (AS) su ne mafificin tsarin rayuwa ga musulmi -idan ya yi tunani a kansu- sukan cusa masa karfin imani, da karfin akida, da ruhin sadaukar da kai a tafarkin gaskiya, da sanin kansa, da dadin ganawa da Allah, da yankewa zuwa gareshi, kuma tana lakkana masa abin da ya wajaba a kan mutum ya san shi a addininsa, da kuma abin da yake kusantar da shi zuwa ga Allah Madaukaki, ya kuma nesata shi daga barna da son zuciya da bidi’a batacciya. A takaice dai wadannan addu’o’in sun kunshi sanin Addini ta fuskar kyawawan dabi’u da tsarkake zukata, ta wata fuskar kuma sun kunshi akidar Musulunci, kai ita ce ma mafi girman madogarar ra’ayoyin falsafa, da binciken ilimi dangane da sanin Ubangiji da kyawawan dabi’u.
Idan da mutane sun iya kuma ba dukkansu ne masu iyawa ba, da sun shiriyu da shiriyar da wadannan addu’o’in suke kushe da ita a cikin abin da ta kunsa madaukaka, da ba zaka samu irin wannan fasadin da kasa take cike da shi ba, kuma da wadannan rayukan da sharri ya yi musu katutu sun yi shawagi a sammai domin jin gaskiya, sai dai yaya dan Adam zai saurari maganar salihai da masu kira zuwa ga gaskiya alhalin fadinsa madaukaki ya nuna hakikaninsu da fadinsa: “Hakika rai mai umarni da mummuna ce”. Surar Yusuf: 53. “Kuma mafi yawancin mutane ko da kayi kwadayi ba masu shiryuwa ba ne”. Surar Yusuf: 103.
Na’am abin da ya kawo kafuwa da damfaruwar munanan ayyuka ga mutum shi ne, rudin kansa, da jahiltar munanan ayyukansa, da yaudarar kansa cewa shi yana aikata aikinsa, sai ya yi zalunci ya ketare iyaka, ya yi karya, ya yi kage, ya bi sha’awarsa yadda ransa yake so, tare da haka yana yaudarar kansa da cewa shi bai yi komai ba sai abin da ya dace ya aikata, kuma ya runtse dagangan daga munin abin da ya aikata, ya kuma karanta kuskurensa a idanunsa. Wadannan addu’o’in daga hadisai da suke samun karfafa daga tushen wahayi, sun yi kokarin sanya mutum ya koyi zargin kansa da kadaita zuwa ga Allah (S.W.T), domin su cusa masa furuci da kuskurensa da kuma cewa shi mai aikata zunubi ne, wanda ya wajaba a kansa ya yanke zuwa ga ubangijinsa domin neman tuba da gafara. Kamar misalin fadin mai addu’a a cikin Addu’ar Kumail:
“Ya Ubangijina! Ya Majibincina! Ashe zaka gudanar da hukunci a kaina a kan abin da na bi son raina a cikinsa, kuma ban kiyaye kawatarwar abokin gabata ba a cikinsa, don haka ya rude ni da abin da ya so, kuma hukuncinka ya taimake shi a kan haka, har na ketare wasu daga cikin dokokinka saboda abin da ya gudana gare ni na daga hakan, kuma na saba wa wasu daga umarce-umarcen ka.”
Babu shakka cewa misalin irin wannan ikrarin a cikin kadaici ya fi sauki ga mutum a kan ikrari a cikin jama’a, duk da kuwa yana daga cikin mafi tsananin wahalar halaye ga mutum koda kuwa tsakaninsa ne da ransa. Idan da wannan hali zai samu ga mutum, da ya samu sha’ani mai girma na kamala wajan rage takamar kansa mai sharri, da tarbiyyantar da ita a kan alheri. Duk wanda yake son tarbiyyar zuciyarsa, to babu makawa ya koyar da ita kadaitaka da `yantaccen tunani domin yi mata hisabi, kuma mafificiyar hanyar wannan kadaitakar ita ce dukufa a kan karanta wadannan addu’o’in da aka samo daga ruwayoyi, wadanda kuma suke ratsa zuciya, kamar karanta addu’ar Abi Hamza Assumali (R.A.)
“Ya Ubangiji ka rufe ni da suturcewarka, ka yafe mini zargina da girman fuskarka”. Yi tunani a kan wannan kalma “Ka rufe ni”, a cikinta akwai abin da yake tayar wa zuciya kwadayin suturce abin da ta tattara a kai na mummunan aiki, domin mutum ya fadaka a kan wannan al’amari, ta yanda kuma zai san haka idan ya karanta wannan fakara bayan waccan:
“Idan da yau wani baicin kai ya san da zunubina to da ban aikata ba, kuma da na tsoraci gaggauta ukuba da na nisanci zunubin”. Wannan irin furuci daga cikin zuciya, da kuma fadaka zuwa ga kwadayin suturce abin da yake da shi na daga munana, yana tayar da kwadayin neman gafara da yafewa daga Allah (S.W.T) don gudun kada ya tozarta shi a gurin mutane, idan da Ubangiji ya so ya yi masa ukuba a nan duniya ko kuma a lahira a kan ayyukansa, sai mutum ya dandani dadin addu’ar sirri, da zance da Allah a asirce, ya yanke ya koma ga Allah, ya yi godiya gare shi da ya yi masa afuwa alhalin yana da kudura amma bai fallasa shi ba yayin da yake cewa:
“Godiya ta tabbata gareka a kan hakurinka bayan saninka, da yafewarka bayan kudurarka”. Sannan kuma addu’ar ta sake nuna wa rai tafarkin neman uzuri daga abin da ta yi sakaci dangane da shi saboda wannan afuwa da hakuri daga gare shi (S.W.T), domin kada alakar da take tsakanin bawa da Ubangijinsa ta yanke, kuma domin koya wa bawa cewa sabonsa ba wai don kafirce wa Allah ba ne ko kuma wulakanta umarninsa, yayin da yake cewa:
“Kuma hakurinka gare ni yana dauka ta yana ja na zuwa ga saba maka, kuma suturcewarka na kira na zuwa ga karancin jin kunya, kuma sanina game da yalwar rahamarka da girman afuwarka yana gaggautar da ni zuwa ga kifuwa a kan abubuwan da ka haramta”. Wannan shi ne tsarin salon addu’ar a ganawa ta asirce ta tsarkake zukata, da saba wa son ransu, da yin da’a, da barin aikata sabo, da wannan littafi ba zai wadatar ba ya kawo irin wadannan misalai fiye da haka alhalin ga su da yawan gaske.
Salon tattaunawa da Ubangiji domin neman afuwa da gafara yana kayatar da ni, kamar yadda ya zo a Addu’ar Kumail Bn Ziyad: “Kuma kaicona! Ya shugabana majibincina! Ashe ka sallada wuta a kan fuskokin da suka kifu ga girmanka suna masu sujada, da kuma a kan harsunan da suka yi furuci da gasgatawa, kuma suna yabo da godiyarka, da kuma a kan zukata da suke neman ilimi game da kai har suka zamanto masu tsoro, da kuma gabobi da suka yi kokari zuwa guraren ibadarka suna masu biyayya, suka kuma yi ishara ga afuwarka suna masu mika wuya? Ba haka zato yake game da kai ba, ba kuma mune muka fi sanin falalarka ba.”
Ka maimaita karanta wannan fakara sannan ka yi tunani game da taushin wannan irin kafa hujjar da kololuwar fasaharsa, da azancin bayaninsa, a lokaci guda yana mai sanya wa zuciya furuci da takaitawarta ga ibada, kuma tana cusa mata rashin debe tsammani daga rahamar Allah da baiwarsa, sannan kuma tana yi wa zuciya magana da zance na tausasawa ta wani bangare a boye, domin ya cusa mata sanin manyan wajibanta, domin tana kaddara cewa ita dama ta riga ta ba da wadannan wajibai baki daya, sannan kuma tana koya wa mutum cewa da wadannan ayyukan ne yake cancantar falalar Allah da gafararsa, wannan kuwa wani abu ne da kan zaburar da mutum ya koma ga zuciyarsa don ya aikata abin da ya wajaba a kansa idan har bai aikata shi ba.
Karanta wani salon addu’ar da a ke neman uzuri a cikin ta da cewa: “Ya shugabana majibincina! Ka sani ina iya hakuri a kan azabarka amma ta yaya zan yi hakuri a kan rabuwa da kai! Kuma ko da na iya hakuri a kan zafin wutarka amma yaya zan yi hakuri a kan rashin dubi zuwa ga girmanka!”.
Wannan wani irin cusa wa zuciya jin dadin samun kusanci da Allah (S.W.T) ne, da duba zuwa ga karamcinsa da kudurarsa, don soyayya da bege gare shi, da kuma nuna cewa wannan irin jin dadin ya kamata ne ya kai ga darajar da tasirin barinsa a wajan rai ya fi zafin wuta azaba. Idan muka kaddara cewa mutum na iya jure zafin wuta, to da ba zai iya hakuri a kan waccan rabuwar ba, kamar kuma yadda daga wannan bangaren addu’ar za a fahinci cewa wannan soyayyar da jin dadin na kusanci da abin kauna abin bauta shi ne mafificin mai ceto ga mai zunubi a gurin Allah, yadda zai yafe, kuma ya yi masa rangwame. Mamakin taushin wannan salo na kaskantar da kai ga Mai girma, Mai hakuri, Mai karbar tuba, Mai gafarta zunubai, ba zai buya ba.
Babu Iaifi mu rufe wannan bayani da kawo takaitacciyar addu’a da ta kunshi kyawawan dabi’u, da kuma abin da ya kamata kowace gaba ta mutum ko kowane mutum ya siffantu da su na daga siffofi kyawawa ababan yabo:
“Ya Allah ka arzuta mu da muwafakar da’a, da nesantar sabo, da gaskiyar niyya, da sanin abubuwa masu alfarma, kuma ka girmama mu da Shiriya da tsayuwa daidai, da daidaita harsunanmu, da daidaito, da hikima, ka cika zukatanmu da ilimi da sani, ka tsarkake cikkunanmu daga haram da shubuha, ka kame hannayenmu daga zalunci da sata, ka runtsar da idanuwanmu daga fajirci da ha’inci, ka toshe kunnuwanmu daga jin maganar banza da giba, kuma ka yi falala ga malamanmu da zuhudu da nasiha, ga masu neman ilimi kuma da kokari da shauki, ga masu sauraro kuma da biyayya da wa’aztuwa, ga marasa lafiyar musulmi kuma da waraka da hutawa, ga matattunsu kuma da rangwame da rahama, ga tsofaffinmu kuma da nutsuwa da kwanciyar hankali, ga matasanmu kuma da komowa da yawan tuba, ga matanmu kuma da jin kunya da kamewa, ga mawadatanmu kuma da kaskan da kai da yalwatawa, ga matalauta kuma da hakuri da wadatar zuci, ga mayaka kuma da cin nasara da galaba, ga ribatattun yaki kuma da kubuta da hutawa, ga shugabanni kuma da adalci da tausayawa, ga al’umma kuma da yin daidai da kyawun hali. Ka sanya albarka ga mahajjata da masu ziyara da guzuri da ciyarwa, kuma ka hukunta abin da ka wajabta musu na daga hajji da umra don falalarka da rahamarka, Ya mafi rahamar masu rahama”.
Kuma ni ina mai wasiyya ga ‘yan’uwana masu karatu da cewa, kada damar karanta wannan addu’a ta kubuce musu, tare da sharadin yin tunani a kan ma’anoninta da abubuwan da take nufi, tare da halarto da zuciya da fuskantowa zuwa ga Allah da tsoro da kaskan da kai, da kuma karanta ta tamkar yana magana da kansa ne, tare kuma da bin ladubban da aka ambata daga Ahlul Baiti (A.S), Domin karanta ta ba tare da fuskantar da zuciya ba to maganar baka ce kawai, kuma ba ta kara wa mutum sani, ba ta sama masa kusanci, kuma ba ta yaye masa bakin ciki, kuma ba a amsa masa addu’a da haka. “Hakika Allah mai girma da buwaya ba ya karbar addu’a daga zuciya rafkananniya, don haka idan ka yi addu’a ka fuskanto da zuciyarka, sannan ka ji cewa lalle za a amsa”(37).

35. Addu’o’in Sahifatus Sajjadiyya

Bayan aukuwar al’amarin karbala mai ban takaici, da kuma kame ragamar shugabancin al’ummar musulmi da Banu Umayya suka yi, kuma suka dulmuya a cikin danniya, suka yi dumu-dumu da jinin mutane, sannan suka yi watsi da koyarwar Addini, sai Imam Zainul Abidin kuma Sayyiddus Sajidin ya zauna a gidansa yana bakin ciki da jin takaici, yana gida babu wani mai kusantarsa, kuma ba zai iya yada wa mutane abin da ya wajaba a kansu ko ya kamata su sani ba.
Sai ya tilastu a kan ya dauki salon addu’a wanda muka ambata na cewa, yana daga cikin hanyoyin tsarkake zukata a matsayin hanyar yada koyarwar Kur’ani da ladubban musulunci, da kuma sanar da tafarkin Ahlul Baiti (AS), kuma hanyar cusa wa mutane ruhin addini da zuhudu, da abin da ya wajaba na daga gyaran zukata da kuma kyawawan dabi’u.
Wannan hanya ce da ya fare ta a fakaice don koyar da mutane ba tare da ya jawo hankalin azzaluman Shugabanni da suke matsa masa ba, kuma ba zasu iya kafa masa wata hujja ba, don haka ne ya yawaita yin wadannan addu’o’i masu zurfi, kuma an tattara wadansunsu a littafin Sahifatus Sajjadiyya da ake yi wa lakabi da Zaburar Zuriyar Muhammad (S.A.W). Salonta da manufofinta sun zo da siga da salon Larabci mafi daukaka, kuma mafi daukakar addini, da mafi ingancin asiran tauhidi da annabci, kuma mafi ingancin hanyar koyar da kyawawan dabi’u ababan yabo, da kuma ladubban musulunci. Kuma ta kunshi maudu’ai daban-daban ne na tarbiyya ta Addini da ta shafi koyarwar Addini, da kyawawan dabi’u, ta hanyar addu’a, ko kuma addu’a ce amma da salon koyar da Addini da kuma kyawawan dabi’u. Ita ce salon bayanin Larabci mafifici, kuma mafi daukakar mashayar manufar sanin Ubangiji da kyawawan dabi’u bayan Kur’ani da Littafin Nahjul Balagha.
Daga cikinsu akwai wanda yake sanar da kai yadda zaka daukaka Allah kuma ka tsarkake shi, da yabonsa da gode masa da komawa zuwa gareshi. Daga ciki akwai wacce take sanar da kai yadda zaka yi zance da Allah, da kebewa da shi da sirrinka, da yankewa zuwa gareshi, daga cikinta akwai wadanda ke shimfida maka ma’anar Salati ga Annabi (S.A.W) da manzannin Allah da zababbunsa daga cikin halittunsa, da yadda ake yin sa, daga cikinsu akwai wadanda zasu fahimtar da kai abin da ya dace ka bi iyayenka da shi, da kuma abin da zai yi maka sharhin hakkokin Uba a kan dansa, da na da a kan mahaifinsa, ko kuma hakkokin makwabta, ko na dangi, ko hakkokin musulmi baki daya, ko hakkokin matalauta a kan mawadata da kuma akasin haka. Daga cikin addu’o’in akwai wadanda zai fadakar da kai kan abin da ya wajaba na basussukan mutane a kanka, da kuma abin da ya kamata ka sani na al’amuran tattalin arziki da dukiya, a abin da ya kamata ka yi mu’amala da shi ga abokanka da sauran mutane baki daya, da wadanda kake neman yin mu’mala da su a maslaharka, da kuma abin da zai hada maka dukkan kyawawan dabi’u, kuma ya zama maka tafarki cikakke na ilimin kyawawan dabi’u.
Daga cikinsu akwai wadanda zasu koya maka yadda zaka yi hakuri a kan munanan abubuwan da suke faruwa, da kuma yadda zaka yi yayin da kake rashin lafiya, da kuma yayin da kake lafiya lau. Daga cikinsu akwai wadanda suke yi maka sharhin ayyukan wajibi da suka hau kan sojojin musulunci da wajiban mutane dangane da su, da dai sauran wadannan da kyawawan dabi’u abin yabo suke farlanta su, duk ta hanyar addu’a. Abubuwan da suke kunshe cikin addu’ar imam su ne:
Na farko: Sanin Allah da girman kudurarsa, da bayanin kadaita Shi, da tsarkake shi da mafi zurfin kalmomi na ilimi, wannan kuwa yana maimaituwa ne a kowace addu’a da salo daban-daban, kamar yayin da kake karantawa a addu’a ta farko: “Godiya ta tabbata ga Allah na farko wanda babu wani na farko da ya kasance kafin shi, na karshen da babu wani na karshe da zai kasance bayansa, wanda idanuwan masu gani suka gaza ganin sa, wahamce-wahamcen masu siffantawa suka gajiya wajen siffanta Shi, Ya fari halittu da kudurarsa a farkon farawa, ya kuma kago su kamar yadda ya so kagowa.”. Karanta ma’anar na farko da na karshe da kyau da kuma tsarkake Allah (S.W.T) daga kasancewar wani gani ko wahami ya kewaye shi, da kuma tunani kan zurfin ma’anar halittawa da samarwa.
Sannan ka karanta wani salon wajen bayyana kudurar Allah da tadabburi a cikin addu’a ta 6: “Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya halitta dare da rana da karfinsa, ya rarrabe tsakaninsu da kudurarsa, ya sanya wa kowanne daga cikinsu iyaka ayyananniya, yana shigar da kowane daya daga cikinsu a cikin dan’uwansa, da kaddarawarsa ga bayi a cikin abin da yake ciyar da su, kuma yake sanya su su girma. Sai ya halitta musu dare domin su huta daga wahalar kaiwa da komowa da dawainiya, kuma ya sanya shi sutura domin su lulluba da hutunsa, sai ya zama wartsakewa da karfi garesu domin su sami jin dadi da sha’awa da shi. Har zuwa karshen abubuwan da ya ambata na fa’idar halittar rana da dare, da kuma abin da ya kamata mutum ya yi godiyarsa na daga wadannan ni’imomi.
A wani salon kuma na bayanin dukkan al’amura a hannun Allah (S.W.T) suke zaka karanta a addu’a ta 7 cewa: “Ya wanda da Shi ne ake warware kulle-kulle! Ya wanda da shi ne kaifin tsanani yake dakushewa! Ya wanda daga gareShi ake neman mafita zuwa yalwar sauki! mawuyatan al’amura na rusunawa ga kudurarka! sabubba suna tasiri ne da ludufinka, kuma kaddarawarka ta gudana ne a bisa ikonka, abubuwa suna zartuwa da nufinka ne, suna masu umartuwa da nufinka ba tare da fadarka ba, kuma masu tsawatuwa ne da nufinka ba tare da haninka ba.
Na Biyu: Bayani game da falalar Ubangiji ga bawansa, da kuma gazawar bawa wajen bayar da hakkin Ubangiji komai abin da ya yi na da’a da ibada kuwa, da kuma yankewa domin komawa zuwa ga Ubangiji kamar yadda kake karantawa a addu’a ta 37: “Ya Allah hakika babu wani da zai kai ga matukar godiya gare ka sai wata Kyautatawarka ta same shi wacce zata sake lizimta masa wata godiyar, kuma ba ya kaiwa ga matukar da’arka koda kuwa ya dage sai ya gaza yin yadda ka cancanta ga falalarka, Mafificin mai godiya gareka a bayinka ya gaza a kan godiyarka, kuma mafi bautarsu mai takaitawa ne ga bautarKa”.
Saboda girman ni’imomin Allah (S.W.T) kan bawansa da ba su da iyaka bawan ya yi kadan ya ba da hakkinsa komai kokarin da ya yi, yaya kenan idan kuma ya sabe shi yana mai tsaurin kai, yayin nan kuma ba zai taba iya kankare sabo koda guda daya ba, kuma wannan shi ne abin da fakara mai zuwa ta addu’a ta 16 take nunawa: “Ya Ubangijina idan da zan yi kuka har fatar idona ta fadi, kuma na yi kururuwa har muryata ta dushe, kuma na tsaya gare ka har kafafuwana su tsattsage, kuma in yi ruku’u gareka har bayana ya sance, kuma na yi maka sujada har kwayoyin idanuna su faffado, kuma turbayar kasa ta cinye duk tsawon rayuwata, kuma na sha ruwan toka har zuwa karshen rayuwata, sannan na yi ta ambaton ka duk tsawon wannan lokacin har sai harshena ya gaza, sannan kuma na zama ban taba daga ganina na dubi sama ba don jin kunyar ka, duk wannan ba zai wajabta shafe mini mummunan aiki daya daga munanan ayyukana ba”.
Na uku: Sanar da lada da azaba, da aljanna da wuta, da kuma cewa ladan Ubangiji dukkaninsa kyauta ne kawai, kuma bawa yana cancantar azaba ne da mafi karancin sabo da ya yi, kuma Ubangiji yana da hujja a kansa game da haka.
Haka nan dukkan addu’o’in Sahifatus Sajjaddiya sun kawo maganar irin wannan azaba mai tasiri, domin tsoratarwa da sanya tsoro a zuciya, da sanya mata sa tsammani da ladan Ubangiji, dukkan wannan shaida ce a kan haka ta salo daban- daban da yake sa wa zuciya tsoro kan sabo. Kamar abin da zaka karanta a addu’a ta 46:- “Hujjarka tabbatacciya, Shugabancinka tsayayye ne ba ya gushewa, don haka tsananin azaba madawwamiya ta tabbata ga wanda ya nisance ka, tabewar tozartuwa ta tabbata ga wanda ya karkace daga gareka, tsiyacewa ta tabbata ga wanda ya rudu ya bar ka, jujjuyawarsa a azabarka ta yawaita, kaikawonsa a cikin ukubarka ya tsawaita, bukatarsa ga burinsa na samun sauki ya nisanta, saukin samun mafitarsa abin yanke kauna ne, adalci ne daga hukuncinka ba ka zalunci a cikinsa, kuma yin daidai a hukuncinka ba ya kaucewa, hakika ka bayyanar da hujjoji kuma ka jarraba uzurori”.
Kuma kamar yadda kake karanta addu’a ta 31: “Ya Allah! ka ji kan kadaitakata ta gabanka, da kidimewar zuciyata daga tsoronka, da firgicewar gabobina don haibarka, kuma ya Ubangijina! zunubina ya sanya ni a matsayin kaskanci a farfajiyarka, idan na yi shiru babu wani da zai yi magana madadina, idan kuma na nemi a cece ni to ni ban cancanci ceto ba.”.
Kamar kuma karantawarka a addu’a ta 39: “Domin kai idan har ka saka mini da gaskiya to zaka halakar da ni, idan kuma ba ka lullube ni da rahamarka ba to zaka halakar da ni, kuma ina rokon ka ka dauke daga zunubina wanda daukar nauyinsa ya gajiyar da ni, ka yi tsira ga Muhammad da Zuriyarsa, kuma ka ba wa raina kanta saboda zaluncinta”.
Na Hudu: Jan mai addu’a zuwa ga dauke sawunsa daga aikata munanan ayyuka, da siffantuwa da munanan siffofi domin wanke ruhinsa da tsarikake zuciyarsa, kamar yadda kake karantawa a addu’a ta 20: “Ya Allah ka cika mini niyyata da ludufinka, kuma ka inganta mini yakinina da abin da yake gare ka, ka gyara min abin da ya baci daga gare ni da kudurarka, Ya Allah! Ka yi tsira ga Muhammad da Zuriyar Muhammad ka jiyar da ni dadi daga shiriya ingantacciya da ba zan taba neman musanya daga gareta ba, da kuma hanya ta gaskiya wacce ba zan taba karkacewa daga kanta ba, da kuma niyyar shiriya da ba zan taba kokwanto a cikinta ba.
Ya Allah kada ka bar wani hali da yake aibi ne da ake aibata ni da shi sai ka gyara shi, ko kuma wani laifi da za a zarge ni da shi sai ka kyautata shi, ko kuma wani halin karimci da yake tauyayye gare ni har sai ka cika Shi”.
Na biyar: Sanya wa mai karanta addu’ar dauke sawunsa daga mutane, da rashin kaskantar da kansa gunsu, kuma kada ya kai kukan bukatarsa gun wani ba Allah ba, domin kwadayin abin da yake hannun mutune yana daga cikin mafi munin abin da mutum zai siffantu da shi kamar yadda zaka karanta a addu’a ta 20: “Kuma kada ka fitine ni da neman taimakon waninka idan na matsu, da kuma kaskan da kai don tambayar wani ba kai ba idan na bukatu, da kuma mika wuya gaba ga wanda ba kai ba idan na tsorata, saboda haka sai in cancanci tabarwarka da haninka da kawar da kanka”.
Da kuma misalin addu’a ta 28: “Ya Allah ni na tsarkake niyyata da yankewa zuwa gareka, kuma na juyo zuwa gareka baki daya, kuma na kawar da fuskata daga dukkan wanda bai wadata da falalarka ba, na ga cewa bukatar mabukaci zuwa ga wani mabukacin wauta ce, kuma bacewar hankalinsa ne.”
Da kuma misalin abin da kake karantawa a addu’a ta 13: “Duk wanda ya yi kokarin magance rashinsa ta gurinka, kuma ya yi kokarin kawar da talauci da taimakonka, hakika ya nemi bukatarsa a gurin da ake tsammani, kuma ya zo wa bukatarsa ta gurin da ake zaton samu, kuma ya zo wa bukatarsa ta fuskarta da ta dace. Wanda kuma ya juya da bukatarsa kuwa ga daya daga cikin halittunka, ko kuma ya sanya shi sababin samunta ba kai ba, to hakika ya jawo wa kansa hani, kuma ya cancanci kubucewar kyautatawa daga gare ka”.
Na Shida: Koya wa mutane wajabcin kiyaye hakkokin wasu, da taimaka wa sashensu ga sashe, da fifita juna a tsakaninsu domin tabbatar da ma’anar yan’uwantakar Musulunci, kamar yadda kake karantawa a addu’a ta 38: “Ya Allah! ni ina mai neman uzuri daga gareka a kan dukkan wani da aka zalunta a gabana amma ban taimake shi ba, da wani kyakkyawan abu da aka kwararo mini shi amma ban yi godiyarsa ba, da duk wani mummunan aiki da aka nemi uzurina ban bayar da uzuri ba, da duk wani mabukaci da ya roke ni ban ba shi ba, da hakkin mai hakki da ya hau kaina daga muminai amma ban cika masa ba, da kuma daga dukkan wani aibi na mumini da ya bayyana gare ni amma ban suturce shi ba”.
Hakika irin wannan neman uzuri yana daga cikin mafi bayyanar abin da zai fadakar da zuciya zuwa ga abin da aikata shi ya kamata na wadannan kyawawan dabi’u madaukaka.
A addu’a ta 39 akwai karin haske a kan hakan, sai ya sanar da kai yadda zaka yafe wa wanda ya munana maka, kuma yana gargadin ka game da yin ramuwar gayya, yana kuma daukaka zuciyarka zuwa matsayin tsarkakku: “Ya Allah duk wani bawa da ya yi mini abin da na hana shi a kansa, ya kuma keta mini abin da na kange shi gareshi, da nauyin zaluntata, ko zuciyata ta tuna shi yana rayayye, to ka gafarta masa abin da ya yi mini, ka yafe masa abin da ya riga ya gabatar gareni, kada ka tsayar da shi don tambaya a kan abin da ya aikata a kaina, kuma kada ka tona asirinsa a kan abin da ya aikata a kaina, kuma ka sanya rangwamen da na yi masa na afuwa gare su, da kuma kyautar da na yi musu na daga sadaka garesu, ya zama mafi tsarkin sadakar masu sadaka, kuma mafi daukakar addu’ar ma’abota kusanci gare ka. Kuma ka musanya mini afuwata gare su da afuwarka, da addu’ata garesu da rahamarka, har kowanne daga cikinmu ya rabauta da falalarka”.
Mamaki ya girmama ga wannan fakarar ta karshe! da kuma yawan girman tasirinta a cikin zukatan masu alheri! Domin fadakar da su a kan kyakkyawan nufi ga dukkan mutane, da nema wa kowa sa’ada hatta ga wanda ya zalunce su. Irin wannan yana da yawa a cikin addu’o’in Sahifatus sajjadiyya, a cikinta akwai da yawa daga irin wadannan koyarwa ta ubangiji don tsarkake rayukan ‘yan Adam wacce da sun yi riko da ita da sun kasance masu shiryuwa.

36. Imaninmu Game Da Ziyartar Kaburbura

Ziyarar kaburburan -Annabi da na Imamai- da katange su da kuma yin gine-gine a kansu suna daga cikin al’amuran da Shi’a suka kebantu da su, kuma suna sadaukar da dukkan abu mai tsada da mai sauki a cikin imani da dadin rai.
Wannan kuwa asalinsa yana komawa ne zuwa ga wasiyyar Imamai da zaburar da mabiyansu kuma da kwadaitar da su a kan irin ladan da yake da shi mai yawa a gurin Allah madaukaki, saboda kasancewarta daga mafifitan ayyukan biyayya da kusanci da Allah bayan ayyukan ibadu wajibai, da kuma cewa kaburburan suna daga cikin mafifitan guraren amsa addu’a da yankewa zuwa ga Allah (S.W.T).
Kuma sun sanya wannan daga cikin cika alkawura ga Imamai, domin ga kowane imami akwai alkawarinsa a kan wuyan mabiyansa, kuma ziyartarsu tana daga mafificin cika alkawari, duk wanda ya ziyarce su yana mai kwadayin haka da gaskata abin da suka kwadaitar a kai, to zasu kasance masu cetonsa a ranar lahira(38).
Akwai fa’idoji masu yawa na Addini da zamantakewa a cikin ziyartar kaburbura da suka sa Imamanmu himmantuwa da ita, domin bayan dada karfin soyayya da mika wuya da kauna tsakanin imamai da mabiyansu, hada da sabunta ambatonsu da tuna kyawawan dabi’unsu, da jihadinsu a tafarkin gaskiya, tana kuma hada musulmi daban-daban wadanda suke warwatse a waje daya domin su san juna, kuma ta dasa ruhin mikuwa zuwa ga Allah a cikin zukatansu, da yankewa zuwa gare shi da bin umarninsa, tana cusa musu hakikanin tauhidi a cikin ma’anonin addu’o’in ziyarorin da suke cike da fasaha wadanda aka samo daga Ahlul Baiti (AS), tare da koya musu tsarkin musulunci da sakonsa, da abin da ya wajaba a kan musulmi na daga dabi’u madaukaka, da kaskan da kai ga mai tafiyar da al’amuran halitta (S.W.T), da gode wa ni’imominsa, don haka ta wannan bangaren tana amfani ne irin na addu’o’in da aka ruwaito wadanda bayaninsu ya gabata. Wasunsu ma suna dauke da sama da haka, kuma mafi daukakarta kamar ziyarar “AminulLahi” wacce take ziyara ce da aka rawaito daga Imam Zainul Abidin (A.S) yayin da ya ziyarci kabarin kakansa imam Ali (A.S).
Kamar yadda wadannan ziyarorin da aka ruwaito suke fahimtar da matsayin imamai (AS) da irin sadaukarwarsu a tafarkin taimakon gaskiya, da daukaka kalmar Addini da kadaitarsu ga ibadar Allah (S.W.T), ga shi kuma sun zo da salon larabci mai fasaha madaukakiya, da ma’anoni masu sauki wadanda kowa yake iya fahimta, kuma suna kunshe da mafifitan ma’anonin tauhidi masu zurfi, da addu’a, da yankewa zuwa gare shi madaukaki. Hakika tana daga cikin mafi ingancin ladubban Addini bayan Kur’ani mai girma da Nahjul Balaga da kuma addu’o’in da aka ruwaito daga garesu (AS), domin a cikinta akwai takaitaccen bayanin sanin Imamai (AS) game da abin da ya shafi sha’anin Addini da gyaran zuciya a dunkule.
Sannan a cikin ladubban ziyarar akwai koyarwa da shiryarwar da ke karfafa tabbatar da samuwar wadannan dabi’u na Addini madaukaka, wanda ya hada da daukaka tsarkin ruhin musulmi, da yaduwar tausasawa ga fakiri, da iya zamantakewa da al’umma, da son cudanya da jama’a, domin daga ladubbanta akwai abin da ya kamata a aikata kafin a fara shiga cikin ginin makabartar domin ziyartarsa.
Daga nan kuma akwai abin da ya kamata a yi a tsakiyar ziyarar, da kuma bayan ziyarar, da mu a nan zamu bujuro da sashen wadannan ladubban domin fadakarwa kan manufarta da muka ambata:
1- Daga ladubbanta, mai ziyarar ya yi wanka yayin fara ziyararsa ya tsarkaka, fa’idar wannan kuwa cikin abin da muka fahimta a fili take, ita ce mutum ya tsarkake jikinsa daga dauda, domin ya kubutar da shi daga rashin lafiya da cututtuka, kuma domin kada mutane su gundura (39) da warinsa, ya kuma ya tsarkake kansa daga kazanta. Hakika ya zo a cikin hadisai cewa; mai ziyara ya karanta wannan addu’a bayan ya kare wanka domin fadakar da shi game da wadancan manufofi madaukaka, sai ya ce: “Ya Allah ka sanya mini haske da tsarki tare, da kuma tsari mai isarwa ga dukkan cuta da ciwo da dukkan aibi, kuma ka tsarkake zuciyata, da gabobina, da kasusuwana, da namana, da jinina, da gashina, da fatata, da bargona, da kashina, da kuma abin da kasa ta dauke shi daga gare ni, kuma ka sanya mini halarta ranar bukatata da fakirancina da talaucina.”
2- Ya sanya mafi kyawu kuma mafi tsaftar tufafin da yake da su, domin sanya kyawawa da tsaftatattun tufafi a taron jama’a abu ne da mutane suke so wa junansu, kuma yake kusantar da su ga junansu, tare da kara musu daukaka da jin daukaka a bukin da suke halartarsa.
Daga abubuwan da suka kamata mu jawo hankali garesu a wannan koyarwa su ne, ba a wajabta wa mai ziyara sanya mafi kyawun tufafi baki daya ba, sai dai ya sanya mafi kyawun abin da zai iya, domin ba kowa ne zai iya yin haka ba, kuma akwai takurawa ga talakawa, al’amarin da tausayawa ba ta bukatar a yi haka, sai ya zamanto ya hada tsakanin wannan tarbiyya da abin da ya kamata na kawa da kuma kiyaye halin talaka da mai raunin hali.
3- Ya sanya turare matukar yana da shi, wannan fa’idarsa tamkar ta sanya sababbin tufafi ce.
4- Ya yi sadaka ga fakirai da abin da ya saukaka gare shi, kuma fa’idar sadaka a irin wannan al’amari sananniya ce, domin a cikin hakan akwai taimaka wa gajiyayyu, da kuma karfafa ruhin tausasawa gare su.
5- Ya tafi yana mai nutsuwa da kwanciyar hankali, mai runtse ganin idonsa, abin da yake cikin irin wannan nutsuwar na girmama alfarmar wannan gurin, da kuma wanda ake ziyarta, da fuskanta zuwa ga Allah madaukaki, da yankewa zuwa gare shi, ba boyayye ba ne, tare da abin da hakan ya kunsa na nisantar damun mutane da matsa musu a yayin wucewa, da kuma rashin munana wa sashensu ga sashe.
6- Ya yi kabbara da fadin: “Allahu Akbar” ya yi ta maimaitawa yadda ya so, a wasu ziyarorin an kayyade kabbarorin zuwa dari. Akwai fa’idar jin rai ga girman Allah a cikin yin haka, da kuma cewa ziyara ba komai ba ce sai bauta ga Allah da girmama shi da tsarkake shi ta hanyar raya alamomin Allah da karfafa Addininsa.
7- Bayan kammala ziyarar ga Annabi ko ga Imami sai ya yi salla mafi karanci raka’a biyu domin bauta ga Allah da godiya gareshi saboda dacen da ya yi masa, ya kuma bayar da ladanta ga wanda ya kai wa ziyarar. A cikin addu’ar da aka ruwaito wacce mai ziyarar zai karanta bayan wannan salla akwai abin da zai fahimtar da mai ziyarar cewa, wannan sallar tasa da aikinsa duk don Allah ne shi kadai, da kuma cewa shi ba ya bauta wa waninsa, ziyarar ba wata abu ba ce sai wani nau’in neman kusanci zuwa gareShi madaukaki.
“Ya Uabangiji gareka na yi salla, gare ka na yi ruku’u, gareka na yi sujada, kai kadai ba ka da abokin tarayya, domin salla da ruku’u da sujada ba sa kasancewa sai gareka, domin kai hakika kai ne Allah babu abin bautawa sai kai. Ya Uabangiji ka yi tsira da aminci ga Muhammad da zuriyar Muhammad kuma ka karbi ziyarata, ka kuma ba ni abin da na roka, domin Muhammad da zuriyarsa masu tsarki.”
A cikin irin wannan nau’in na ladabi, akwai abin da yake bayyana wa wanda yake son fahimtar hakikanin manufofin Imamai (A.S) da mabiyansu masu koyi da su a ziyartar kaburbura, da kuma abin da yake toshe bakin masu nuna jahilta da suke raya cewa, ziyarar kaburbura ibada ce gare su da neman kusanci gare su, kuma shirka ce da Allah. Abin zato a nan shi ne cewa, hadafin wadannan shi ne, nesantar da jama’a daga abin da yake jawo wa jama’ar imamiyya amfanin zamantakewa da na addini a bukukuwan ziyara, domin ya zama tsakuwar ido ga masu kiyayya da Ahlul Baiti (A.S), in ko ba haka ba, ba ma tsammanin wadannan mutane suna jahiltar hakikanin manufar Ahlul Baiti (A.S), mustahili ne ga wadannan da suka tsarkake niyyarsu ga Allah, suka kadaitu da ibada, suka bayar da rayukansu wajan taimakon addini, su kira mutane zuwa ga shirka da Allah.
8- Daga ladubban ziyara akwai cewa: Mai ziyara ya lizimci kyautata abotakar wanda yake tare da shi, da karanta magana sai dai da ta alheri, da yawaita ambaton Allah, da kaskan da kai, da yawaita salla, da salati, da runtse idanuwansa, kuma ya taimaka wa mabukata daga cikin yan’uwansa idan ya ga guzirinsu sun yanke, da taimaka musu, da tsantseni kan abin da aka hana, da kuma husuma, da yawaita rantsuwa da jayayya(40).
Sannan hakikanin ziyara ba komai ba ne sai salati ga Annabi (S.A.W) da Alayensa, da la’akarin cewa “Su rayayyu ne ana arzuta su gun Ubangijinsu”. Kuma suna jin magana suna amsawa, kuma ya isa ya ce: Assalamu alaika ya RasulalLah! Sai dai abin da ya fi, ya karanta abin da aka rawaito na hadisai da suka zo game da ziyara daga Ahlul Baiti (A.S), saboda abin da yake cikinta na daga manufofi madaukaka da fa’idoji na addini, tare da balagarta da fasaharta, da kuma abin da yake cikinta na daga addu’o’i madaukaka da mutum yake fuskanta zuwa ga Allah makadaici a cikinta.

37. Imaninmu Game Da Ma’anar Shi’anci Wurin Ahlul Baiti

Ahlul Baiti (AS) ba su da wata himma bayan sun debe tsammanin al’amarin al’umma ya dawo hannunsu sai gyara halin musulmi da tarbiyyantar da su tarbiyya ta gari kamar yadda Allah (S.W.T) yake so daga garesu. Don haka suka kasance tare da duk wanda yake bin su, kuma suka aminta da shi a kan sirrinsu, suna bayar da kokarinsu wajen koya masa hukunce-hukuncen Shari’a, da cusa masa ilimin addini, da sanar da shi abin da yake nasa, da kuma wanda yake kansa.
Ba sa daukar mutum cewa mabiyinsu ne kuma shi’arsu sai idan ya kasance mai bin umarnin Allah, mai nisantar son zuciyarsa, mai riko da koyarwarsu da shiryarwarsu. Kuma ba sa ganin son su ya wadatar wajen tsira, kamar yadda wasu suke raya wa kansu daga cikin masu holewa da bin sha’awece-sha’awece da son ransu wadanda ke neman hanyar fandare wa bin Allah. Imamai ba sa daukar sonsu da biyayya garesu mai tseratarwa ne sai dai idan ta hadu da kyawawan ayyuka, kuma mabiyansu sun siffantu da gaskiya da rikon amana, da tsentseni da tsoron Allah.
“Ya Khaisama! ka isar daga garemu cewa ba zamu wadatar da su daga komai ba sai da aiki, kuma ba zasu samu soyayyarmu ba sai da tsentseni, kuma mafi tsananin hasarar mutane ranar alkiyama shi ne wanda ya siffanta adalci sannan kuma ya saba masa zuwa ga waninsa”(41).
Su suna son mabiyansu su zamanto masu kira zuwa ga gaskiya ne, masu shiryarwa zuwa ga alheri da shiriya, kuma suna ganin cewa kira a aikace ya fi kira da harshe isarwa: “Ku kasance masu kiran mutane zuwa ga alheri ba da harsunanku ba, su ga kokari da gaskiya da tsentseni daga gare ku”(42).
A yanzu zamu kawo maka wasu muhawarori da suka gudana tsakaninsu da wasu daga cikin mabiyansu domin ka san matukar tsanantawarsu da kwadayinsu a kan gyara dabi’un mutane:
1- Muhawarar Abu Ja’afar Bakir (AS) shi da Jabir Ju’ufi(43): “Ya Jabir! Ashe ya isa ga wanda ya siffantu da cewa shi shi’a ne ya yi da’awar yana son mu? Wallahi! Ba kowa ne shi’armu ba sai wanda ya ji tsoron Allah ya bi shi”.
“Su ba a gane su sai da kaskan da kai, da tsoron Allah, da rikon amana, da yawan zikiri, da azumi, da salla, da bin iyaye, da taimakon makwabta na daga fakirai, da mabarata, da masu bashi, da marayu, da gaskiyar magana, da karatun Kur’ani, da kame harshe daga ambaton mutane sai dai da alheri, kuma su ne aminan jama’arsu a kan al’amura. Ku ji tsoron Allah ku yi aiki saboda abin da Allah ya tanada, kuma babu wata dangantaka tsakanin Allah da wani, kuma mafi soyuwar bayi a wajan Allah wanda suka fi jin tsoronsa suka fi biyayya gareshi. Ya Jabir! Wallahi ba mu kusanta zuwa ga Allah sai dai da da’a, kuma babu kubuta daga wuta a gare mu, kuma babu wani mai hujja a kan Allah, duk wanda ya kasance mai biyayya ga Allah to shi masoyi ne gare mu duk wanda ya kasance mai sabo ne ga Allah to shi makiyi ne gunmu, kuma ba a samun soyayyarmu sai da aiki da tsentseni.
2- Tattaunawar Abu Ja’afar (AS) da Sa’id Bn Hasan(44):
Abu Ja’afar (AS) “ Shin dayanku zai zo ga dan’uwansa ya sanya hannunsa a jakarsa ya dauki abin da yake so bai cire shi ba?
Sa’id: Ban san da haka ba a cikinmu.
Abu Ja’afar (AS): To Babu komai kenan.
Sa’id: To halaka ke nan.
Abu Ja’afar (AS): Mutane ba a cika hankulansa ba tukuna.
3- Muhawar Imam Sadik (A.S) da Abu Sabah Alkinani(45).
Alkinani: Muna shan wahalar mutane game da ku.
Abu Abdullah: Menene abin da kuke gamuwa da shi daga mutane?.
Alkinani: Magana ba ta gushewa tsakaninmu da mutun, sai ya ce: Wannan Dan Ja’afariyya ne mugu.
Abu Abdullahi: Mutane suna aibata ku da ni?
Alkinani: E mana.
Abu Abdullah: Wallahi karancin mai bin Ja’afar a cikinku ya yawaita! Kadai sahabbaina shi ne wanda tsantseninsa ya tsananta, ya yi aiki don mahaliccinsa ya kaunaci ladansa, wadannan su ne sahabbaina!
4- Abu Abdullahi (AS) yana da wasu maganganu game da wannan al’amari da zamu kawo wasu kamar haka:
A- “Baya daga cikinmu sam, wanda ya kasance a wani gari da a cikinsa akwai mutane dubu dari ko fiye da haka, ya zama a cikin garin akwai wanda ya fi shi tsantseni”.
B- “Mu ba ma kirga mutum mumini har sai ya zamanto mai biyayya ga dukan umarninmu yana mai nufi, ku sani daga cikin bin umarninmu da nufinsa akwai tsentseni, don haka ku yi ado da shi Allah ya yi muku rahama”.
C- “Wanda mata masu tsari ba sa magana game da tsantsaninsa ba ya daga cikin shi’armu, haka nan wanda ya kasance a cikin wata alkarya mai mutane dubu goma, a cikinsu akwai wata halitta ta Allah da ta fi shi tsentseni, shi ba ya daga cikin masoyanmu”.
D- “Kadai shi’ar -Ja’afar- shi ne wanda ya kame cikinsa da farjinsa, kokarinsa ya tsananta, kuma ya yi aiki ga mahaliccinsa, ya kaunaci ladansa, ya ji tsoron azabarsa, to idan ka ga wadannan to wadannan su ne shi’ar Ja’afar.

38. Imaninmu Game Da Zalunci

Ketare haddin wani da zaluntar mutane suna daga cikin mafi girman abubuwn da Imamai (AS) suke girmama muninsa, wannan kuma bi ne ga abin da Kur’ani ya zo da shi na daga tsoratarwa game da zalunci da munana shi, kamar fadinsa madaukaki: “Kada ka tsammaci Allah mai sha’afa ne game da abin da azzalumai suke aikatawa, sai dai kawai yana jinkirta musu ne saboda ranar da idanuwa zasu zazzaro”. (Surar Ibrahim: 42)
Hakika abin da yake kai matukar bayyana munin zalunci da kyamarsa ya zo a maganganun Amirul Muminin Ali Dan Abi Dalib (AS), kamar fadinsa shi mai gaskiya ne abin gaskatawa, a Nahjul balaga huduba ta 219: “Wallahi idan da za a ba ni Sammai bakwai da kuma abin da yake kasan falakinta, a kan in saba wa Allah game da tururuwa da in kwace mata Sha’irin da ta jawo, ba zan aikata ba”. Wannan shi ne matukar abin da mutum zai iya surantawa game da kame kai da tsoratarwa daga zalunci da kyamar yinsa.
Shi ba zai zalunci tururuwa ba a kan kwayar sha’ir koda kuwa an ba shi sammai bakwai, to yaya halin wanda yake zubar da jinin musulmi, yake handame dukiyoyin mutane, yake cin mutuncinsu? Yaya za a auna tsakaninsa da aikin Amirul Muminin? Kuma yaya matsayinsa da iliminsa (AS)? Wannan ita ce tarbiyyantarwar Ubangiji da addini yake bukatar ta daga kowane mutum.
Na’am, hakika zalunci yana daga mafi girman abubuwan da Allah ya haramta, saboda haka ne zarginsa ya zama abu na farko da ya zo a hadisan Ahlul Baiti da addu’o’insu, da kuma nesantar da mabiyansu daga gare shi.
Wannan ita ce siyasarsu, kuma a kanta suke mu’amala hatta da wanda yake yi musu shisshigi yake rashin kunyar hawa matsayinsu. Kissar imam Hasan (AS) game da hakurinsa ga mutumin Sham wanda ya yi masa tsaurin ido ya zage shi, shi kuma ya tausaya masa ya kuma tausasa masa, har sai da shi ya ji kunyar mummunan abin da ya aikata. Kuma ka riga ka karanta abin da ya gabata a addu’ar shugaban masu sujjada na daga ladubba madaukaka game da afuwa ga masu ketare iyaka, da nema musu gafara. Wannan kuma shi ne matukar daukakar ran mutum da kamalar mutumtakarsa, duk da kuwa ketare haddin azzalumi kwatankwacin yadda ya ketara ya halatta a shari’a, kamar yadda yin addu’a a kansa ya halatta, sai dai halacci wani abu ne, afuwa kuma wacce take daga kyawawan dabi’u wata aba ce daban, kai gun imamai shige gona da iri wajan yin addu’a a kan azzalumi ana kirga shi zalunci.
Imam Sadik (A.S) ya ce: “Bawa yana kasancewa abin zalunta, ba zai gushe ba yana ta yin addu’a har sai ya zamanto azzalumin”. Idan wannan shi ne halin wanda aka zalunta to yaya halin wanda ya fara zalunci da ketare iyakar tun karon farko yake kuma cin mutuncinsu, yana kwashe dukiyarsu, yana munafuncinsu gun azzalumai, ko yake yaudarar su, yana jefa su cikin halaka, ko ya cutar da su, ko ya yi leken asiri a kansu!? Irin wadannan a wajan Ahlul Baiti (AS) su ne mafi nisantar mutane a wajan Allah, mafi tasananinsu sabo da azaba, mafi muninsu ayyuka da dabi’u.

39. Imaninmu Game Da Taimakekeniya Da Azzalumai

Yana daga abin da yake nuna girman zalunci da munin karshensa cewa, Allah (S.W.T) ya hana taimakekeniya da azzalumai, da kuma karkata zuwa gare su. “Kuma kada ku karkata zuwa ga azzalumai sai wuta ta shafe ku. Kuma ba ku da wasu masoya koma bayan Allah, sannan ba za a taimake ku”. Hudu: 113. Wannan shi ne ladabin Kur’ani da Ahlul Baiti (AS). Hakika hadisai da dama sun zo daga garesu wadanda suka kai matuka wajan hana karkata zuwa ga azzalumai, da alaka da su, da yin aiki tare da su a cikin kowane irin aiki, da taimaka musu ko da tsagin dibino ne.
Babu shakka mafi girman abin da aka jarrabci musulmi da musulunci da shi, shi ne sassauci ga azzalumai, da kawar da kai game da miyagun ayyukansa, da mu’amala tare da su, ballantana taimaka musu a kan zaluncinsu. Ba abin da ya jawo wa al’ummar musulmi bala’o’i sai karkacewa daga tafarki madaidaci da gaskiya, har Addini ya yi rauni tare da shudewar zamani, karfinsu ya tafi, ya kai halin da yake a yau ya koma bako. Musulmi ko kuma wadanda suke kiran kansu musulmi suka zamanto ba su da wani mataimaki ban da Allah, kuma su ba za a taimake su ba hatta a kan mafi raunin makiyansu, da mafi kaskancin masu tsaurin ido a kansu kamar Yahudawa kaskantattu, balle kuma Kiristoci masu karfi.
Imamai (AS) sun wahala wajen nesantar da duk wanda ke da alaka da su daga taimakekeniya da azzalumai, suka kuma tsananta wa mabiyansu game da tafiya tare da ma’abota zalunci da cudanya da su, kuma hadisansu a game da wannan babin ba zasu kirgu ba, daga ciki akwai abin da Imam Zainul Abidin (AS) ya rubuta zuwa ga Muhammad Bn Muslim Azzuhuri, bayan ya gargade shi game da taimakon azzalumai a kan zaluncinsu da fadinsa: “Shin a kiran su gareka yayin da suka kira ka ba su sanya ka kan dutsin nika da suke juya nikan zaluncinsu da kai ba, kuma gada da suke ketarawa ta kanka zuwa bala’o’insu ba, da tsani na bi zuwa ga batansu, mai kira zuwa ga zaluncinsu, mai shiga tafarkinsu, suna sanya shakku da kai a zukatan malamai, kuma suna jan zukatan jahilai da kai zuwa gare su, waziransu na musamman da mafiya karfin mataimakansu ba su kai inda ka kai ba wajen gyara barnarsu, da kaikawon kebatattun mutane da saura jama’a zuwa garesu, abin da suka ba ka ya yi matukar karanta a maimakon abin da suka karba daga gareka da ya yi matukar girmama! Abin da suka gina maka ya yi matukar kankanta a maimakon abin da suka rusa maka da ya girmama! Ka duba kanka domin ba mai duban ta sai kai, ka yi mata hisabi irin na mutum abin tambaya”(46).
Wannan kalma ta “Ka yi mata hisabi irin na mutum abin tambaya”. ta girmama! Yayin da son rai ya yi rinjaye a kan mutum sai ya wulakanta sirrin samuwarsa da karamarsa, kuma ba zai samu wani mai daukar nauyin aikinsa ba, ya wulakanta abin da yake yi na ayyuka, ya raya cewa ba shi ne zai yi wa kansa hisabi a kan abin da yake yi ba na zunubi, wannan kuwa yana daga sirrorin ran mutum mai umarni da mummuna, sai Imam (A.S) ya so ya fadakar da Zuhuri game da wannan sirrin na rai da yake boye a cikinta, domin kada wahami ya yi galaba a kansa, sai ya yi sakaci da nauyin da yake kansa.
Mafi isa matuka daga wannan a suranta haramcin taimakekeniya da azzalumai shi ne maganar Safwan Jammal tare da Imam Musa Kazim (AS), wanda ya kasance daga cikin shi’ar Imam din, kuma daga masu rawaito hadisinsa amintattu (kamar yaddda ya zo a littafin Rijal na Alkashi game da Safwan) ya ce: “Na shiga wajansa.
Sai ya ce da ni: Ya Safwan duk wani abu daga gareka kyakkyawa ne mai kyau in banda abu daya.
Na ce: A sanya ni fansa gare ka! Wane abu ne?
Ya ce: Ba da hayar rakumanka ga wannan mutumin wato Harunar Rashid.
Na ce: Wallahi ni ban ba shi haya ba ina mai ashararanci, ko dagawa, ko don farauta, ko wasa ba, sai dai na ba shi haya ne don wannan tafarkin wato hanyar Makka, kuma ba na aikin da kaina, sai dai ina tura shi da bayina.
Ya ce: Ya Safwan kudin hayarka yana zama bashi a kansu?
Na ce: Na’am, a sanya ni fansa gareka.
Ya ce: Shin kana so su wanzu har su biya ka kudin hayarka?
Na ce: Na’am.
Ya ce: To duk wanda ya so wanzuwarsu yana cikinsu, duk wanda ya kasance daga cikinsu shi mai shiga wuta ne.
Safwan ya ce: Sai na tafi na sayar da rakumana baki daya.
Idan son rayuwar azzalumai da wanzuwarsu ya kai wannan matsayi, to ina ga wanda suke hada kai da shi a kan zalunci ko kuma yake karfafa su a zalunci, ina ga wanda ya shiga cikin jama’arsu ko yake aiki irin nasu, ko yake bin tawagarsu ko kuma yake bin umarninsu?.

40. lmaninmu Game Da Aiki A Hukuma Azzaluma

Idan har taimakar azzalumai koda da rabin dabino ne, kai hatta ma son wanzuwarsu suna daga mafi tsananin abubuwa da lmamai (AS) suka yi gargadi game da su, to menene hukuncin tarayya da su a cikin hukunci da shiga cikin ayyukansu da rikon ofisoshinsu. Menene kuma hukuncin wadanda suke daga wadanda suka assasa daularsu, ko kuma ya zama cikin rukunan shugabacinsu masu dulmuya cikin karfafa hukumarsu, (domin karbar shugabancin azzalumi rusa gaskiya ne dukkaninta, da raya barna dukkaninta, da bayyana zalunci da fasadi) kamar yadda ya zo a Hadisi a “Tuhaful Uku1” daga Imam Sadik (AS).
Sai dai kuma halaccin aiki a karkashin azzalumi ya zo daga gare su (AS) idan a ciki akwai kiyaye adalci, da tsayar da haddin Allah da kyautatawa ga muminai, da yin umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna. Ya zo a ruwaya cewa “Allah yana da wadanda ya haskaka hujjoji da su, ya ba su iko a kasashe a kofofin azzalumai, da su ne yake kare waliyyanSa, ya kuma gyara al’amuran musulmi da su, wadannan su ne muminai na hakika, su ne manarorin Allah a bayan kasa, su hasken Allah ne a cikin bayinsa”. Kamar yadda ya zo a Hadisi daga Imam Musa Bin Ja’afar (AS). A wannan Babin akwai hadisai da dama da suke bayyana tafarkin da ya kamata masu rike ofis da ma’aikata su gudanar da ayyukansu a kai, kamar abin da ya zo a wasikar Imam Sadik (AS) zuwa ga Najjashi Shugaban Ahwaz(47).

41. Imaninmu Game Da Kira Zuwa Ga Hadin Kai A Musulunci

An san Ahlul Baiti (AS) da kwadayinsu a kan wanzuwar addinin musulunci, da kira zuwa ga daukakarsa da hada kan mabiyansa, da kiyaye ‘yan’uwantaka a tsakaninsu, da cire mugun kuduri daga zukatansu, da kullace-kullace daga rayukansu, ba za a mance da matakin Amirul Muminin Aliyyu dan Abi Dalib (AS) game da halifofin da suka gabace shi ba, duk da fushin da ya yi da su da kuma yakininsa da kwacewarsu ga hakkinsa, amma sai ya tafi tare da su, ya zauna lafiya da su, kai an boye ra’ayinsa na cewa shi ne wanda aka yi wasiyya da halifancinsa, har ya zama bai bayyana nassin ba a bainar jama’a har sai da al’amarin ya koma hannunsa, sannan ya kafa hujja da sauran wadanda suka rage daga cikin Sahabbai game da al’amarin nassin Al-Ghadir a ranar Rahba da ta shahara. Ya kasance ba ya boye shawara garesu game da abin da ya shafi musulmi ko musulunci na amfani da maslaha, saudayawa yana fada game da wannan al’amari: “Sai na ji tsoron idan ban taimaki musulunci da ma’abotansa ba zan ga gibi a cikinsa ko rushewa”.
Kamar yadda babu wani abu da ya taba zowa daga gareshi wanda zai yi tasiri a karfafa mulkinsu, ko raunana jagorancnsu, ko rage kwarjininsu, sai ya kuntata wa kansa, ya zauna a gida duk da abin da yake gani daga gare su. Dukkan wannan saboda kiyaye maslahar musulunci ta gaba daya, da kiyaye kada a ga wani gibi a musulunci ko rushewa, har aka san haka daga gare shi, kuma halifa Umar dan Haddabi ya kasance yana fada yana kuma maimaitawa: “Kada na kasance cikin wani al’amari mai wuyar sha’ani da Abul Hasan ba ya ciki.” Ko fadinsa: “Ba don Ali (A.S) ba da Umar ya halaka”.
Haka nan ba za a mance da matakin Imam Hasan dan Ali (AS) ba dangane da yin Sulhu da Mu’awiya, bayan ya ga cewa dagewa a kan yaki zai shafe ya kuma kawar da Alkawari mafi girma –Kur’ani- da adalci har ma da musulunci daga samuwa har zuwa karshen zamani, a kuma shafe shari’ar Ubangiji, a kuma gama da wadanda suka yi saura daga Zuriyar Manzo daga Ahlul Baiti, sai ya fifita kiyaye zahirin musulunci da sunan Addini, duk da ya yi sulhu da Mu’awiya babban makiyin Addini da ma’abotansa, mai husuma mai mugun kuduri ga imam Hasan (A.S) da shi’arsa, tare da abin da ake tsammani na faruwar zalunci da kaskanci gareshi shi da mabiyansa, ga kuma takubban Banu Hashim da na shi’arsa a zazzare ba sa son komawa ba tare da sun yi aikinsu na kariya da gwabzawa ba, sai dai maslahar musulunci madaukakiya ita ce ta fi dukkan wadannan al’amuran.
Amma Shahidi Imam Husain (AS) idan ya motsa to domin ya ga cewa idan aka ci gaba da halin da ake ciki, Banu Umayya ba su sami wanda zai tona asirinsu ba, to da sannu zasu shafe sunan Musulunci, su kawar da darajarsa, sai ya so ya tabbatar wa tarihi ketare iyakarsu, ya fallasa abin da suke kulla wa Shari’ar Manzon Allah (S.A.W). Ba don yunkurinsa mai albarka ba, da Musulunci ya zama wani labari ne da tarihi zai rika ambatonsa tamkar wani addinin barna. Kwadayin Shi’a a kan raya ambatonsa ta hanyoyi daban- daban ya zamanto saboda kammala sakon da yunkurinsa na dauki-ba-dadi da zalunci ne, kuma domin raya al’amarinsa na cika umarni da biyayya ga Imamai (A.S)(48).
A nan kwadayin Ahlul Baiti (A.S) na wanzuwar izzar musulunci zata bayyana garemu koda kuwa mai mulki ya kasance mafi tsananin makiyansu ne a matakin Imam Zainul Abidin (A.S) da sarakunan Banu umayya alhalin sun maraita shi, an keta alfarmarsa a lokacinsu, kuma yana mai yawan bakin cikin a kan abin da suka yi wa babansa da Ahlin gidansa a waki’ar karbala, amma duk da haka yana yi wa rundunar musulmi addu’a da nasara, musulunci kuma da izza, musulmi kuma da yalwa da aminci, kuma ya riga ya gabata cewa makaminsa kawai wajen yada ilimi Shi ne addu’a, ya koya wa Shi’a yadda zasu yi addu’a ga sojojin Musulunci da musulmi, kamar addu’arsa da aka sani da “Addu’ar masu dakon iyaka” wacce yake cewa a cikinta: Ya Allah! ka yi tsira ga Muhammad da Zuriyar Muhammad, ka yawaitasu, ka kaifafa makamansu, ka kare matattararsu, ka kange iyakarsu, ka hada taronsu, ka shirya al’amarinsu, ka kadaita da wadatar da bukatunsu, ka karfafa su da cin nasara, ka taimake su da hakuri”. Zuwa inda yake cewa: “Ya Allah ka karfafa guraren Musulunci da haka, ka kiyaye gidajensu da shi, ka yawaita dukiyarsu da shi, ka shagaltar da su gabarin yakarsu don su dukufa ga ibadarka, da hana kai musu farmaki don su kadaita da kai, har ya zamanto ba a bauta wa kowa a bayan kasa sai kai, kuma ba a sanya wa goshi kasa saboda wani sai kai.” Haka nan ya ci gaba da addu’arsa mai fasaha, -kuma tana daga mafi tsawon addu’o’insa- wajen fuskantar da sojojin musulmi zuwa ga abin da ya kamace su na daga kyawawan dabi’u, da kuma shirya kansu, da tanadi a kan makiya, ta kunshi dukkan darussan yaki na jihadin Musulunci da bayanin manufarsa da fa’idarsa, kamar kuma yadda take fadakar da musulmi da irin gargadi da takatsantsan dangane da makiyansu, da abin da ya wajaba su yi riko da shi a mu’amalarsu da kariyar kansu, da kuma abin da ya wajaba a kansu game da yankewa daga komai zuwa ga Allah baki daya, da nisantar abubuwan da ya haramta, da yin abu saboda girman zatinsa.
Haka nan sauran imamai (A.S) a matakansu da suka dauka game da sarakunan lokutansu, duk da sun sami takurawa daga garesu iri-iri, da kuma azabtar da su da dukkan nau’i na kekasar zuciya da tsanantawa, domin su yayin da suka san cewa hukumar adalci ba za ta dawo hannunsu ba, sai suka juya zuwa ga koya wa mutane al’amuran Addininsu, suna fuskantar da mabiyansu fuskantarwa ta addini madaukaki. Dukkan wani yunkuri da ya faru a zamaninsu daga bangaren Alawiyyawa da wasunsu, bai kasance da ishararsu da son su ba, ya ma saba wa umarninsu da karfafawarsu ne a fili, duk da cewa sun fi kowa kwadayin kafa hukumar musulunci hatta sun fi Abbasawa son haka su kansu.
Ya isa garemu mu karanta wasiyyar Imam Musa Alkazim (AS) ga shi’arsa: “Kada ku kaskantar da kawukanku da barin biyyyar shugabanku, idan ya kasance mai adalci to ku roki Allah wanzuwarsa, idan kuwa ya kasance azzalumi to ku roki Allah gyaransa, domin gyaruwarku na cikin gyaruwar shugabanku, kuma shugaba adali yana matsayin uba mai rahama ne, ku so masa abin da kuke so wa kanku, kuma ku ki masa abin da kuke ki wa kanku”(49).
Wannan ita ce matukar abin da ake siffantawa na kiyayewar al’umma ga amincin shugaba da su so masa abin da suke so wa kansu, su ki masa abin da suke ki wa kansu.
Bayan duk wannan muna cewa: Alhakin shi’a da wasu marubuta na wannan zamani suke dauka ya girmama! Yayin da suke siffanta shi’a da cewa ita kungiya ce ta asiri mai barna, ko kuma wata jama’a ce ta ‘yan juyin juya hali. Haka nan cewa wajibi ne a kan mabiyin koyarwar Ahlul Baiti (A.S) ya ki zalunci, da azzalumai, da fasikai, ya yi duba zuwa ga mataimakansu duba na kyama, da rashin yarda, da wulakanci, wannan dabi’a ba ta gushe ba suna gadonta jikoki da ‘ya’ya, amma sam ba ya daga dabi’arsu su yi yaudara ko cin amana, kuma ba tafarkinsu ba ne yin juyin juya hali, ko su yi tawaye a kan jagorancin da yake an kafa shi da sunan musulunci, ko a boye ko a sarari.
Kuma ba sa halattawa kansu kisan gilla ko afka wa musulmi ko wace irin Mazhaba ko Darika yake bi, wannan kuwa domin rikonsu ne da koyarwar Ahlul Baiti (A.S), kuma duk musulmin da ya yi kalmar shahada biyu a wajansu, dukiyarsa da jininsa kubutattu ne, kuma cin mutuncinsa haramun ne; “Dukiyar mutum musulmi ba ta halatta sai da son ransa”. Musulmi dan’uwan musulmi ne, kuma yana da hakkoki a kansa kamar yadda bahasi mai zuwa zai yi bayani”.

42. Imaninmu Game Da Hakkin Musulmi A Kan Musulmi

Daga cikin mafi girma da kyawun abin da Musulunci ya yi kira zuwa gareshi shi ne ‘Yan’uwantaka tsakanin musulmi a kan duk sassabawarsu da martabobinsu da mukamansu. Kamar yadda mafi munin abin da musulmi suka yi a yau da kuma kafin yau shi ne, sakacinsu wajan riko da wannan ‘yan’uwantaka ta musulunci.
Domin mafi karancin koyarwar wannan ‘yanuwatakar ita ce “Ya so wa dan’uwansa musulmi abin da yake so wa kansa, kuma ya ki masa abin da yake ki wa kansa, kamar yadda zai zo a hadisin Imam Sadik (A.S).
Ka duba ka yi tunani a kan wannan dabi’a mai sauki a mahangar Ahlul Baiti (A.S), zaka samu cewa yana daga mafi wahalar abin da zaka iya samu wajan musulmi, da musulmi zasu yi wa kansu adalci su san addininsu sani na hakika, su yi riko da wannan dabi’a ta so wa dayansu dan’uwansa abin da yake so wa kansa, da ba a ga zalunci daga wani ba ko ketare iyaka, ko sata, ko karya, ko yi da wani, ko annamimanci, ko zargi da mummuna, ko suka da karya, ko wulakanci, ko girman kai.
Idan da musulmi sun tsaya sun fahimci mafi karancin ma’anar hakkin ‘yan’uwantaka a tsakaninsu kuma suka yi aiki da ita, da zalunci da ketare iyaka sun kau daga bayan kasa, kuma da ka ga ‘yan Adam sun zama ‘yan’uwa suna masu haduwa da juna cikin farin ciki, kuma da mafi daukakar sa’adar zamantakewa ta cika garesu, kuma da mafarkin malaman falsafa na da na samar da mafificiyar hukuma ya tabbata, da sun kasance masu musayar soyayya a tsakaninsu, da ba su bukaci wasu hukumomi da kotuna ba, ko ‘yan sanda, ko kurkuku, ko dokokin laifuffuka, da dokokin haddi da kisasi, kuma da ba su rusuna wa ‘yan mulkin mallaka ba, kuma da dagutai ba su bautar da su ba, kuma da kasa ta canja ta zama aljannar ni’ima kuma gidan sa’ada.
Bugu da karin cewa, da dokokin soyayya sun jagoranci rayuwar ‘yan Adam kamar yadda Addini yake so na koyarwar ‘yan’uwantaka, to da kalmar neman adalci ta bace daga harsunanmu da ma’anar cewa, ba zamu zamanto muna bukatar adalci da dokokinsa ba ballantana har mu bukaci amfani da kalmarsa, saboda dokokin soyayya sun isar mana wajen yada alheri, da aminci, da sa’ada, da murna, domin mutum ba zai bukaci amfani da adalci ko dokoki ba, sai idan ya rasa soyayya daga wanda ya wajaba ya yi masa adalci, amma a wajan wanda yake nuna masa kauna da soyayya, kamar da, da dan’uwa, sai dai ya kyautata musu ya hakura da dama daga abubuwan da yake so, duk wannan sakamakon so da kauna ne daga yardar zuciya, ba don adalci ko masalahar kansa ba.
Sirrin haka kuwa shi ne cewa mutum ba ya so sai kansa da kuma abin da ya dace da kansa, kuma mustahili ne ya so wani abu ko wani mutum da yake wajen ransa, sai dai idan yana da alaka da shi, kuma ya shiga ransa. Kamar kuma yadda yake mustahili ne ya sadaukar da zabin kansa gareshi a cikin abin da yake so yake kuma kauna saboda wani mutum da ba ya sonsa, ba ya kuma kaunarsa, sai dai idan yana da wani imani mai karfi da ya fi karfin son ransa, kamar imani da kyawun adalci da kyautatawa, a yayin nan yana iya sadaukar da dayan abubuwan da yake so, ya yi fansa da shi saboda son wani.
Farkon madaukakan darajoji da suka wajaba musulmi ya siffantu da su, su ne, ya kasance yana jin hakkin ‘yan’uwantaka ga sauran mutane, idan kuwa ya kasa wannan, to zai gaza aikata mafi yawa da haka saboda galabar son ransa, saboda haka yana wajaba a kansa ya cusa wa kansa akidar son adalci, da kyautata biyayya ga shiryarwar musulunci, idan kuwa ya gaza hakan to bai cancanci ya zama musulmi ba sai dai a suna, kuma ya fita daga soyayyar Allah (S.W.T), kuma Allah ba ya da wani buri a kansa kamar yadda zai zo a hadisin imam (A.S) mai zuwa. Saudayawa sha’awar mutum takan yi galaba a kansa, sai ya zamanto mafi wahalar abin da yake fama da shi, shi ne, ransa ta yarda da akidar adalci, balle kuma ya samu imani cikakke da ya fi karfin sha’awarsa.
Saboda haka ne ma kiyaye hakkin ‘yan’uwantaka ya zama daga mafi wahalar koyarwar addini idan babu imani na gaskiya game da ‘yan’uwantaka. Don haka ne imam Abu Abdullah (A.S) ya ji tsoron yi wa sahabinsa “Almu’ula Bn Khunais” bayanin dalla-dallan tambayarsa game da hakkin ‘yan’uwantaka sama da abin da ya kamata ya bayyana masa, domin tsoron kada ya koyi abin da ba zai iya aiki da shi ba.
Sai Mu’ula ya ce(50): Menene hakkin musulmi a kan musulmi?
Sai Abu Abdullahi ya ce: yana da hakkoki bakwai wajibai, babu wani hakki daga cikinsu sai ya wajaba a kansa, idan ya tozarta daya daga ciki to ya fita daga soyayyar Allah da biyayyarsa, kuma Allah ba shi da wani buri a gareshi.
Sai na ce masa: A sanya ni fansa gareka! Mecece?
Sai ya ce: Ya Mu’ula ni ina mai tausasa wa gareka, ina tsoron ka tozarta ba zaka kiyaye ba, ko kuma ka sani ba zaka aikata ba.
Na ce: Babu karfi sai da Allah.
Yayin nan sai Imam (A.S) ya ambaci hakkoki bakwai, bayan ya fada game da na farkonsu cewa: “Mafi saukin hakki daga cikinsu shi ne ka so wa dan’uwanka kamar yadda kake so wa kanka, ka kuma ki masa abin da kake ki wa kanka”.
SubhanalLahi! Wannan shi ne hakki mai kankanta, to yaya wannan hakkin mafi kankanta yake a gare mu yau mu musulmi? Kaicon fuskokin da suke da’awar musulunci amma ba sa aiki da mafi kankantar abin da ya wajaba na daga hakkokinsa. Abu mafi ban mamaki kuma shi ne, a dangata wannan rashin ci gaban da ya samu musulmi ga musulunci, alhalin laifi ba na kowa ba ne sai na wadanda suke kiran kansu musulmi amma ba sa yin aiki da mafi karancin abin da ya wajabta musu da su yi aiki da shi na koyarwar addininsu.
Domin tarihi kawai, kuma don mu san kawukanmu da takaitawarta zamu ambaci wadannan hakkoki bakwai wadanda Imam (A.S) ya bayyana su:
l- Ka so wa dan’uwanka musulmi abin da kake so wa kanka, kuma ka ki masa abin da kake ki wa kanka.
2- Ka nisanci fushinsa, ka bi yardarsa, ka kuma bi umarninsa.
3- Ka taimake shi da kanka, da dukiyarka, da harshenka, da hannunka, da kafarka.
4- Ka zamanto idonsa, dan jagoransa, kuma madubinsa.
5- Kada ka koshi, shi kuma yana cikin yunwace, kada ka kashe kishirwarka shi kuma yana jin kishirwa, kada ka zama a suturce shi yana tsirara.
6- In kana da mai hidima shi kuma dan’uwanka ba shi da mai hidima, to wajibi ne ka tura mai hidimarka, sai ya wanke masa kaya, ya dafa masa abinci, ya gyara masa shimfida.
7- Ka kubutar da rantsuwarsa, ka amsa kiransa, ka gaishe da maras lafiyarsa, kuma ka halarci jana’izarsa. Idan kuma ka san yana da wata bukata sai ka yi gaggawar biya masa ita, kada ka bari har sai ya tambaye ka, sai dai ka gaggauta masa.
Sannan ya rufe maganarsa da cewa: “Idan ka aikata haka to ka hada soyayyarka da soyayyarsa, kuma soyayyarsa da soyayyarka”.
Akwai hadisai da yawa da suka kunshi ma’anar da ta zo a wannan hadisi daga imamanmu (A.S), wasunsu daga littafin Wasa’il a babobi daban-daban.
Tayiwu wasu su yi tsammanin cewa abin nufi da ‘yanuwantaka a hadisin Ahlul Baiti (A.S) ya kebanci tsakanin musulmi ne wadanda suke daga mabiyansu a kebance, amma komawa ga ruwayoyinsu yana kawar da wannan zato, koda yake sun kasance ta wani bangare suna tsananta musantawa ga wanda ya sabawa tafarkinsu kuma ba ya riko da shiriyarsu. Ya wadatar ka karanta hadisin Mu’awiya Dan Wahab ya ce(51):
Na ce masa(52): Yaya ya kamata gare mu mu yi tsakaninmu da mutanenmu, da kuma wadanda muke cudanya da su na daga mutane wadanda ba sa kan al’amarinmu”.
Sai Ya ce: “Ku duba Imamanku wadanda kuke koyi da su ku yi yadda suke yi, na rantse da Allah! su suna gaishe da maras lafiyarsu, suna halartar jana’izarsu, suna ba da shaida garesu da kuma a kansu, kuma suna bayar da amana garesu”.
Amma ‘yan’uwantakar da Imamai suke son ta daga mabiyansu, tana saman wannan ‘yan’uwantaka ta musulunci, kuma kai ka riga ka ji wasu hadisai a fasalin bayanin sanin shi’a da ya gabata. Kuma ya isar ka karanta wannan muhawara tsakanin Abana Bn Taglib da Imam Sadik (A.S) daga hadisin(53) da Abana ya rawaito da kansa yana mai cewa: Na kasance ina dawafi tare da Abi Abdullahi (A.S) sai wani mutumi daga cikin mutanenmu ya bujuro mini wanda ya riga ya tambaye ni in raka shi wata biyan bukatarsa, sai ya yi mini ishara, sai Abu Abdullahi (A.S) ya gan mu.
Sai ya ce: Ya Abana kai wannan yake nema?
Na ce: Na’am.
Ya ce: Shin yana kan abin da kake kai?
Na ce: Na’am.
Ya ce: Maza ka tafi zuwa gare shi ka yanke dawafin.
Na ce: Koda ya kasance dawafin wajibi?
Ya ce: Na’am.
Abana ya ce: Sai na tafi, bayan nan -wani lokaci- sai na shiga wajansa (A.S) na tambaye shi game da hakkin mumini. Sai ya ce: Bari kada ka kawo wannan! Ban gushe ba ina sake tambaya har sai da ya ce: Ya Abana ka raba masa rabin dukiyarka, sannan sai ya kalle ni ya ga abin da ya shige ni, sai ya ce: Ya Abana ashe ba ka san Allah ya riga ya ambaci masu fifita wasu a kan kansu ba?
Na ce: Haka ne!
Ya ce: “Idan ka ba shi rabin dukiyarka ba ka fifita shi ba, kana fifita shi ne kawai idan ka ba shi daya rabin!
Na ce(54): Hakika a yanayinmu mai ban kunya bai dace ba mu kira kanmu muminai na hakika. Mu muna wani waje ne, koyarwar Imamanmu (A.S) tana wani wajen. Kuma abin da ya Shigi zuciyar Abana zai Shigi zuciyar duk mai karanta wannan hadisin, sai dai ya juya fuskarsa kawai yana mai mantar da kansa shi kamar wani ake wa magana ba shi ba, kuma ba ya yi wa kansa hisabi irin na mutumin da yake abin tambaya.

Fasali Na Biyar

43. Imaninmu Game Da Tashin Kabari Da Tashin Kiyama

Mun yi imani da cewa Ubangiji zai tayar da mutane bayan mutuwarsu a wata sabuwar halitta a ranar da aka yi wa bayi alkawarinta, sai ya saka wa masu biyayya ya azabtar da masu sabo, wannan al’amari ne da baki dayansa da abin da ya tattara na daga sauki, abu ne wanda dukkan shari’o’in da aka saukar daga sama da masana Falsafa suka yi ittifaki a kai, kuma babu wata madogara ga musulmi sai dai ya yi imani da akidar Kur’ani mai girma wacce Annabinmu mai girma ya zo da ita, domin duk wanda ya yi imani da Allah imani yankakke, ya kuma yi imani da Muhammad manzo ne daga gare shi, wanda ya aiko shi da shiriya da addinin gaskiya, to babu makawa ya yi imani da abin da Kur’ani ya ba da labarinsa game da tashin kiyama, da sakamako da azaba, da aljanna da ni’ima, da wuta da kuna, kuma Kur’ani ya bayyana haka a sarari, kuma ya yi nuni da shi a cikin abin da ya kai kusan ayoyi dubu.
Idan har shakku ya samu wani game da wannan, ba don komai ba ne sai domin yana shakku game da ma’abocin sakon, ko kuma game da samuwar mahaliccin halittu da kudurarsa, ba komai ba ne sai shakkun da yake bujuro masa game da asalin addinai dukkaninsu, da kuma ingancin shari’o’i gaba dayansu.

44. Imaninmu Game Da Tayar Da Jikkuna

Tayar da jikkuna wani al’amari ne da yake larura daga laruran Addinin Musulunci, Kur’ani mai girma ya yi ishara game da shi: “Shin mutum yana tsammanin ba zamu tattara kasusuwansa ba ne. A’aha, Lalle mu masu iko a kan mu daidaita yatsunsa ne”. Surau Alkiyama: 3. Da fadinsa: “Idan kayi al’ajabi to abin al’ajabi ce maganarsu cewa ashe idan muka mutu muka zama turbaya za a dawo da mu halitta sabuwa”. Ra’ad: 5. Da fadinsa: “Shin mun gajiya ne da halittar farko, sai dai su suna cikin rudewa ne game da sabuwar halitta”. Surar Kaf: 14.
Tayar da jikkuna ba wani abu ba ne sai dawo da mutum ranar tashin kiyama da jikinsa bayan rididdigewa, da sake dawo da shi zuwa ga kamarsa ta farko bayan ya zama rididdigagge. Ba wajibi ba ne a yi imani da dalla-dallan tayar da jikkuna fiye da abin da Kur’ani ya ambata, ko sama da abin da ya fada na daga; Hisabi, da Siradi, da Auna ayyuka, da Aljana, da Wuta, da Sakamako, da Ukuba, daidai gwargwadon abin da bayaninsa ya zo a cikin Kur’ani mai girma.
“Bai wajaba ba sanin hakikar da babu mai iya kai wa gareta sai ma’abocin zurfin ilimi, kamar ilimin cewa shin jikkuna zasu dawo ne da kan kansu ko wasu makamantansu ne? Kuma shin rayuka zasu rasu ne kamar jikkuna ko kuwa zasu ci gaba da kasancewa har sai sun sadu da jikkuna yayin tashin kiyama? Kuma cewa shin Tashin kiyama ya kebanci mutum ne ko ya hada har da dukkan dabbobi ne? Kuma shin tashin a lokaci daya ne ko a sannu-sannu ne? Kuma idan yin imani da Aljanna da Wuta wajibi ne, amma bai zama dole a san cewa samammu ne a halin yanzu ba, ko kuma sanin cewa a sama suke ko a kasa, ko kuma sun saba. Haka nan idan sanin ma’auni ya zama wajibi, amma bai wajiba ba a san cewa ma’aunin na ma’ana ne ko kuwa yana gurin gwada nauyi ne biyu. Kuma ba dole ba ne a san cewa siradi jiki ne siriri, ko kuwa daidaituwa a kan tafarki madaidaici ne. Hadafin wannan bayani shi ne, a musulunci ba a shardanta bincike domin sanin cewa wadannan abubuwa suna da jiki ne ko kuwa(55).
Wannan akidar ta tashin kiyamar da saukin nan nata ita ce wacce musulunci ya zo da ita, idan mutum ya so ya wuce haka domin saninta dalla-dalla sama da abin da Kur’ani ya zo da ita domin ya gamsar da kansa, don kore shakkun da masu bincike da masu kokwanto ke tayarwa ta hanyar dalilan hankali, ko bahasin dalili na zahiri, to yana wahalar da kansa ne, kuma zai fada a cikin mushkiloli da jayayya maras iyaka. A Addini, babu adinda yake tilasta wannan zurfafawar dalla-dalla da littattafan masana Akida da malaman falsafa suke cike da shi, kuma babu wata larurar Addini, ko ta zamantakewa, ko siyasa, da take tilasta irin wadannan rubuce-rubucen da makalolin da aka makale littattafai da su, haka nan babu wata fa’ida, wadannan abubuwan sun karar da karfi da kokari da lokuta da tunanin masu jayaya ba tare da fa’ida ba.
Gamsuwarmu game da gazawar mutum game da riskar wadannan al’amuran da suke boyayyu a gare mu, kuma wadanda suke sama da fahintarmu da samuwarmu, wadanda suka dara matsayinmu, sun wadatar wajen raddin wadannan shubuhohi da shakkun da ake tayarwa game da wadancan bayanai. Tare da sanin cewa, Allah (S.W.T) mai iko ne a kan ya ba mu labarin hakikanin aukuwar Tashin kiyama da tashi daga kabari. Ilimin dan Adam da gwaje-gwajensa, da bincike-bincikensa, mustahili ne su iya samo wani abu da bai san shi ba, wanda ba ya kuma karkashin gwajinsa da bincikensa, da ba zai iya saninsa ba sai bayan mutuwarsa da ciratarsa daga wannan duniya zuwa wata duniyar daban, idan haka ne, yaya za a saurari ya yi hukunci da tabbatarwa ko kore wannan abu, balle ya shiga bayanansa dalla-dalla da abubuwan da suka kebanta da shi, sai dai idan ya dogara a kan bokanci, da zato, da mamaki, kamar yadda yake a dabi’ar dan Adam ya yi mamakin dukkan abin da bai saba da shi ba, kuma iliminsa da riskarsa ba su san shi ba, kamar mai fada da jahilcinsa yana mai mamakin tashi daga kabari da tashin kiyama: “Wanene zai rayar da kasusuwa alhali suna rididdigaggu”.
Ba komai ne ya sa shi mamakin ba sai rashin sabawa da ganin matacce rididdigagge an mayar masa da sabuwar rayuwa, sai dai mai wannan mamakin ya manta da yanda aka halicce shi tun farko alhalin da can ya kasance rasasshe, gabobinsa da yankunan jikinsa riddidigaggu an hada su ne daga kasa da abubuwan da ta kunsa, da kuma sarari da abin ya tattaro, har ya zama mutum madaidaici mai hankali: “Shin mutum ba ya gani ne mu mun halitta shi daga digon maniyyi sai ga shi yana mai husuma bayyananne. Kuma ya buga mana misali ya mance halittarsa, ya ce: Wanene zai rayar da kasusuwa alhalin suna rididdigaggu”. Yasin: 77-78.
Ana gaya wa mai irin wannan maganar da ya mance kansa: “Ka ce; wannan da ya fare su tun karon farko shi ne zai rayar da su, kuma shi masani ne da dukkan halittu”.
Yasin: 79. Kuma a ce masa: Bayan ka san mahaliccin halittu da kudurarsa, kuma ka san Manzo da abin da ya ba da labari game da shi, da gajiyawar iliminka hatta a gano sirrin halittarka da sirrin samuwarka, da yadda ka girma da kuma yadda ka fita daga marhalar digon mani da ba ya jin komai, ba ya hankalta zuwa marhalolin da ke biye da aka harhada daga kwayoyin halitta manesanta, domin ka zamanto mutum madaidaici, mai hankali, mai tunani, mai riska da mariskai. Kuma a ce da shi: Yaya kake mamakin dawo maka da rayuwa sabuwa bayan ka zama rididdigagge, kana kokarin tsinkayar sanin abin da kwarewarka ka da iliminka ba zasu iya gano shi ba?
A kuma ce masa: Ba ka da wata mafita sai mika wuya kana mai ikrari da wannan hakika, wacce mai juya al’amuran halittu, masani, mai kudura, wanda ya samar da kai daga rashi. Kuma dukkan wani kokari na binciko abin da ba zai yiwu a gano shi ba, kuma iliminka ba zai kai gare shi ba, to kokari ne maras amfani, da rudani cikn dimuwa, da bude ido a cikin duhu mai dundum.
Duk da irin inda dan Adam ya kai gare shi na ilimi a wannan zamani, ya kago lantarki, da rada(56), da amfani da makamin kare dangi, da sauran kage-kagen da, da an yi magana game da su a shekarun baya da an kirga su a cikin mustahilan abubuwa ababan yi wa isgili, amma duk da haka mutum ya kasa gano hakikanin wutar lantarki, da sirrin kwayar zarra, ya kasa gano hatta hakikanin daya daga cikin siffofinta, to yaya zai ji kwadayin gano sirrin halitta da samuwa, sannan ya kara gaba yana son ya san sirrin Tashin kiyama da Tashi daga kabari.
Haka ne, ya kamata ga mutum bayan ya yi imani da musulunci ya nisanci bin son zuciya, kuma ya shagaltu da abin da zai gyara masa lahirarsa da duniyarsa, da kuma abin da zai daukaka masa matsayinsa a gurin Allah, kuma ya yi tunani a kan abin da zai taimake shi a kansa, da kuma abin da zai fuskanta bayan mutuwa na daga tsananin kabari da hisabi bayan halarta a gaban Mai mulki, Mai yawan sani. “Kuma ku ji tsoron ranar da wata rai ba ta wadatar wa wata rai komai kuma ba a karbar ceto daga gareta, kuma ba a karbar fansa daga gareta, kuma ba a taimakon su”. Bakara: 48.

Bayanin Karshe

Da mun so buga littafin da muka fassara na Shahid Sadar mai taken “Dan sako da Sako da Mai sako” wanda yake bincike game da hanyoyin tabbatar da samuwar Allah ta hanyar Mandik istikra’i(57), amma sai muka ga amfaninsa ga mutane duk da yana da yawa amma kadan ne zasu amfana daga gareshi, domin kuwa duk da ya kasance an fassara shi da harshen Hausa ne amma akwai kalmomi da yawa da sai wanda ya san ilimin Mandik ko Falsafa zai fahimta. Kuma ga wahalar mayar da isdilahohin (58) ilimin daga Larabci zuwa Hausa, al’amarin da in Allah ya yarda a nan gaba zai zama malamai sun fara shi, musamman da yake mafi yawancin kalmomin ilimomi daban-daban ba a yi wani kokarin samar da su a Hausa ba, wanda irin wannan ya taso ne daga sakaci da halin ko-in-kula na Farfesa wane da Dakta wane da Alhaji wane, sa’annan kowanne ya zauna babu kokarin ganin ci gabantar da al’ummar gaba ta fuskacin tunani da ilimi ba, hada da cewa shi Alhaji wane ba zai iya kashe wa Farfesa wane da Dakta wane kudi domin su kawo canjin ilimi cikin al’umma ba. (Da haka ne sai al’umma ta zauna da karancin sanin ilimomin wasu nahiyoyi cikin harshenta kuma ga shi su irin wadanda muka ambata a sama ba sa nuna kishinta ko ma ba su da shi, sai ya zama kowa yana kishin kansa ne yana kuma jin komai nasa, nasa ne shi kadai, da haka sai aka rasa ci gaban al’umma, komai a kullum sai ja da baya yake yi, ta haka ne zaka ga, ga shi Alhaji wane yana ganin nan ba wajan ciniki ba ne da zai ci riba alhalin ribar lahira ba a kwatanta ta da ta duniya, ballantana ma irin wadannan kampanoni masu buge-buge sukan samu riba mai yawa wani lokaci har da wani dan tallafi daga hukumominsu. Amma ba mu manta da cewa a sauran kasashe kafin su irin wadannan mutane su fara Gwamnatocinsu ne suke fara kawo canjin ilimi cikin yaren al’umma ba, amma ba mu san menene ya sanya a Afrika musamman a kasashenmu abin ya yi muni matuka ba fiye da sauran kasashen duniya, wannan yana bukatar su masu mulkin kasar a kalla in ba zasu ji tsoron Allah da hisabin lahira ba to su zama masu kishin al’ummarsu mana).
Tunanin wahalar fahimtar Littafin “Dan sako da Sako da Mai sako” ga masu karatu shi ne ya sanya muka yi tunanin canza littafin da wanda yake da sauki game da Ilimin kalam (Akida) mai suna Akidojin imamiyya na Malam Rida Muzaffar, amma bayan mun fara ba mu yi nisa ba sai aka yi mana ishara da cewa an riga an fassara shi, amma bayan nazari kadan da neman shawarwarin wasu daga abokai suka yi nuni da cewa idan dai zai fi sauki a kan wanda aka fassara to yana da kyau, hada da wasu abubuwa da suka hada da hakkin mallaka, da wasu gyare-gyare, sai muka dauki wannan shawarar domin neman lada wajan Ubangiji da kuma fatan ya zama ya fi sauki ga mai nazari, musamman da ya zama abin nufi shi ne amfanar da al’umma da ilimin sanin Allah (S.W.T) da siffofinsa da ayyukansa ta hanyar kalmomi masu sauki da zasu yi saukin fahimta. Da fatan Allah ya sanya shi mai amfani ga al’umma gaba daya. Wannan shi ne Littafin: Akidojin Shi'a Imamiyya, Wallafar Asshaikh Rida Al-Muzaffar, Fassarar, Hafiz Muhammad Sa’id Kano Nigeria.
Godiya Ta Tabbata Ga Allah Ubangijin Talikai


1. Biharul Anwar: 53, shafi 126.
2. Wato abubuwan da suke wajibi ne kowane mutum ya san su.
3. Shi ne nazarin dalilan shari'a domin samun masaniya game da rassan hukunce-hukuncen shari'ar da shugaban Manzanni (S.A.W.) Ya zo da ita kuma ba ta canzawa ko sakewa da sakewa zamani da kuma halaye.
4. Ihtiyadi shi ne bin fatawar malamai da aiki da mafi nutsuwar zance daga cikin fatawowinsu.
5. Wato idan wasu suka yi sun dauke wa sauran mutane.
6. Abin da yake bai damfara ko dogara da wuri ba.
7. Abin da yake ya damfara ko ya dogara da wuri.
8. Karfici a nan ba irin wanda yake fitar da mutum daga musulunci ba ne kamar yadda yake sananne cewa kafirci matakai-matakai ne.
9. Siffofin Idafa su ne siffofin da suke nuna alaka tsakanin bangare biyu, wato bangaren Allah da kuma na bayinsa, kamar arzutawa da halittawa.
10. Shi ne wanda samuwarsa daga waninsa take wato shi abin halitta ne.
11. Wannan ra’ayi ne na daya daga malaman mu’utazila da mabiyansa, abin da yake nufi shi ne, siffofin tabbatar da kamala ga Allah suna komawa ga kore tawaya ne, kamar idan aka ce mai iko ne to awajansu abin da ake nufi shi ne ba gajiyye ba ne, amma wai ba a iya cewa ma’anar ta mai iko ne, domin gudun kada a kamanta shi da bayinsa. A lokacin da wannan ra’ayi ya kai su ga tauye Allah (S.W.T) domin idan aka ce mai ilimi yana nufin ba jahili ba amma kuma ba ya nufin ma’anar mai ilimi, wannan a gun mu mazhabar imamiyya isna ashariyya tauye Allah ne da kore masa kamala, Allah ya tsare mu daga kaucewar tunani.
12. Wannan ra’ayi ne na Ash’ariyya da suke ganin siffofin ma’ani ba kawai ma’ana ba ne da Allah shi ne hakikanisnsu na zahiri kamar yadda sauran siffofinsa suke, suna ganin wadannan siffofi suna da tabbatattun hakikaninsu a zahiri na hakika da suke siffantuwa da su, misali kamar Ali da yake da sunaye ne da siffofi, da za a ce masa Ali dan Muhammad, baban Isa, dogo ne, kuma kakkaura, sai a ce siffofinsa dan Muhammad, baban Isa, da dogo, da kakkaura, duk a zahiri suna da daidaikun da suke siffantuwa da su, sai ya zama Ali shi yana nuni izuwa gareshi ne kawai banda sauran siffofi, sauran siffofi kuwa suna da nasu samammu na zahiri da suke siffantuwa da su. Da maganar Ash’ariyya gaskiya ne da a nan Allah ya zama guda takwas, kamar yadda a misalinmu Ali zai zama su biyar, wato Ali, da dan Muhammad, da baban Isa, da dogo, da kuma kakkaura.
13. Wato siffofn kari guda bakwai da masu wannan nazari suka ce su ba Allah ba ne amma sun dadu ga zatin Allah kuma zatin yana bukatarsu a ra’ayin Ash’ariyya kamar yadda ya gabata a bayaninmu, da kuma Siffofin khabariyya; kamar hannun Allah, da idonsa, da fuskarsa, da suke da tawili da ma’anar da laraba suka sani alokacin saukra da littafin kur’ani mai girma, Sifffofin khabariyya siffofi ne wadanda ake tawilinsu kamar tawilin hannu da karfi ko iko ko alkawarin Allah, kamar yadda ya zo da kinayoyi da kalmomin aro a kur'ani mai girma.
14. Alhalin Allah yana ko'ina bai kebanta da wani wuri ba.
15. A sani masu wannan ra’ayi suna magana ne a matakin yiwuwa a hankalce saboda musunsu ga rawar da hankali zai iya takawa a wannan fage, amma a aikce ba su siffanta shi da wannan miyagun siffofi ba sai da lazimin maganarsu, wato sakamakon abin da suke fada suka kuma tafi a kai zai kai ga siffanta Allah da miyagun siffofin tawaya irin wadannan a hankalce.
16. Su ne mutanen da suka tafi a kan cewa ayyukan bayi a bisa hakika ayyukan Allah ne ba tare da wani tawili ba a kan haka, don haka Allah (S.W.T) shi ne yake aikata ayyukan bayi kai tsaye.
17. Mujabbira, da Ash’ariyya suna da wannan ra’ayi da aka san shi da jabar na musun wasida tsakanin Allah da ayyukan da ya halitta ba. Sun musa abin da ya sanya shi tsakaninsa da bayinsa da falalarsa. Misali kamar ‘ya’yan mangwaro da suke zuwa daga itace, sai suka ce kai tsaye Allah ne ya halitta su ba tare da wata rawa da shuka a matsayinta na wasida ta taka ba, wannan shi ne kwatankwacin ayyukan bayinsa a wajansu, don haka kai tsaye ayyukansu ayyukansa ne.
18. Mu’utazilawa sun saba da Mujabbira da Ash’ariyya, su sun tafi akan Tafwidi da ma’anarsa take nufin cewa; babu hannun Allah a cikin ayyukan bayi ko kadan, wannan ra’ayi da shi da na farkon duka a gun mazhabar imamiyya kuskure ne.
19. “Da rai da abin da ya daidaita ta kuma ya cusa mata fajircinta da kuma takawarta”. Surar Shamsi: 7-8.
20. Dabi’a al’amura ne kamar ki, so, fushi, yarda, da sauran halayen rai da zuciya.
21. “Manzanni masu bushara kuma masu gargadi domin kada mutane su zama suna da wata hujja a kan Allah bayan manzanni kuma Allah mabuwayi ne Mai hikima”. Surar Nisa’i: 165.
22. “Kuma sai muka yi wahayi ga Musa kan cewa jefa sandarka sai ga shi tana hadiddiye abubuwan da suke kirkira. Kuma gaskiya ta tabbata abin da suke aikatawa kuma ya baci, Sai aka rinjaye su a nan sa’annan suka juya suna kaskantattu, Kuma aka kifar da masu sihirin suna masu sujada”. Surar A’araf; 117-120.
23. “Kuma Manzo zuwa ga Bani Isra’ila cewa lalle ni na zo muku da aya daga Ubangijinku ni ina halitta muku daga laka abin da yake kamar surar tsuntsu kuma in hura a cikinsa sai ya zamanto tsuntsu da izinin Allah kuma ina warkar da makaho da mai cutar albaras kuma ina rayar da matattu da izinin Allah, kuma ina ba ku labarin abin da kuke ci da wanda kuke taskacewa a gidajenku lalle a cikin wannan akwai aya gare ku idan kun kasance muminai”. Surar AI- Imran: 49.
24. Duba fadin Allah madaukaki: “Kuma idan da mutane da aljannu zasu taru a kan su zo da kwatankwacin wannan kur’anin to da ba zasu zo da makamancinsa ba koda kuwa sashensu na taimakon sashe”. Surar Isra’i: 88.
“Ko suna cewa shi ne ya kage shi ne ka ce to ku zo da surori goma makamantansa kagaggu kuma ku kira duk wanda zaku iya wanda ba Allah ba in kun kasance masu gaskiya”. Surar Hud: 13 kalubalantar su kan su kawo sura guda kamarsa: “Kuma idan har kun kasance a cikin kokwanto daga abin da muka saukar to ku zo da sura daya kamarsa kuma ku kira shaidunku da ba Allah ba in kun kasance masu gaskiya”. Surar Bakara: 23. Allah Ta’ala Yana cewa: “Ko suna cewa ya kage shi ne ka ce ku zo da sura guda kamarsa kuma ku kira duk wanda za ku iya koma bayan Allah in kun kasance masu gaskiya”. Surar Yunus: 38.
25. Isma shi ne rashin aikata sabo a kowane hali da zamani a rayuwar mai ita, shin a lokacin yarinta ne ko girma ko tsufa, kafin aike da daukar nauyi ko a lokacin hakan.
26. Fadinsa madakaki: “Kuma lalle mun rubuta a littafi bayan ambato cewa duniya bayina salihai ne zasu gaje ta, lalle a cikin wannan akwai isarwa ga mutane masu ibada”. Surar Anbiya’i: 105-106. Hadisai kuwa sun zo da silsila daban-daban har zuwa kan Manzo (S.A.W.) da kuma Imamai (A.S) cewa: Mahadi (A.S) daga ‘ya’yan Fadima (A.S) zai bayyana a karshen zamani domin ya cika duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci.
27. Amirul muminin Aliyyu Dan Abi Dalib (A.S) ya siffanta shi a daya daga cikin hudubobinsa yana cewa: “Ya zabe shi bishiyar Annabawa da fitila mai haske da kuma mai tsororuwar daukaka da mafi darajar gurare, da fitilun haskaka duffai kuma shi ne mabubbugar hikima”. Daga cikin wannan hudubar har ila yau Amirul Muminin (A.S) yana cewa: “Likita mai zazzagawa da maganinsa ya shirya kayan aikinsa yana amfani da su duk lokacin da bukata ta kama wajen warkar da makantattun zukata, da kuraman kunnuwa, da bebayen bakuna, yana bibiyar guraren gafala da maganinsa da kuma guraren rudewa. Ba su yi amfani da hasken hikima ba, ba su kunna kyastu makoyar ilimi ba, su sun zamanto kamar dabbobi masu kiwo a duwatsu masu tsauri.” (Nahajul Balagha Huduba: 108).
28. Ubangiji madaukai yana cewa: “Mu Mu ne Muka saukar da ambato kuma lallai Mu masu karewa ne gare shi”. Surar Hijri: 9.
29. Duba fadinsa madaukaki: “Kuma yayin da Isa dan Maryam ya ce: Ya Bani Isra’la lalle ni Manzon Allah ne gare ku, mai gaskata abin da yake gaba gare ni na Attaura kuma mai bayar da bushara game da wani Manzo da zai zo bayana sunansa Ahmad. Sai dai a yayin da ya zo musu da hujjoji bayyanannu sai suka ce wannan sihiri ne bayyananne”. Surar Saff: 6.
30. Fadinsa madaukaki: “Idan ma ba ku taimake shi ba to ai Allah ya riga ya taimake shi yayin da wadanda suka kafirta suka fitar da shi yana na biyun su biyu yayin da suke cikin kogo yayin da yake cewa ma’abocinsa kada ka damu hakika Allah yana tare da mu, sai Allah ya saukar da nutsuwarsa gareshi ya kuma taimake shi da rundunoni da ba ku gan su ba, kuma ya sanya kalmar wadanda suka kafirta makaskanciya kalmar Allah kuma ita ce madaukakiya kuma lalle Allah Mabuwayi ne Mai hikima”. Surar Tauba: 40.
31. Kamar yadda yake a fadar Ubangiji “Ka ce: Ya Ubangiji Ka kara mini ilimi”. Surar Daha: 114.
32. Masu ruwaya a tafarkin Sunna da Shi’a sun hadu a kansa.
33. Masu fadin cewa imamai ubangizai ne ko kuma su ba ma mutane ba ne.
34. Masu imani da shigar Ruhin Ubangiji madaukaki jikin imamai.
35. Koma wa Littafin Sakifa na mawallafin wannan littafin domin karin bayani da sharhi ga wasu ayoyin kur’ani.
36. Tanasuhi shi ne ciratar wata rai daga wani jiki zuwa wani jikin daban da ba na farko ba.
37. Babul Ikbal aladdu’a daga kitabuddu’a na littafin Usulul Kafi daga Imam Sadik (A.S).
38. Daga maganar Imam Rida (A.S), duba littafin Kamiluz ziyarata da Ibn Kulawaih Sh: 122.
39. Tuhaful Ukul: sh, 24.
40. Kamiluz ziyarati: shafi: 131.
41. Usulul Kafi, Kitabul iman, Babu ziyaratul ikhwan.
42. Usulul Kafi, Kitabul iman, Babul wara’i.
43. Usulul Kafi, Kitabul iman, Babut ta’a wat takawa.
44. Usulul Kafi, Kitabul iman, Babu Hakkil mu’umini ala akhih.
45. Usulul Kafi, Kitabul iman, Babul wara’i.
46. Tuhaful Ukul: sh, 66.
47. Al- Wasa’il Kitabul Bai’i Babi na 78.
48. Sun kasance suna cewa Allah ya yi rahama ga wanda ya raya al’amarinmu.
49. Alwasa’il, Kitabul amri bil ma’arufi wan nahayi anil munkari: Babi 17.
50. Alwasa’il, Kitabul hajji, Abwabu ahkamul ushura, Babi 122, hadisi 7.
51. Usulul Kafi, Kitabul ushura, Babi na farko.
52. Wato yana nufin Imam Assadik (A.S).
53. Alwasa’il kitabul hajji, Abwabul ushura: babi 122, hadisi 16.
54. In ji fawallafin littafin.
55. Kitabu Kashiful gita’i, shafi 5.
56. Na’urar hangen abubuwa daga nesa.
57. Hanyar kididdiga da fitar da sakamako bisa asasin daidaikun bincike.
58. Kalmomin da suka kebanta da wata ma’ana ta musamman a wani ilimi sabanin ma’anarta ta lugga.