Kyawawan halaye


::.

Kyawawan Halaye Da Ladubban Musulunci

::.

Jiga-Jigan Kyawawan Halaye

::.

Kyawwan Halaye Da Rukunansa Guda Hudu

::.

Rukunoni Biyu Na Ladubban Musulunci

::.

Siffofin Al'umma A Tsarin Musulunci

::.

Musulunci Da Kyawwan Halaye 'Yan Tagwaye Ne

::.

Abubuwan Da Aka Wajabta

::.

Abubuwan Da Aka Haramta

::.

Wasu Abubuwan Da Aka Haramta Din

::.

Munanan Halaye Da Kuma Abin Kinsu

::.

Dabi'u Mafifita Da Kyawawan Halaye
::. Tuba Da Komawa Zuwa Ga Allah
::. Sallar Dare Da Falalarta
::. Daga Ladubban Haihuwa

Kyawawan Halaye Da Ladubban Musulunci

Musulunci ya karafafi dabi'u na gari kuma ba wa ladubbansa muhimmanci mai girma har sai da manzon rahama (S.A.W) ya yi nuni da cewa; an sanya hadafin aiko shi domin cika kyawawan halaye ne, yana mai cewa: "An aiko ni ne kawai domin in cika kyawawan halaye ne"(1).
Yayin da Allah ya yi nufin ya yi yabo ga masoyinsa (S.A.W) ya yabe shi da kyawawan halaye ne yana mai cewa: "lallai kai ma'abocin halaye ne madaukaka"(2).
Yayin da ya yi nufin ya tunatar da al'umma rahamar da ya ba su ya yi nuni da taushin hali ne yana mai cewa: "saboda rahama daga Allah ne ka tausayawa musu"(3).
Da akwai ruwayoyi masu yawa da suka zo suna nuna muhimmanci kyawawan halaye da ladubban musulunci har Kur'ani mai girma ya kasance idan ya ambaci wasu ukubobi yakan raba su da ambaton afuwa da yafewa wanda suke bangare ne na kyawawan halaye, kuma ya ambaci afuwa da cewa tafi kusa da takawa.

Jiga-Jigan Kyawawan Halaye

Musulunci ya sanya takawa a matsayin ma'aunin kyawawan halaye da ladubba a cikin addini, kuma kyawawan halaye suna da rukunai guda hudu, ladubba kuwa suna da guda biyu, kuma musulunci ya kwadaitar da musulmai a kansu kuma ya umarce su da siffantuwa da su.

Kyawwan Halaye Da Rukunansa Guda Hudu

Amma rukunai hudu na kyawawan halaye su ne kamar haka;
1-Tsarkin zuciya da kuma gaskiyar niyya, Ubangiji yana cewa a game da muhimmacin tsarkin zuciya da kuma salamarta da gaskiyar niyya da tsarkakarta: "Ranar da dukiya ko 'yaya ba zasu amfanar ba, sai dai wanda ya zo wa Allah da zuciya kubutacciya"(4). Wato; wacce ta kubuta daga shirka da kafirci da kuma miyagun halaye.
2-Sakin fuska da walwalarta, a hadisi ya zo cewa: "Mumini farin cikinsa yana kan fuskarsa bakin cikinsa kuwa yana cikin zuciyarsa" da kuma fadinsa: "mumini mai annashuwa ne mai murmushin fuska". da kuma fadinsa: "sakin fuska yana kawo soyayya kuma yan shigarwa aljanna" da kuma fadin: "turbune fuska yana nisantarwa daga Allah kuma yana shigarwa wuta".
3-Dadin magana da kyawun zance, Ubangiji yana cewa: "ku fadi kyakkyawa ga mutane"(5). Imam Ali (A.S) yance cewa: 'Ni ina ki muku ku kasance masu zage-zage"(6).
4-Kyakkyawar mu'amala da zama tare da mutane, Ubangiji madaukaki yana cewa: "Ka riki afuwa dayi umarni da kyakkyawa, ka kawar da kai daga jahilai"(7), kuma yana fadi cewa: "Idan jahilai suka yi musu (mummunar) magana sai su fadi (kyakkyawar magana ta) aminci"(8).

Rukunoni Biyu Na Ladubban Musulunci

1-Ladubban daidaikun mutane, wadannan sun shafi rayuwar mutum a kansa, kamar ladubban ci da sha, da bacci, da farkawa, da sanya tufafi, da mazauni, da tafiya, da zaman gida, dalafiya, da rasin lafiya, dasauransu na daga abubuwan da musulunci ya zo da su kuma lizimtarsu yana kusanatar da mutum zuwa ga dukkan wani alheri da lafiya kuma yana nisantar da shi daga dukkan sharri da abin ki kuma ya sanya hsimaisa'ada abin yabo.
2-Ladubban zamantakewa da ya shafi dukkan al'umma; wannan tana da alaka da rayuwar mutum ta al'umma kamar ladubban zama da iyaye da iyali da 'ya'ya da muksanta da dangi, da makwabta da abokai da dalibai da malami da dukkan mutne, kai har ma da ssauran halittu, kuma musulunci ya zo da mafi kyawun koyarwa da ladubba wacce zata kawo aminci da zaman lafiya da tsaro da nutsuwa da kuma kaunar juna da son juna da hadin gwiwa tsakanin dukkan mutane da dukkan al'umma.

Siffofin Al'umma A Tsarin Musulunci

Al'umma a tsarin musulunci ita ce: al'umma da ta lizimci kyawwan halaye na 'yan'adamtaka wacce ya zo da ita, kuma ya bambanta da sauran tsarin zamantakewa da:
1-Shi tsari ne wanda ya saba da wanda muke gani gaba daya a yau a tsakanin ja'amar musulmi, domin bayan imani da Allah da ranar lahira kuma yana da tsarin kyawawan halaye, don haka ne ma yake da tsarin da wani tsari a duniya bai isa ya kawo irinsa ba.
Don haka ne tsarin musulunci yake daukar mutum a matsayin samamme madaukaki yayin da sauran tsarurruka suke daukar mutum a matsayin kaya da za a yi amfani da shi domin cimma buri.
2-Rayuwa tana samn cigaba a dukkan janibobinta a tsarin musulunci na adalci, sai ta raya gidaje da hanyoyi da shuke-shuke, kuma da cigaban sana'o'I da yalwar cinikayya da kuma habakar dukiya, da kuma wadatar mutane a yanayin da babu zalunci ko cutarwa ko takurawa ko tsanantawa ko ta'addanci ko wasu dabaibayi ko dauri ko kurkuku ko gidan azabtarwa ko matsaloli ko talauci a cikinsa.
Shi ya sanya soyayya da kaunar juna da yarda da raya kasa, suka mamaye al'umma a lokacin da aiwatar da musulunci da cigaban da ba a samu irinsa a duniya ba a yau duk da yawan kayan aikil.
3-Kowane mutum daga jama'ar musulmi shi mai isar da sakon musulunci ne da koyarwarsa da zancensa da aikinsa kuma shi mai kiyaye kowane mutum ne na al'umma, kuma shi abin tambaya ne ga kowane mutum, don haka sai ya yi umarni da kyakkyawa ya yi hani ga mummuna, ya yi kira zuwa ga musulunci da hukumar musulunci ta duniya, da hikima da wa'azi da kuma tattaunawa ta hanya mai kyau.

Musulunci Da Kyawwan Halaye 'Yan Tagwaye Ne

Hakikar addinin musulunci shi ne kyawawan halye na dan Adam, kuma su 'yan tagwaye ne da ba a raba su, domin babu wani abu sai da musulunci ya sanya kyawawan halaye a cikinsa, kuma dukkan dokokin musulunci da ya kafu a kansa dukkansu sun doru kan kyawawan halaye ne madaukaka. Domin mu san hakan mauan iya nuni da wasu daga wajibai da hani na haram da kuma abin da aka ki shi na munanan halaye domin mu ga yadda dukkansu suka yi dacewa da rayuwar mutum ta badini da ta zahiri da kuma daga hannunsa da kama shi zuwa ga kyawawan halaye da laduban musulunci mafi daukaka.

Abubuwan Da Aka Wajabta

Ubangiji yana cewa: "Allah yana umarni da adalci da kyautatawa da kuma bai wa ga ma'abocin kusanci" . Sai ya lizimta wa mutum musulmi sanin wajibai da aiki da su kuma zamu kawo wasu daga ciki a nan:
1. Ba wa mace sadakinta ko ladanta
2. Ba wa mai shayarwa ladanta
3. Ba wa mai girbi hakkinsa
4. Ba wa ma'abocin kusanci hakkinsa
5. Bayar da zakka
6. Bayar da dukiyar maraya
7. Tsoro da takatsantsan ga abin da Allah ya hana
8. Rikon ado gun masallaci
9. Rikon abin da Manzo da Ahlul Baiti (A.S) suka zo da shi
10. Bayar da amana
11. Bayar da sheda
12. Bayar dahakkin Allah da na mutane
13. Niman izininshiga gidan mutane
14. Umarni da kyakkyawa
15. Aikata kyakkyawa
16. Imani da Allah da ranar lahira
17. Kaskantar da kai ga Allah
18. Barranta da makiya Allah da waliyyansa
19. Kin makiya Allah
20. Neman tsani zuwa ga Allah
21. Neman yardar Allah
22. Kin ma'abota bidi'a
23. Kwana gun matarsa
24. Biyayya ga Annabi da alayensa
25. Bin limami a salla
26. Kawar da fasadi
27. Tuba
28. Tabbatakan gaskiya
29. Tabbata a jihadi
30. Nisantar mummnan zato
31. Nisantar bauta ga wanin Allah
32. Nisantar karya da shedar zur da muzik
33. Karkata zuwa ga sulhu
34. Amsa wa Allah da manzonsa
35. Son Allah da waliyyansa
36. Hijabin mace ga namiji bare
37. Hajji
38. Zantawa da ni'imar Allah
39. Haramta abin da Allah da manzonsa suka haramta
40. Kyautata zato ga Allah
41. Renon 'ya'ya
42. Kiyaye farji
43. Kiyaye salla da ibadu da alkawura da amana
44. Hukunci da abin da Allah ya saukar
45. Neman yafewar wanda aka zalunta
46. Gaisuwa
47. Tsoron Allah da rusuna masa
48. Kaskan da kai ga muminai
49. Humusi
50. Tsoron Allah
51. Addu'a
52. Kira zuwa ga Allah
53. Kariay ga addini da rayuka
54. Kare mummuna
55. Ambaton Allah kowane hali
56. Tarbiyyar yara
57. Amsa sallama da rubutu
58. Shiryar da mutane zuwa ga gaskiya
59. Yarda da hukuncin Allah
60. Ziyarar Annabi da imamai
61. Mika wuya da tsarkake wa ga Allah
62. Rige zuwa ga gafarar Allah
63. Sauraron Kur'ani mai hikima
64. Tafiya a bayan kasa domin daukar darasi
65. Godiya ga Allah da iyaye
66. Hakuri
67. Abota da iyaye da kuma makusanta
68. Gaskiyar magana
69. Gyara tsakanin mutane
70. Azumin wata Ramadan
71. Rama abin da ya jawo lalacewarsa da batansa
72. Ciyarda mai jin yunwa
73. Neman arziki
74. Nieman ilimi
75. Biyayya ga Allah da manzonsa da majibinta lamurra
76. Bayyana gaskiya
77. Bayyana ki ga masu sabo
78. Bautar Allah
79. Daukar darasi daga darussan rayuwar wasu
80. Adalci
81. Zama da mata da kyakkyawa
82. Sanin ilimin wajibi na asasin addini da rassansa da kyawawan halaye da ladubba
83. Taimakekeniya
84. Runtse gani daga haram
85. Neman gafara
86. Kishi
87. Matsawa wasu a mazauni
88. Ilimin addini
89. Tunani a ni'imar Allah
90. Hukunci da gaskiya
91. Tsayar da addini da aiki da shi
92. Fadin kyakkyawa
93. Daidaita al'amura
94. Neman halal
95. Kasancewa tare da masu gaskiya
96. Nisantar wanda Allah ya la'anta
97. Hana kafirai shiga masallatai
98. Nadama kan zunubi
99. Nasiha ga mumini da taimaka masa
100. Ciyarwa a tafarkin Allah
101. Aure
102. Hana mummuna
103. Hanuwa daga abin da Allah da manzonsa suka hana
104. Komawa zuwa ga Allah
105. Niyyar gaskiya da kyakkyawa
106. Tahajjudi
107. Hijira saboda Allah
108. Rushe bata
109. Son ma'abota kusanci
110. Tsentseni a haram
111. Awo da ma'aunin adalci
112. Cika alkawari
113. Kare rai da iyali daga wutar lahira
114. Dogaro da Allah
115. Yakini da Allah da ranar lahira

Abubuwan Da Aka Haramta

Allah yana cewa: "ka ce ku zo in karanta muku abin da ubangijinku ya haramta muku" . Kamar yadda ya lizimci mutum musulmi ya nemi sanin wajibai haka nan ya lizimta masa neman sanin haram da kuma nisantar ta, kuma mu a nan zamu kawo galinbin abubuwan da aka haramta musamman wadanda a na iya cin karo da su kamar haka:
1. Taimakawa kan sabo
2. Taimakon azzalumi
3. Nutsuwa da fushin Allah
4. Musun mu'ujiza
5. Musun ranar sakamako da tashin jiki ko wani daga asasin addini ko na mazhaba
6. Musun larurin addini
7. Kawar da kai daga ambaton Allah
8. Izgili da muminai
9. Barna
10. Dagewa kan kananan sabo
11. Sanya zoben zinare ga namiji
12. Jawo mani: kamar da hannunsa ko da na wani, amma idan ta hannun matarsa ne to ba komai
13. Cutar da muminai
14. Kaucewa hukuncin shari'a
15. Amfani da kwanon zinare da azurfa koda don ado ne
16. Wulakanta musulmi
17. Yada sirrin wanda bai yarda a yada ba
18. Yada sirrin juna tsakanin miji da mata
19. Rashin biyayyar mace ga mijinta cikin abin da yake wajibi ne ta bi shi
20. Rashin biyyar 'ya'ya ga iyayensu
21. Wasa da kayan caca tare da sanya kudi
22. Bayyana sabo
23. Yada alfahasha
24. Ci a Ramadan ko ranar azumin wajibi ba tare da wani uzuri na shari'a ba
25. Boye kaya
26. Rashin nisantar bawali da najasosi
27. Rashin yarda da Allah a cikin kaddararsa
28. Umarini da mummuna
29. Cutar da makwabta
30. Karbar lada a kan wajibi ayyananne a dunkule
31. Karkata zuwa ga azzalumi
32. Jefa kai cikin halaka
33. Jingina yaro ga wanda ba babansa ba
34. Fitar mace ba tare da izinin mijinta ba
35. Sumbuntar namiji ko mace ga bare
36. Sumbuntar mutum waninsa don sha'awa sai dai miji da matarsa kawai ko baiwarsa
37. Bidi'a cikin addini
38. Mutum ya auri 'yarsa
39. Mummunan zato da gini kansa
40. Kage
41. Bayan gida tare da ba wa alkibla baya ko gaba
42. Girman kai ga barin bautar Allah
43. Adon namiji da zinare
44. Duban taurari
45. Girman kai
46. Barin salla wajiba
47. Barin kowane irin wajibi ne
48. Jinkirta hajji daga shekarar da ya samu iko
49. Karyata wani abu na Kur'ani ko hukuncin shari'a
50. Barna
51. Jinkirta salla har lokacin ta ya fita
52. Kai hukunci gun azzalumi ba larura
53. Halartar wajen shaye-shaye
54. Mace ta yi ado ga namiji bare
55. Hore mala'ika ko rohani ko aljani da sauransu
56. Sanya bacci na magadisu
57. Boye aibin kaya da algus
58. Jinkirta rama Ramadan har wani Ramadan din
59. Barin umarni da kyakkyawa da hani da mummuna
60. Barin ladabatar da yara da zai ga fasadi
61. Haramta halal
62. Halatta haram
63. Leken aibobin mutane
64. Tsoratar da mumini
65. Barin takiyya wajen da yake dole
66. Kamantuwa da kafirai a shiga da adon kai da sauransu
67. Ji wa wani ciwo ko dukansa ko zaginsa ko yanke masa wata gaba
68. Rashin amsa sallama
69. Hukunci ba da abin da Allah ya saukar ba
70. Tsare hakkin Allah
71. Tsare hakkokin mutane
72. Tsare wani babu wani hakki
73. Sanya tufafin alhariri ga namiji babu wani uzuri na shari'a
74. Hassada da kuma aiki da ita
75. Tozarta hakkin mutane
76. Kiyaye littattafan bata da jaridu ko mujallu na bata dasayar da su da sayansu da koyar da su da koyonsu da yada su
77. Cin dukiyar maraya
78. Shan abu mai sanya maye
79. Cin mushe
80. Cin naman alade
81. Cin naman dabbar da aka haramta
82. Cin naman dabbar da ba a ambaci sunan Allah ba wajen yanka ta ko ta rasa wani sharadi na yanka
83. Cin tabo ko sauran abubuwan daaka haramta
84. Ha'inci
85. Kayan kide-kide da muzik, kamar sayar da su da sayen su da kuma ajiye su daamfani da su
86. Yaudara
87. Neman auren mace mai miji ko kuma mai idda
88. Cin maniyyin tumaki
89. Cin sauran abubuwan da aka haramta a jikin dabba
90. Sayar da karen kwararo ko alade da sayansu
91. Yakar shugaba na shari'a adali
92. Cin najasa ko mai najasa da shansu
93. Karya ga Allah da manzonsa da imami
94. Buga ganga ko garaya da molo da ihu
95. Sata
96. Yada barna
97. Kashe gaskiya

Wasu Abubuwan Da Aka Haramta Din

1. Daudanci da hada zina tsakanin mutum biyu
2. Karya
3. Shiga kungiyoyin bata kamar na kominis
4. Shiga addinan bata kamar na sufancin ko na babiyya
5. Kiyayya da mumini
6. Son makiya addini
7. Zagi musamman ga Allah da Annabi da imami da addini da littafi da mazhaba da sauran abubuwa masu tsariki
8. Taba littafin Kur'ani babu tsarki
9. Mai baki biyu; ya yabi mutum idan ba ya nan kuma ya zage shi
10. Karbar rashawa da cin hanci domin boye gaskiya da bayyanar da karya
11. Karbar rashawa da bayr da ita cikin al'amuran hukunci sai da lalura
12. Karbar riba da bayr da ita da rubuta sheda a kanta da zama tsakatsaki a kai
13. Zama kasar da mutum ba zai iya kare addininsa ba ko gusar da alamomin musulunci
14. Zuwa kasar da zata cutar da addinin mutum
15. Fashi
16. Aske gemu ko tsige shi, da abin da yake mai kaifi
17. Aske gemun wani
18. Rawa
19. Shiga cikin cacar ful
20. Tafiya makarantun da zai kai ga fasadi
21. Tafiya bandaki da wurin wanka na iyo da makarantu da wuraren da ake cakuda maza da mata
22. Raddin ga Allah da manzonsa da imamai da marja'ai da suke kan tafarkinsu cikin hukuncin shari'a
23. Yarda da sabo
24. Jifan wani da zina
25. Annamimanci
26. Sauraron annamimanci
27. Zuwa sinima na barna
28. Kokarin rusa masallatai
29. Taimakon (ko dan aiken) azzalumai
30. Amfani da kayan kida da caca da kuros da sauransu
31. Waka da fadin karya a ciki
32. Toshe titi da hanyar musulmi
33. Aibata mumini da wulakanta shi da zarginsa
34. Karanta zunubi da zai kai ga jinkirta tuba
35. Fitar mata ba tsari da kuma cire hijabi
36. Shirka da Allah mai girma
37. Yada alfasha
38. Sabawa karya
39. Warware alkawri
40. Shedar zur
41. Sharadi da sanya kudi na tsere sai dai abin da aka fada a littafin fikihu a babin tsere da harbi
42. Rufa ido
43. Munafunci
44. Ba wa azzalumi da 'yan bidi'a uzuri da kuma kaunarsu
45. Tozarta wanda ake ciyarwa
46. Wasa da tattabaru da tsuntsaye da sauransu na daga abubuwan da sukan kai ga haram
47. Zalunci da ta'addanci
48. Zihari
49. Saba wa iyaye
50. Aikin tsafi da kuma abin da zai raba miji da mata ko kuma abin da yake sanya son wani ba tare da sonsa ba
51. Cin dukiyoyin mutane da barna
52. Jiji da kai a ibada
53. Algus
54. Waka da sauraronta
55. Canja wasiyya
56. Fushi da yakan kai ga haramun
57. Giba; rada, da sauraronta
58. Fasadi a bayan kasa
59. Fitina
60. Fasikanci da fajirci
61. Sayar da littafi madaukaki
62. Sayar da makami ga kafirin yaki
63. Kiyafa: donganta mutane da iyayensu ta hanyar kallon kafafunsu ko jikinsu da canke
64. Caca da kayan shadaranji koda kuwa babu kudi
65. Yanke salla wajiba
66. Rantsuwa bisa karya
67. Tone kabari
68. Yanke zumunci
69. Jingina 'ya'ya ga Allah
70. Bokanci
71. Fatawa ba da ilimi ba
72. Fada daga tafarkin Allah
73. Kisa ba da hakki ba
74. Auren mace da aka haramta da nasaba ko shayarwa ko surukuta
75. Aurar namiji da aka haramta aurarsa
76. Kin zuwa jihadi
77. Gudu daga filin daga
78. Kafirci
79. Kasuwanci da abin da aka haramta
80. Tauye mudu da awo
81. Boye sheda
82. Boye gaskiya
83. Wake da siffanta mace mai kamewa ko yaro
84. Zambon mumini a waka
85. Bode al'aura ga wanda ya haramta ya gani
86. Luwadi
87. Wasannin banza na holewa
88. Taba jikin ajnabi ko ajnabiyya
89. Taba mace ko namiji da sha'awa ba ta hanyar halal ba
90. Amfani da kayan maye kamar shad a saye dasayarwa da dasa su ko shuka su da aikinsu da cin kudinsu da kai wa wani da kuma hayar kanti ko abin hawa ko wani abu daban, da kuma sauran amfani kamar magani in ba da larura ba
91.Sabawa bakanci
92. Aikata abubuwan da aka haramta wa mai haramin aikin hajji
93. Zuwa wajen bokaye da 'yan bori da 'yan camfi da masu halarto da rahuhanya da aljanu da sauansu
94. Mata su shafi juna da sha'awa
95. Maza su shafi juna da sha'awa
96. Hana zakka ko humusi ko sauran hakkoki na wajibi
97. Jinkirta hakkoki
98. Hannu da ajnabiyya
99. jayayya da Allah da manzonsa da imami bisa shisshigi
100. Saba wa Allah da manzonsa da imamai
101. Keta umarnin Annabi
102. Shisshigi da wuce gona da iri musamman ga Allah
103. Leken gidajen makwabta
104. Zama a kan teburin da ake shan giya
105. Hana aikata kyakkyawa
106. Shiga ayyukan azzalumai
107. Keta alfarmar Ka'aba da wurare masu tsarki
108. Yanke kauna daga rahamar Allah
109. Ruku'u da sujada ga wanin Allah
110. Rantsuwa da barranta da Allah da manzonsa ko imami ko addinin Muhammad
111. Kai wa zuwa ga mulki ba ta hanyar shari'a ba
112. Azabtar da mutane don su fadi wani abu da ake bincike
Muna iya ganin wasu mun maimata su saboda muhimmancin su da kuma hani da aka yi game da hani mai tsanini ko azaba mai tsanani a kan yinsu.
Sannan kuma wasu da muka fada kafirci ne yinsu wasu kuma shirka ne, wasu kuma manyan zunubai ne, wasu kuma akwai kaffara a kansu wasu haddi kamar yadda aka yi bayani dalla-dalla a littattafai.

Munanan Halaye Da Kuma Abin Kinsu

Akwai munanan halaye dadabi'u da suke munana kuma ya kamata ga dukkan musulmi ya kaurace musu kuma suna da yawa malaman ilimin kyawawan halaye sun ambace su a littattafansu kuma mu a nan zamu kawo wasu daga ciki, duk da wasu ma an haramta su a shari'ance, wadanda suka hada da:
1. Daukar fansa
2. Alfahari
3. Cutarwa koda ba da haramun ba kamar ya gina gidansa ta yadda zai kare wa makwabcinsa rana ko iska
4. Wulakanci ko da bai kai haddin haramci ba
5. Wulakanta mutane
6. Tsoratar da mutane kodai bai kai haddin haramci ba
7. Yada abin da ake son boyewa
8. Karya a cikin raha
9. Izgili
10. Wuce iyaka kamar ya zauna tarabbu'I a waje mai tsukuku
11. Wulakanci cikin alheri
12. Kage cikin raha; kamar ya ce wane yana da ci
13. Magana da abin da babu ruwan mutum
14. Dogaro kan mutane
15. Aikin lagawu
16. Boye abubuwan da aka boye da ba su shafi mutum ba
17. Raki gun musifa
18. Jur'ar yin munana
19. Bakin ciki akan abin da ya kubuce na duniya
20. Rashin kula da al'amuran lahira
21. Son yabo da kurantawa
22. Son shugabanci da girma
23. Son dukiya
24. Son duniya
25. Hassada matukar ba ta kai haddin haramci ba
26. Kwadayi
27. Dora nauyi kan wani
28. Hikidi da mugun kuduri
29. Tsoron mutane
30. Kutsawa cikin mummunan halaye
31. Neman zabar rayuwar da ya so ta duniya, kamar kayyaduwa da nau'in tufafi dasauaransu
32. Saba alkawari
33. Riya koda a wanin ibada ne
34. Munana zato ga Allah
35. Munana zato ga mutane
36. Mummunar dabi'a
37. Mummunan wajen halarta
38. Kokarin aikta mummuna da ba haramun ba ne
39. Rashin yarda da rabo
40. Zama da kaskantun mutane
41. Kukan sha'anin rayuwa
42. Rowa
43. Shige gona da iri a rayuwar duniyanci
44. Shagube koda ba na haramun ba
45. Kaskanta mutane
46. Kaskantar da kai
47. Kaskantacciyar himma
48. Dukan kai
49. Kwadayi
50. Yawan bacci
51. Dogon buri
52. Rashin kishi
53. Kishi a inda bai dace ba
54. Gaggawa
55. Shisshigi daidai gwargwadon da bai kai haram ba
56. Kyautata zato ga kansa
57. Kabilanci da bangaranci
58. Rashin girmama babba
59. Rashin tausayawa karami
60. Rashin dogara da Allah
61. Fushi babu wani dalili na shari'a
62. Yawan wadata data kasance dalilin dagawa
63. Dimuwa
64. Gafala
65. Fankama da abin mutane
66. Mummunar magana koda ba haramun ba ce
67. Tayar da fitina
68. Kekasar zuciya
69. Raba kan mutane da rashin jituwa
70. Girman kai
71. Boye gaskiya koda kuwa boyeta bai kai wajibi ba, koda kuwa ta hanyar shiru ne
72. Ganin alherin kansa da yawa
73. Karanta alherin wani
74. Yawaita sharrin wani
75. Karanta sharrin kansa
76. Butulcewa ni'ima
77. Rashin godiya
78. Yawan raha
79. Rashin daidaituwa tsakanin zahiri da badini koda kuwa a kan al'amuran duniya ne
80. Rashin kunya
81. Nisantar muminai
82. Zaman banza
83. Yawan dariya
84. Waswasi a al'amuran duniya
85. Yawan shagaltuwa da rayuwa
86. Kazanta da rashin lizimtar tsafta
87. Rashin adalci
88. Shisshigi a al'amuran duniya
89. Sakaci a ciki
90. Zama da masu sabo
91. Yunkune da bata fuska
92. Rashin kulawa da mustahabbai
93. Lizimtarmakaruhai
94. Rashin kulawa da abin da ya ce da abin da aka ce game da shi
95. Rashin bayar da muhimmanci ga hukuncin shari'a

Dabi'u Mafifita Da Kyawawan Halaye

Akwai dabi'u mafifita abin yabo da musulunci ya yi maraba da su kuma ya yi umarni a siffantu da su, da ya kamata mutum musulmi ya siffantu da su kuma suna da yawa, amma zamu kawo abin da ya samu daga cikinsu:
1. Nutsuwa da alkawarin Allah
2. Yin sannu-sannu a al'amura
3. Kaskantar da kai gun Allah
4. Adalci da fadin gaskiya game da mutane
5. Wadatuwa daga mutane
6. Fifita wasu a kan mutum kansa
7. Ciyarwa a tafarkin Allah
8. Taimakon mutne
9. Saba wa kai aikin alheri
10. Umarni da kyakkawa
11. Hani ga mummuna
12. Gyara tsakanin mutane
13. Ikhlasi a ayyuka
14. Nutsuwa da Allah
15. Bin iyaye
16. Kaskan da kai
17. Ziyarta juna
18. Jituwa da juna
19. Tubadaga haram
20. Mika wuya ga umarnin Allah a komai
21. Dogaro ga Allah
22. Tabbata kan al'amura kyawawa
23. Hakuri
24. Kyawawan halaye
25. Kiyaye makwabta
26. Son Allah da kuma son wanda Allah ya yi umarni
27. So saboda Allah
28. Ki saboda Allah
29. Tsoron Allah
30. Kaunar Allah
31. Tsoron zunubai
32. Rashin dogaro da ayyuka
33. Cudanya da mu'amala da mutane
34. Magana da kawukanmu
35. Cudanya da iyalinmu da 'ya'yanmu
36. Yarda da rabon Allah
37. Zuhudu
38. Baiwa
39. Sitirta mutane
40. Gyara aibobin rai
41. Dadada magana
42. Godiya ga mai ni'ima
43. Gyara ga mutane da hikima da wa'azi
44. Sakin fuska
45. Yawaita sadaka da taimakon raunana
46. Sadar da zumunci
47. Yada sallama
48. Bin halaye da raunana da marasa lafiya suke ciki
49. Tsafta
50. Suturta aibobi
51. Daidaitawar zahiri da badini a komai
52. Gaskiya da nisantar kayra koda a raha
53. Hakuri
54. Karbar bakuntar mumini
55. Ansa mu a bakunci
56. Aika wad a kyauta wuraren da suke na alheri haka nan ma karbarta
57. Rangwame ga mutane
58. Kamewa
59. Adalci a komai
60. Girmama ma'abota addini
61. Nisantar kaskantattun dabi'u
62. Kishi
63. Son talakawa
64. Mujahada da rai
65. Bayar da rance
66. Biyan bukatun muminai
67. Kame cutar da su
68. Kiyaye sirri da rashin yada shi
69. Ambaton mutane da alheri
70. Gaggauta alheri
71. Yi wa kai hisabi
72. Nasiha gamuminai da shawara
73. Niyyar alheri
74. Tsarkake kai da kuma kawar da munanan halaye daga gareta
75. Takawa
76. Tsentseni
77. Nisantar shubuha
78. Juriya kan barin sabo
79. Juriya kan bin Allah
80. Ambaton mutuwa
81. Wadatar zuci
82. Kunya
83. Sakin fuska

Tuba Da Komawa Zuwa Ga Allah

Daga Annabi (S.A.W) ya ce: babu wata rana da alfijir dinta yake bullowa ko shafakin darenta ya buya, sai mala'iku biyu sun amsa da sautuka hudu daya yana cewa: ina mai dai ba a halicci wadannan halittu ba.
Sai dayan ya ce: ina ma dai da aka halicce su sun san me ya sa aka halicce su.
Sai daya ya ce: ina ma dai yayin da suka san me ya sa aka halicce su sun yi aiki da abin da suka sani.
Sai dayan ya ce: ina ma dai yayin da ba su yi aiki da abin da suka sani ba sun tuba daga abin da suka yi.
Daga imam Ali (A.S) yayin da wani mutum ya ce: Ina neman gafarar Allah! sai ya ce: kaiconka! Shin ka san menen istigfari kuwa? Ka sani neman gafara daraja ce ta madaukaka kuma yana wakana da abu shida:
Na farko nadama kan abin da ya wuce
Na biyu niyyar rashin komawa har abada
Na uku ka bayar da hakkokin mutane har sai ka koma zuwa ga Allah babu komai na mutne a kanka
Na hudu ka je ka yi dukkan wata farilla da ka tozarta hakkinta
Na biyar ka sami naman jikinka da ya ginu da haram sai ka kawar da shi da bakin ciki har sai fata ta hadu da kashi kuma sannan sai wani nama sabo ya tofo
Na shida ka narkar da jiki da zafin biyayya kamar yadda ya ginu da dadin sabo. Sannan sai ka ce: Astagfirullah(11)! (ina neman gafarar Allah).
Wani hadisi ya zo cewa wanda ya yi nufin aikata mummuna bai aikta ta ba, to tayiwu bawa ya yi mummuna sai Ubangiji ya gan shi ya ce: na rantse da grimana da daukaka ta ba zan gafarta maka ba bayan wannan har abada"(12).
Daga Ja'afar Sadik (A.S) ya ce: "ku ji tsorn kananan zunubai ku sani ba a gafarta ta. Sai na ce: menene muhakkirat? Sai ya ce: mutumin da yake zunubi sai ya ce: ina farin ciki ba ni da wani lafin sai wannan(13).
Daga imam Ali (A.S) ya ce: "mafi tsananin zunubai azaba shi ne wanda mai yinsa ya raina shi"(14).
Daga imam Ja'afar Sadik (A.S) ya ce: "A'aha wallahi! Allah ba ya karbar komai na biyayya tare da cigaba da wani abu na saba masa"(15).

Sallar Dare Da Falalarta

Hakika an karfafa sosai a game da sallolin dare a ruwayoyi masu yawa daga imamai (A.S) a kan cewa ita raka'a goma sha daya ce: takwas sallolin dare, da kuma raka'o'in shafa'i da na wutiri. Kuma lokacinta daga rabin dare har zuwa bullowar alfiji. Kuma kowace raka'a biyu tana da sallama daban, sai da wutiri shi raka'a daya ne, kuma an so karanta "kul huwallah ahad" sau talatin a kowacce daya daga raka'o'in biyu na farko, amma a sauran raka'o'i sai a karanta surori masu tsawo kamar an'am da kahafi da anbiya, wannan duk idan akwai isasseh lokaci.
An so karanta mafi tsawo a raka'ar farko sannan sai mafi gajerta a ta biyu, haka nan an so karanta falaki da nasi da tauhid a shafa'i da wuturi, ko tauhid (kulhuwallahu) a dukkansu.
Kuma ya yi addu'a a kunutun wutiri ga mumini arba'in yana cewa: Allah ka gafarta wa wane, ya ambaci sunansa, kuma amma kada a kirga yaro cikin mutane arba'in, kuma a yi alkunuti da istigfari saba'in amma sau dari ya fi, kuma a lokacin istigfari ya daga hannunsa na hagu ya kirga da na dama. Abin da ya fi shi ne; ya ce: "astagfirullah min jami'i zulmi wa jurmi wa israfi fi amri wa atubu ilaih". Kuma ya isa ya ce: "astagfirullah rabbi wa atubu ilaihi".
An so karantawa sau bakwai a ce: "haza makamul a'izi bika minan nar", kuma an so a fada sau dari uku ; "al'afw"!. Idan an fadi wasalin karshe sai a ce: "al'afwa" da fataha.
Falalarta ta isa girma cewa: Ubangiji ya yi wahayi ga Annabi Musa (A.S) yana cewa; tashi cikin dare, ni kuma zan sanya kabarinka dausayi ne na aljanna(16).
Daga imam Ali (A.S) ya ce: tsayuwar dare mai sanya lafiya ce ga jiki(17).
Daga imam Ja'afar Sadik (A.S): sallar dare tana kyautata fuska kuma tana kyautata halaye kuma tana sanya kanshin jiki, kuma tana kawo arziki, kuma tana biyan bashi, kuma tana tafiyar da bakin ciki, kuma tana karfafa gani(18).
Daga gareshi (A.S) ya ce: wanda yake sallar dare kuma ya raya cewa yana kwana da yunwa ya yi karya(19).

Daga Ladubban Haihuwa

Akwai abubuwan da ake so yayin haihuwa da zamu yi nunin al'amura biyu game da su:

Al'amari na farko

An so yi wa abin haihuwa wanka yayin haihuwarsa da kuma yi masa kiran salla a kunnen dama da ikama a hagu da dura masa ruwan furat da kuma sanya masa suna rana ta bakwai, kuma an so aske gashinsa a yi sadaka da gashin da nauyinsa na zinare ko azurfa, idan kuwa ba a yi masa aski ba a ranar bakwai to mustahabbancin ya fadi.
Mustahabbi ne a yi masa akika (yanka masa ragon suna) da akuya/tumkiya ko rakumi a ranar bakwai, kuma duk abin da ya fi girma shi ya fi. Kuma ana son ba wa mai karbarsa ranar haihuwa (kamar unguwar zoma) kafa da cinyarta na abin da aka yanka, idan kuwa ba shi da unguwar zoma to sai a ba wa uwa wannan rabon, ita kuma sai ta ba wa wanda ta so. Idan kuwa unguwar zoma ta kasance bayahudiya ce da ba ta cin naman dabbobin musulmi sai a ba ta kimar wannan abin. Kuma an so sadaka da sashen abin yanka da dafa saura, sai a kira goma daga muminai su ci amma idan suka yi yawa hakan ya fi.
An so yi wa jariri kaciya ranar bakwai ga haihuwarsa, kuma da ba a yi masa kaciya ba to wajibi ne ya yi wa kansa idan ya balaga.
An so karanta wanan addu'a yayin kaciya: "allahumma hazihi sunnatika wasunnati nabiyyuka, wat tiba'an minna laka wali nabiyyika bi mashiyya tika, wa bi iradatika wa kadha'ika li amrin aradtahu wa kadha'in hatamtahu, wa amrin anfaztahu, wa azaktahu harral hadidi fi khitanihi, wa hijamatihi, li amri anta a'arafu bihi minni, allahumma fa dahhirhu minaz zunubi, wa zid fi umrihi, wadfa'al afati an badanih, wal auja'i an jismihi, wazid'hu minal gina, wad fa'a anhul fakar, fa innaka ta'alamu wala na'alamu".
An ruwaito daga imam Ja'afar Sadik (A.S) cewa an so karanta wannan addu'a ga yaro kafin balaga koda kuwa ba a karanta masa ba yayin kaciya, hakika Allah zai kare wannan yaron daga zafin karfe na kisa.
Sannan idan ba a yi masa akika ba, to an so har zuwa karshen rayuwarsa koda kuwa ya mutu ne, kuma abin da yafi na akika idan namiji ne to sai a yanka namiji daga dabbobi, idan mace ce sai a yanka mata mace, amma wanin wannan to namijin dabba za a yanka. Kuma dabbar akika ba ta da sharadin dabbar layya, idan ba a samu dabbar ba to bai isa ba a yi sadaka da kimarta.
Ya halatta ga uba ko uwa su ci daga akikar (ragon sunan) 'ya'yansu sai dai an karhanta, haka nan an karhanta ga wadanda suke da kusanci da shi, amma ga uwa karhancin ya fi muni.
Sannan abin da ya fi shi ne a yanka akika daga gabarta, kada a karya kashinta, amma ba mu sami wani dalili ba a kan cewa a binne kashinta, ya halatta a yanyanka ta sai a ba wa makwabta amma abin da yafi a dafa a kira wasu muminai su ci.
Akika ba ta kebanta da talakawa don haka ya halatta a ba wa masu kudi haka nan sharifai, koda kuwa akikar ba ta sharifi ba ce, idan uba bai yi wa dansa ragon suna ba to an so ga da ya yi wa kansa idan ya girma, amma layya tana isarwa ga ragon suna.
Da yaro zai rayu har zuwa azahar din rana ta bakwai to an so yi masa akika da ya mutu bayan azahar ne, amma idan bai kai azahar ba to akika ta saraya.

Al'amari na biyu

Hakika mafificin abinci ga jariri shi ne nono, kuma mafificin nono shi ne na uwa, sai dai bai wajaba a kanta ta shayar da shi ba in ba da lada ba, kuma ladanta yana kan mahaifinsa, don haka yana halatta ga uwa ta karbi ladan shayar da yaro, duk da abin da ya fi shi ne kada ta karba.
Amma da Uba ba zai iya biya ba, ko kuma ba shi da abin biya to a nan wajibi ne kan uwa ta shayar da shi.
Sannan da jariri yana da dukiya ya halatta ga uba ya bayar daga dukiyarsa, kuma an so uwa ta shayar da jariri daga nonota duka biyu, kuma muddar shayarwa shekara biyu ce cikakkiya, bai halatta ba a rage daga shekarun biyu sai wata uku kawai, kuma bai halatta a rage kasa da hakan ba sai idan akwai larura, sannan kuma abin da ya fi kada a haura shekaru biyu.
Da uwar a wannan mudda ta shayar da danta kyauta ko kuma daidai gwargwadon ladan da wata matar zata iya karba idan ta shayar da shi, to bai halatta ba ga uba ya karbe da daga gareta, amma da ta nemi kudi sama da ladan da wata matar zata karba to ya halatta ya karba ya ba wa wata matar don ta shayar da shi.
Sannan kuma uwa ita take da hakkin tarbiyyar renon da har zuwa shekaru biyu, amma idan 'ya ce to har zuwa shekaru bakwai idan ta kasance musulma ce kuma 'ya, mai hankali, amintacciya, kuma ba ta da wani miji sai shi. A wannan yanayi bai halatta ba ga miji ya kwace dansa/'yarsa a wannan mudda da muka ambata a sama, amma bayan wannan mudda to hakkin reno yana ga uba ne, idan ya mutu sai hakkin ya koma hannun uwa, wasiyyin uba ba shi da iko a kan hakkin miji. Allah ne mafi sani.
Wannan shi ne karshen abin da muka so kawo wa a takaice na daga kashe-kashen koyarwar musulunci madaukakiya, wacce take wajaba a kan dukkan musulmi ya koye ta ya yi aiki da ita, domin mu rabauta duniya da rayuwar ni'ima kuma rabauta a lahira da rayuwar aljanna madawwamiya mai wanzuwa in Allah ya so. Ga Allah muke neman taimako da dacewa.