Bangare Na Biyu


::.

Rassana Al'amuran Addini

::.

Zamantakewar Al'umma Da Tsarin Musulunci

::.

Musulunci Da Siyasa

::.

Ayyukan Hukumar Musulunci

::.

Tattalin Arzikin Musulunci

::.

Lamunin Rayuwa A Musulunci

::.

Musulunci Da Rundunar Yaki

::.

Tattalin Kayan Yaki

::.

'Yanci A Musulunci

::.

Tsarin Kotun Musulunci

::.

Kiwon Lafiya A Musulunci
::. Al'adun Musulunci
::. Aminci Da Tsaro Da Zaman Lafiya A Musulunci
::. Yi Wa Masu Laifi Ukuba Da Kuma Kama Su
::. Ukubar (Horon) Kurkuku
::. Samar Da Aminci Ga Kowa
::. Musulunci Da Gina Iyali
::. Ra'ayin Musulunci Game Da Mace
::. Aure A Mahangar Musulunci

Rassana Al'amuran Addini

Kafin mu fara bayani kan wannan bangare ta koyarwar musulunci babu laifi mu yi nuni da kashi na farko na koyarwar musulunci madaukakiya, wato usuluddini wacce magana ta gabata game da ita, kuma wajibi ne mutum ya yi imani da ita, domin ta damfaru da tunanin da akida ne don haka bai isa ba ya bi wani a kanta.
Amma rassan addini na hukunce-hukunce wadanda yanzu zamu yi magana a kanta to ta shafi dukkan rayuwar mutane ne kuma dukkan motsin mutum tun daga haihuwarsa har bayan mutumwarsa kuma tun da ba kowane mutum ba ne zai iya yin ijtihadi wato; ya fitar da hukunce-hukuncen daga dalilansu ba wadanda suka hada da kur'ani mai girma da sunna madaukakiya da haduwar malamai da kuma hankali to sai musulunci ya halatta wa mutum ya yi koyi da mujtahidi mai cika sharuddan takalidi (koyi da shi) a ciki, kuma ya koma masa wajen sanin hukunce-hukuncen shari'a domin ya saukaka masa.
Rassan addinin suna da yawa amma mu zamu yi nuni da mafi muhimmancinta sanannu goma sannan sai mu yi bayanin abin da ake bukatarsa in Allah ya so, wadannan goman su ne:
1. Salla
2. Azumi
3. Humusi
4. Zakka
5. Hajji
6. Jihadi
7. Umarni da kyakkyawa
8. Hani ga mummuna
9. Mika wilaya ga waliyyan Allah
10. Barranta daga makiya Allah
Sannan idan an hada da wasu rassan zaka samu ciniki; saye da sayarwa, aure, saki, kisasi, diyya, wadanda zamu yi bincikensu da fadi a bangaren mas'aloli. Sai dai akwai wani bangare mai muhimmanci a wannan zamin na mu da ya hada da: zamantakewar dan Adam, tsarin al'umma da siyasa, da tattalin arziki, da runduna, da kuma soja, da kotu, da hukunci, da wayewa, da kafofin watsa labarai, da lafiya, da likitanci, da 'yancin dan Adam, da na al'umma da sauransu wadanda zamu yi bayaninsu a wannan bangare ne in Allah ya so.

Zamantakewar Al'umma Da Tsarin Musulunci

Ba makawa musulunci yana da tasiri na musamman na hukunci kuma da tafiyar da al'amuran al'umma, kuma babu makawa an aiwatar da wannan tsari a kasashen musulmi kusan karni goma sha uku har sai da daular musulunci ta fadi kusan sama da karni.
Sannan kuma kowane mutum shaida ne a kan cewa cigaban musulunci ya kasance misali ne matuka kuma musulunci ya aiwatar da hukunci na warware matsalolin duniya, kuma da an dawo da wannan hukunci da duniya ta zama aljanna mai ni'ima kuma da mutane sun rayu a inuwar hukuma suna masu ni'mutwa.
Don haka: Wannan wane tsari ne? Shin zai yiwu tsarin musulunci ya komo a wannan rayuwa ta roket da kwayar zarra da kuma intanet da sauransu? Yaya zai warware matsaloli idan da zai karbi jagoranci?
Lallai wadannan tambayoyi ne da suke bukatar jawabi…
Amma mu mukan iya bayar da amsar da zata sanya mai karatu ya yi mamaki har ya yi tsammanin muna maganar aljannar duniya ce, tare da cewa mu a shirye muke mu kawar da wannan mamakin nasa ta hanyar kawo dalilai na musulunci a kan kowace amsa kuma mu kawo masa dalili da misali na tarihin hukumar musulunci, na daga abin da zai iya nuna masa karfin tsarin musulunci da ikon dawowa wannan rayuwa da kuma jagorantar duniya wannan kuwa duk da murya mai karfi. domin shi ne kawai tsarin da zai iya jagorantar rayuwa a da can da kuma a yanzu da kuma nan gaba, saboda hikimar dokokinsa na Allah a kan tafiyar da al'amuran rayuwar mutane da nufin da zai iya kai shi ga cimma burinsa da warware matsaloli da kuma kawar da abin da yake cuta da jahilci da rasin lafiya da kuma kai wannan duniya zuwa ga gacin aminci da kuma kai shi zuwa ga arzuta da dacewar duniya da lahira. Wannan tsarin yana kunshe da cigaba da kuma dukkan abin da mutum yake bukata a wannan yanayi: na siyasa da tattalin arziki da 'yanci da sauransu:

Musulunci Da Siyasa

T. Shin akwai siyasa a musulunci?
A. Na'am: a cikinsa akwai mafi kyawun siyasa da kuma duk wani nau'in hukunci na tafiyar da kasa da bayi.
T. Shin hukumar musulunci ta mulkin kai ce, ko kuma tsarin sarauta?
A. Ita ba mulkin kai ba ce ko sarauta da ake nufi a yau a yammacin duniya, shi tsari ne na shawara da abin da ake nufi da shawartawa, kuma ta wannan yanayi ana iya ce masa mulkin kai, amma babu wani mulki na hukumar gado a musulunci.
T. Menene siffofin shugaban musulmi?
A. Shi ne mutum da yake mumini mai ilimin addini cikakke kuma ya san sha'anonin duniya da kuma siffantuwa da adalci, to duk sadda wadannan siffofi suka cika ga mutum, kuma mafi yawan mutane suka yarda da shi to ya zama shugaba, amma idan aka rasa daya daga cikin wadannan siffofi to ya sauka daga matsayinsa da gaggawa, haka nan idan al'umma ba su yarda ya wanzu shugaba ba, to suna da hakkin canza shi su kawo wanda ya cika sharudda.
T. Wanene yake ayyana shugaba a musulunci?
A. Mafi yawan al'umma, amma wannnan idan bai kasance ma'asumi ba kamar Annabi ko Imami (A.S).

Nau'in Hukunci Da Na'uin Hukuma

T. Shin a musulunci akwai zabe ko jin ra'ayin mutane da kuma jefa kuri'a da hukumar kasa da ta gari da sauransu.
A. Na'am duk akwai wannan a zamaninmu zamanin boyuwar imam Mahadi (A.S) amma da yanayi na musulunci, misali:
Na daya: Majalisa tana zartarwa da aiwatarwa ga dukkan dokokin da suka zo, amma ba domin ta shar'anta ba, domin shar'antawa wannan aiki ne kuma hakki ne na Allah madaukaki.
Na biyu: babu tawaya a dokokin musulunci kuma babu gajiyawa a ciki balle mu bukaci shar'antawa ko sanya dokoki, a hadisi ya zo cewa "musulunci ya bayyana mana komai hatta da hukuncin yakushi" a wani hadisin ya zo cewa: "halal din Muhammad halal ne har zuwa ranar kiyama, kuma haram dinsa haramun ce har zuwa ranar kiyama"(1).
Saboda haka bai kamata ba ga wani mutum ya haramta ko ya haltta, hakkin da mutane suke da shi na aiwatarwa ne ko zartarwa. Misali: musulunci ya hukunta cewa ciniki hakkin mutane ne haka nan tijara, don haka majalisa ba ta da hakkin canja wannan ta sanya shi ga wasu mutane kawai ko ga wata hukuma kawai. Haka nan musulunci game da titi bai ce a bi ta dama ko hagu ba, don haka majalisa tana da hakkin hakan domin musulunci addini ne na tsari ba hargitsi ba, shi kuwa ayyana ta dama za a bi ko ta hagu tsari ne wanda musulunci ya yi hukunci da shi kuma ya shar'anta shi, to haka zaka kiyasata sauran abubuwa.
T: Don me muke ganin tawaya da matsaloli a yau a shar'antawa ko tsarawa a kasashen musulmi?
A: Su wadannan kasashe a suna ne suke na musulunci amma babu wani abu da ya wuce haka –wato a aikace ba na musulunci ba ne- Allah yana cewa: "duk wanda ya kauce wa ambato na to yana da rayuwa mai kunci, kuma ranar lahira za a tashe shi makaho"(2). Don haka duk wanda ya kauce wa tsarin musulunci to zai kuntata rayuwarsa kamar yadda muke ganin kunci a kasashen musulmi a yau, kuma a lahira yana da aibi da wuta.

Ayyukan Hukumar Musulunci

T. Mene ne ayyukan hukumar musulunci game da al'umma"
A. Ayyukanta su ne kiyaye adalci tsakanin mutane a waje da ciki da cigabantar da rayuwar mutane da kuma yi musu tanadin: arziki da dukiya da koyar da su da wayar da su da kuma kiyaye amincinsu da zaman lafiyar su.
T. Menene doka wacce hukumar musulunci take aiki da ita"
A. Doka ce wacce aka samu daga Kur'ani da Sunna da Ijma'i da hankali.
T. Wane ne mai tsara doka a matsayin aiki da ita?
A. Su ne malamai masu adalci daga makomar al'umma, masana da addini da duniya wadanda mutane suke koma wa garesu a koyi.
T. Shin akwai kungiyoyi a musulunci?
A. Ba laifi da kungiyoyi a karkashin kulawar malamai idan sun kasance domin cigaban al'umma ne kuma don aikin zartarwa ba shar'antawa ba, domin shar'antawa aiki ne na Allah (S.W.T)(3).

Tattalin Arzikin Musulunci

T. Shin a musulunci akwai tattalin arzikin?
Na'am shi ne ma mafi tsarin wanda duniya ta taba gani.
A. Shin tattalin arzikin musulunci dan jari hujja ne ko kuma gurguzu ko kuma na rabawa na tsatsauran gurguzu?
T. Shi tsari ne ba na jari hujja ba, kuma ba na guguzu ba, kuma ba na rabawa ba da ma'anar da aka sani a yau.
T: To yaya tsarin tattalin arizikin musulunci yake kenan?
A: Shi tsarin musulunci yana girmama ikon mallakar daidaikun mutane ga dukiya kuma yana tabbatar da hakan da sharadin kada dukiya ta kasnce ta haram kuma ya bayar da hakkinta(4).
T. Yaya dukiya take taruwa ga daula?
A. Ta hanyar hakkokin da suke wajibi da aka sanya a musulunci.
T. Wane hakkoki ne na wajibi?
A. Su guda hudu ne: humusi, zakka, haraji, jizya.

Madogarar Dukiya A Musulunci

T. Menene ake nufi da madogarar samun dukiya a musulunci ga daula da kuka ambata?
A. Humusi: shi dukiya ce da shugaban musulmi yake karbar kashi ishirin cikin dari nata: daga ribar cinikayya da kuma ma'adinai, da taskoki, da abin da aka samu a karkashin ruwa, da dukiyar halal da cakuda da haram da kuma ganimar yaki da kuma wani kaso daga kasa.
Zakka: dukiya ce da shugaban yake karba daga daya cikin arba'in na tumaki da shanu da rakuma da zinare da azurfa da dabino da zabib da sha'ir da alkama.
Haraji: shi ne abin da shugaban yake karba daga masu shuka a kasashen da aka ci su da yaki da kai hari.
Jizya: shi ne abin da shugaban musulmi yake karba daga Yahudawa da Nasara da majusawa da suke karkashin alkawari da sauran kafirai domin a kare su kuma su samu kariya.
T. Shin a musulunci akwai banki?
A. Na'am sai dai kada ya kasance akwai riba ko karbar kari, domin a musulunci ana ganin riba a matsayin yaki da Allah da manzonsa, kuma a aiwatar da dokokin musulunci a dukkan hukunce-hukuncen banki, kuma ana tafiyar da hakkokin masu aiki daga dukiyarsa (banki) amma idan ta tawaya to sai a ba su daga Baitulmali.
T. Shin daula tana iya karbar wani abu daga mutane bayan wannan?
A. A'a, daula ba ta da hakkin karbar wanin wannan daga mutane, kuma ya zo a hadisi cewa; Wanda ya karbi dukiyar wani ba tare da yardarsa ba, to Allah zai kwatar masa a ranar lahira maimakon kowane dirhami salla dari bakwai daga sallolinsa karbabbu a bayar da ita ga mai dukiya.

Baitulmali (Gidan Dukiyar Daula)

T. Me daular musulunci zata yi da abin da take karba na dukiyoyi?
A. Daular musulunci tana da wani ofis da ake kira Baitulmali da ake boye dukiyar a cikinsa kuma ana tanadin sa ne domin bukatun dukkan mabukatan musulmi.
Daula ce take yin dukkan ayyukan gyara da raya kasa da ci gaba, kuma ta dauki nauyin duk wani talaka da dukiya isasshiya domin tafiyar da rayuwarsa, har sai ya kasance babu wani talaka a kasa.
Kuma a biya bukatar duk wani mai bukata,, wanda yake bukatar aure ko jari ko gida ko kanti ko likita don magani ko kuma tafiya ta lalura, ko yana neman guzuri a kan hanyar tafiyarsa ko kuma karatu da yake bukatar dukiya da sauransu to wannan duk yana komawa ga Baitulmali ne, kuma hanyar tabbatar da bukatarsa tana da sauki, wato; ita ce shedu biyu ko rantsuwa a kan cewa yana bukatar abu kaza kuma ba shi da dukiya da zata ishe shi, to ta haka ne zai kasance babu wani mabukaci ko talaka da zai ragu a daula.
T. Shin wadannan hakkoki hudu sun isa dukkan bukatun mutane?
A. Wannan ya isa idan aka hada da abin da daula take samu na Anfal, kuma ya zo a hadisi cewa; "idan ma ba ta isa ba to Allah zai kara yawanta"(5).

Karancin Ofisoshi Da Ma'aikata

T. Yaya dukiyar da kuka ambata zata isa tare da karancinta, kuma muna ganin yau ga dukiya mai yawa amma ba ta isa?
A. Zata isa saboda karancin ma'aikata da kuma rikon amanar masu kula da ita, da kuma barin al'amura a hannun mutane. Misali: masu aiki a daula ba su da yawa kuma mafi yawan ayyukan hukuma a yau suna hannun mutane ne, sai ayyukan hukuma suka zama ba su da yawa sosai, kuma abin sani cewa idan ma'aikata suka yi karanci kuma aka bar al'amura a hannun mutane kuma masu kula da albarkatun kasa suka zama amintattu, to dukiya zata yawaita(6).
T: Shin ana ba wa wanda ya kasa aiki dukiyar?
A: Idan talaka ya kasance ba zai iya aiki ba to ana ba shi daidai gwargwadon bukatarsa kamar yadda yake bisa al'adar hukumomi a yau(7).

Lamunin Rayuwa A Musulunci(8)

T. Shin a musulunci akwai lamunin rayuwa?
A. Na'am kuma shi ne mafi kyawun lamuni na al'umma kuma mafi daukaka.
T. Shin zaku iya yi mana bayanin wani abu na lamunin rayuwar al'umma a musulunci?
A. Lamunin rayuwar al'umma a musulunci –wato daukar nauyin rayuwa da matsalolin al'umma- wani abu ne da ya kai matukar da ba a taba samun irinsa ba a wani tsari a fadin tarihin samuwar dan Adam.

Misalan Lamunin Rayuwar Al'umma Na Musulunci

Musulunci ya lamunce rayuwa yana cewa:
1. Dukkan wanda ya mutu yana da bashi ko ya bar iyali ba mai kula da su, to yana kan jagoran musulmi ya biya bashinsa kuma yana kansa ya reni iyalansa.
2. Duk wanda ya mutu yana da dukiya to dukiyarsa ta magadansa ce gaba daya.
3. Hade kuma da hidimar dukiya da Baitulmali yake yi wa mutane, domin daukar nauyin bukatunsu na farko.
Da kuma yalwata musu.
T. Shin kana iya ganin duk da haka akwai lamunin rayuwar al'umma irin wannan a duk duniya hatta da inda ake da cigaban wayewa?
A. Tabbas babu.
Kai tsari na jahiliyya kafin musulunci da kuma na cigaban zamani a yau suna ma sanya haraji mai yawa ne a kan gado, kamar yadda kuma ba sa daukar nauyin biyan bashin wani mutum ko kuma daukar kulawa da iyalansa, kuma ba laifi idan muka kawo wasu misalai kan lamunin musulunci kamar haka.

Misali na farko

Akwai ruwayoyi masu yawa da suka zo game da lamuntar al'amuran al'umma da zamu kawo wata kamar hakan:
Daga Abu Abdullahi (A.S) ya ce: manzon (S.A.W) ya ce: "Ni ne na fi cancanta da kowane mumini fiye da kansa kuma Ali (A.S) shi ne ya fi cancanta da shi bayana". Sai aka ce da shi (imam Ja'afar Sadik) me wannan yake nufi? Sai ya ce: fadin Annabi (S.A.W) wanda ya bar bashi ko kaya to suna kaina, wanda kuwa ya bar dukiya to ta magadansa ce"(9).

Misali na biyu

Ali bn Ibrahim ya kawo a tafsirinsa daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "Babu wani wanda yake bin bashi da zai tafi da wanda yake bi bashi wajen wani jagora na musulmi kuma ta bayyana ga wannan shugaban cewa ba shi da shi, to sai shi wannan talakan marashi ya kubuta daga bashinsa kuma bashinsa ya koma kan jagoran musulmi da zai biya daga abin da yake hannunsa na dukiyar musulmi"(10).
Imam Sadik bayan ya fadi wannan hadisi daga Manzon Allah (S.A.W) sai ya ce: "babu wani dalili da ya sanya mafi yawan yahudawa musulunta sai bayan wannan magana ta Annabi (S.A.W), kuma sun yi imani da su da iyalansu"(11).

Misali na uku

Sheikh Mufid ya karbo daga majalisinsa da sanadin da muka ambata daga imam Ja'afar Sadik (A.S) yana cewa: Manzon Allah (S.A.W) ya hau kan mimbari sai fuskarsa ta canja kuma launi ya juya sannan sai ya fuskanto da fuskarsa ya ce: "ya ku jama'ar musulmi! ni an aiko ni ne kusa da alkiyama … -har inda yake cewa- ya ku mutane wanda ya bar dukiya to taiyalinsa ce da magadansa, amma wanda ya bar wani nauyi ko rashi to yana kaina a zo gareni"(12).
Hakan na ya karbo daga Abu Abdullahi (A.S) ya ce: wanda yake da wata dukiya kan wani mutum da ya karba kuma bai ciyar da ita a barna ko sabo ba sai ya kasa biya, to wanda yake binsa dole ne ya jira shi har sai Allah ya arzuta shi sai ya biya shi, idan kuwa akwai jagora mai adalci to yana kansa ne ya biya masa bashinsa, saboda fadin Manzon Allah (S.A.W) acewa:"duk wanda ya bar dukiya to ta magadansa ce, kuma wanda ya bar bashi ko wani rashi to yana kaina ku zo gareni, don haka yana kan jagora duk abin da yake kan Annabi (S.A.W)(13).

Misali na hudu

Musulunci ya sanya kusan dukkan daula da take kusan fadin kwata na duniya gaba daya talauci ya kawu daga gareta ya kasance labari ne.
Hurrul amuli ya ambaci cewa: imam Ali (A.S) yana tafiya a cikin lungunan garin Kufa wata rana, sai ya ga wani mutum yana rokon mutane, sai ya yi mamaki sosai, sai ya juya da shi da wadanda suke tare da shi suna tambayarsa menene haka?
Sai ya ce: ni tsoho ne kuma kirista na tsufa ba na iya aiki kuma ba ni da wata dukiya da zan rayu da ita, sai na shiga bara.
Sai imam Ali (A.S) ya yi fushi ya ce: kun sanya shi aiki yana saurayi sai da ya tsufa zaku bar shi?! Sai ya yi umarni a sanya wa wannan kirista wani abu daga Baitulmali albashi da zai rika rayuwa da shi(14).
Wanan kissa tana nuna cewa; talauci ya kusa kawuwa gaba daya har sai da ya kasance ba shi da wani mahalli a daular musulunci. Hatta imam Ali (A.S) da ya ga talaka guda daya sai da ya yi mamakinsa, ya gan shi wani abu bare da bai dace da al'ummar musulmi ba. Sannan ya yi umarni da a sanya masa albashi da zai rayu da shi tare da cewa shi kirista ne da baya riko da musulunci, domin kada a samu talaka a kasar musulmi da zai fito koda kuwa mutum daya ne. Kuma domin duniya ta san abin da musulmi suke a kai na yaki da talauci: da cewa kuma hukumar musulunci ita ce take yaki da talauci ta kuma daukaka matsayin talakawa ba kawai musulmi ba, har da wasunsu na daga kafirai matukar suna karkashin daular.

Misali na biyar

Kulaini ya karbo daga Hasan ya ce: yayin da Ali (A.S) ya rusa Dalha da zubair sai mutane suka guda suna ababan rusawa, sai suka wuce wata mata a kan hanya ta firgita daga garesu ta yi bari saboda tsoro, kuma dan nata ya fito rayayye sannan sai ya mutu. Sannan sai uwar ma ta mutu, sai imam Ali (A.S) da sahabbansa suka same ta an jefar da ita da danta a kan hanya, sai ya tambaye su me ya same ta?
Sai suka ce: tana da ciki ne sai ta ji tsoro da ta ga yaki da rushewar mutane da gudunsu.
Sai ya tambaye ta waye ya riga mutuwa a cikinsu?
Sai suka ce danta ya riga ta mutuwa.
Sai ya kira mijinta baban yaron mamaci ya ba shi gadon sulusin diyyar dansa, sannan sai kuma ya gadar da uwar sulusi, sannan kuma sai ya gadar da mijin rabin diyyar matar wacce ta gada daga dansa sannan sai ya ba wa makusantan matar ragowar gadonta, sannan kuma sai ya gadar da mijin rabin diyyar matar wato dirhami dubu biyu da dari biyar sannan sai ya ba wa makusantanta rabin diyyarta wato dubu biyu da dari biyar na dirhami, wannan kuwa saboda ba ta da wani da banda wannan da ta jefar da shi ya mutu.
Ya ce: wannan kuwa duka ya bayar da shi ne daga Baitulmalin Basara(15).
Haka nan ne musulunci ya sanya Baitulmali domin amfanin al'ummar musulmi da kuma biyan bukatunsu, da bayar da hakkokinsu, wannan kuwa kamar yadda ya zo ne a hadisi cewa: hakkin mutum musulmi ba ya faduwa banza . A wani hadisin ya zo cewa: jinin mutum musulmi ba ya tafiya banza. Da wannan ne musulunci ya yalwata wa al'umma da yalwa da arziki da kuma lamunce rayuwar al'umma da adalci.

Musulunci Da Rundunar Yaki

T: Shin akwai rundunar yaki a musulunci?
A: Na'am, kuma mafi kyawun tsarin runduna.
T: Shin akwai tsarin yin aikin soja na tilas a musulunci?
A: Babu wannan, yin aikin soja –koda na hidimar kasa ne- abu ne bisa zabi(17).
T: Yaya haka kuwa?
A: Daular musulunci tana da fadi mai yawa da take da makamai kuma take kwadaitar da mutane yin tirenin a lokutan da suke da dama, babu bambanci tsakin babba da karami(18).
Ta haka ne dukkan al'umam zasu iya sanin ayyukan yaki, kamar yadda su kuma masu aiki suna kasuwarsu, kuma da gun iyalansu, kowane mutum yana iya motsa jikinsa awa daya ko awa biyu a rana a misali sannan sai ya tafi kasuwancinsa.
Amma da za a kawo wa daula hari to dole ne a kan kowane mutum ya kare daular musulunci, kuma wanda yake kwadayin hidimar soja da kansa sai a sanya masa albashi domin ya tsaya a kan hakan ya yi hidima.

Tattalin Kayan Yaki

Me musulunci yake gani game da kayan yaki?
Musulunci yana ganin wajabcin tattalin abin da daula zata iya kare kanta da shi na makamai da kuma kare haramin daular musulunci da kiyaye amincin musulmi(19), don haka kamar yadda madaukaki yake fadi: "ku tanadar musu abin da zaku iya na karfi…"(20).
Me daula zata yi wa iyalin wanda aka kashe a yaki?
Idan iyali ne talakawa da ba zata iya aiki ba to sai a ba su gwargwadon bukatunsu kowace shekara, idan kuwa ba haka ba, to ba abin da za a ba su, sai dai idan akwai maslahar ba su.
Menene matsayin msulunci game da yaki da zaman sulhu?
Musulunci shi ne addinin zaman lafiya da sulhu da aminci kamar yadda Allah madaukaki yake cewa: "ku shiga cikin aminci gaba daya" . Don haka ne ma yake aiki domin yada aminci da amana da zaman lafiya a dukkan duniya kuma yake kokairn ganin ya kashe wutar yaki da kawar da fitinar yaki tsakanin mutane da kuma tuge asalinta da duk abin da yake karfafa wannan da kuma kafa abin da yake kawo soyayya da sulhu da tsarkaka da kuma barin yaki yayin kira zuwa ga sulhu koda kuwa da makiyi ne mayaudari. Madaukaki yana cewa: "idan suka karkata zuwa ga sulhu to karkata zuwa gareshi"(22). A lokaci guda yana hana mu tsanantawa da ta'addanci da yaudara da kisa da yaki da dukkan abin da yakan kai ga tsoratarwa ko firgitawa da rashin kwanciyar hankali a tsakanin mutane.

'Yanci A Musulunci

T. Shin akwai 'yanci a musulunci?
A. Na'am, kuma shi ne ma mafificin 'yanci da ba a taba samunsa a mafarkin dan Adam ba a cikin mafi cigaban duniya.
T. Menene 'yancin musulunci?
A. Suna da yawa, amma zamu kawo wasu daga ciki:

'Yancin Kasuwanci Da Tijara

'Yancin yin aiki da kuma kasuwanci da tijara, kowane mutum yana da 'yanci ya zabi sana'ar da yake so ko aiki ko kasuwanci, kuma yana iya yin kamun kifi da farauta da fitar da ma'adinai da taskoki da kuma kamo ko kange wani abu abin da yake halal ya mallaka. Kamar yadda yana iya odar kaya ko fitar da kayan da ya so, ko ya sayar ko ya saya, kuma babu wani hani kan haka, babu wani kudin kwastam a musulunci ko sharudda game da hakan.
Sai dai kawai kada wannan kayan su zama haramun ne a musulunci kamar giya, ko cin riba ko boye kaya ko cutarwa ga rayuwar mutane da tattalin arzikinsu.

'Yancin Sana'a Da Noma

Akwai 'yancin sana'a da noma, kuma duk wanda ya so ya yi shuka a wani fili duk yadda ya so to yana da ikon yin haka, babu wani abu na taskace noma ko filin noma a musulunci da ma'anar da ake cewa a yau.
Amma idan kasa ta kasance wacce aka ci da yaki ce to wajibi ne bayar da harajinta zuwa ga daula, kuma ana cewa da ita; kasar haraji. Idan kuwa manomi ya kasance talaka ne to wajibi kan daula ta tanada masa aibn da zai biya bukatunsa, kuma bai laifi mutum ya shuka komai ya so da yawansa da sharadin ba zai toshe wa wasu dama ba, kuma yana iya shuka komai ya so sai dai idan mai cutarwa ne ga mutane kamar koken da wiwi.
Kuma daula ba ta da ikon karbar komai sai abin da yake bisa sharadinsa kamar humusi da zakka bisa sharuddansu kamar yadda ya gabata.
Haka ma dukkan sana'o'i; kowa yana da 'yancin yinsu sai abin da ya kasance haramun ne a musuluci kamar sana'anta giya ko kayan maye.

'Yancin Gini Da Raya Kasa

'yancin gini daraya kasa; wanda ya ga dama yana iya raya kasa kowace iri ce kuwa, a karkasin hukumar musulunci mutm yana iya samun kasa ta halal kuma ya gina abin da ya ga dama a wannan filin, kamar gida ko mahalli, ko ma'aikata, ko masallaci, ko husainiyya, ko makaranta, ko asibiti, ko makamancin wannan da dukkan'yancinsa, kuma bai halatta ba ga daula ta riki ko kwabo daga gareshi saboda kasa ko makamncin haka.
Hakika musulunci ya tabbatar da cewa: "duk wanda ya raya wani fili to nasa ne" . sai dai idan kasar ta kasance an bude ta da yaki ne to dole ne ya bayar da ladan kasa ga daula.
Idan aka gudanar da wannan hukunci a kasa to wannan ya isa ya biya bukatun mutane na wajen zama, da kuma dauke matsalar wajen zama a dukkan kasashen musulmi(24).

'Yancin Zama Da Tafiya

Duk inda mutum ya ga dama zai iya zama ko ya tafi ya bar wurin duk wannan yana hannunsa ne, kuma babu wani sharadi ko iyaka takasa ko gari da musulunci ya yarda da ita. Kuma babu batun kabila ko yare ko launin fata, da wannan 'yancin nan ya zama babu wata kima ga passpot ko takardar shedar 'yan kasanci da dukkan ire-irensu, kamar yadda zamu ga wasu kasashen turai sun kawar da irin wannan mummnar bidi'a.

'Yancin Ayyukan Zamantakewa Da Na Siyasa

Duk wannan ya halatta sai abin da musulunci ya haramta wanda yake kadan ne kwarai da gaske, kuma babu wata ma'aikata ta leken asiri, domin musulunci ya hana leken asiri a kan kowane mutum. Kuma babu wani ofishin leken asiri a musulunci wannan duk bai halatta ba, sai dai akwai ofishin sanin al'amuran da suka shafi maslahar al'umma da kuma kare amincinta da gyaranta, a daular musulunci kowa yana da 'yanci a alkalami da bayani da magana da rubutu da kuma kafa jam'iyya ko kungiya ko tarayya ko tara taimakon da kyaututtuka da buga mujalla da jarida da assasa gidan rediyo da sauransu.

'Yancin Sauran Ayyuka

Akwai 'yancin daidaiku da na jama'a, misali: mutumin da ya san tuki to yana da hakkin tukin mota koda kuwa ba shi da takardu ko makamancinsu, kamar yadda mamaci ba shi da bukatar neman izini domin a binne shi, wannan yana kan ma'abotansa ne su shirya shi kuma su binne shi a ko'ina suka so, ko kuma inda ya yi wasiyya a binne shi ba tare da bayar da wani lada ko kudi da makamancinsu ba. Haka nan sauran al'amura suke.
T: wannan yana nufin jefar da mafiya yawan ofisoshi da ake da su?
A: Na'am haka ne, haka nan daular musulunci ta kasance ba ta da wasu ofisoshi masu yawa sai 'yan kadan, shi ya sa muka ce ma'aikata a daular musuluci 'yan kadan ne sosai, kuma mafi karancin yawansu shi yake kai rage nauyi mai yawa daga wuyan hukumar musulunci, kuma ba zai tsananta mata ba da kashe dukiya mai yawa.

Tsarin Kotun Musulunci

T: Shin a musulunci akwai alkali da kotu?
A: haka ne, akwai mafi kyawun tsarin kotu da alkalanci amusulucni da mafi adalcin alkali daga mazaje.
T: yaya ya kamata alkali da kotun musulunci su kasance?
A: wajibi ne alkali ya kasance namiji kuma mumini, adali, masanin hukunci, kuma mujtahidi a mas'alolinsa da hukuncinsa.
Hukunci kuwa dole ne ya kasance bisa shedu da rantsuwa ba tare da wani murgudi ba ko wani karkacewa ko biyan kudin kotu, ko na wani rubutu ba, kuma ba ya bukatar takardar shigar da kara ko kuma rijistar mai kai kara, da makamancin hakan kamar yadda yake a yau a kotuna da wajan hukunci.
Saboda wannan saukin da yake cikin kotun hukuncin musulunci ne ma da kuma adalci da take da shi muna iya ganin cewa; alkali daya yana iya jin dukkan kararrakin da ake yi kuma ya yi hukunci cikin kankanin lokuta a bisa dokokin musulunci da shedu adilai. Alkali daya yana iya isar gari guda mai miliyoyin al'umma ta yadda babu wata matsala da zata rage.
T: Daga ina ne albashin alkali yake?
A: Daga Baitulmali.
T: menene aikin alkali?
A: Ta hanyar taimakon masu taimakonsa zai iya yin ayyuka masu yawa a ofisoshi da ake da su a yau, yana kula da aikin wakafofi da kuma karbar dukiyar gajiyayyu domin ba su ita, da kuma taskace dukiyar wawa da kuma yi musu aure da saki da saye da sayarwa da jingina da haya da kuma raba rikici tsakanin mutane da gudanar da haddi a kansu(25).

Lauyanci A Musulunci

T: Shin a musulunci akwai tsarin lauyanci?
A: Babu tsarin lauyanci a musulunci da wannan ma'ana, kuma tsarin musulunci ba ya bukatar lauyoyi da wanan yawan, dukkan wadannan al'amura tsarin musulunci ya mayar da su ga hukunci ne cikin sauki da aminci.
T: Me musulunci zai yi da lauyoyi da ma'aikata da bai yarda da aikinsu ba?
A: Musulunci ba ya yin kai tsaye gaba gadi kan gyaran al'umma, yana bi ne sannu-sannu tare da su wajen aiwatar gayare-gyarensa.
Na farko: yana tanadar wa wadanda bai yarda da aikinsu ba abin da zai dace da su na aiki, sannan kuma sai ya ba su taimako daga taskar daula da abin da zai taimaka musu a sha'anin rayuwarsu, har sai sun samu aikin da suke so, bayan nan ba wani wanda kuma zai iya tawaye ga tsarin musulunci da tunanin cewa ba ya la'akari da aikinsa, domin musulunci ya tanadar masa aikinsa cikin yalwa da daukaka da mutumtawa.

Kiwon Lafiya A Musulunci

T: Shin akwai aikin lafiya a musulunci?
A: Na'am akwai mafi kyawun tsarin lafiya da magani kuma mafi tsarin hanya a yalwa da fadada, kuma ya shafi lafiyar jiki da ruhi da lafiyar mutum daya da ta jama'a da kyawun yanayi da al'umma.
T: yaya tsairn lafiya yake a musulucn?
A: musulunci ya sanya hanyoyi domin samu lafiya kamar guda uku:
1- Tsari kai da riga kafi: wannan yana kare mutum daya da al'umma da yanayi daga fadawa cikin cututtuka da rashin lafiya da annoba da sauransu ta hanyoyi kamar haka:
a-Haramta abubuwan da sukan jawo cututtuka da annoba kamar: giya, kayan maye, zina, luwadi, madigo, abubuwa masu cutarwa, waka, abubuwan da suke jawo fajirci, da tsaraici, da wuraren fajirci da kuma dandalin tsaraici.
b-Sunnanta kwadaitar da abubuwan da suka shafi ladabin zamantakewa da daidaiku da al'umam kamar tsafta, da wanka, da kaho, da tsaga, da azumi, da shafa mai, da aure, da dura, da kwalli, da farar kasa, da yadda ake ci da yadda ake sha, da tufafi, da mazauni da bacci da farkawa da sauransu.
2-Magani: wannan kuwa yana komawa ne zuwa ga yin magani na itaciya da na abin ci, kuma yana amfanarwa kwarai da gaske ga cuta cikin sauki, wannan kuwa koda ba ga kowa ba, to amma yana kore cututtuka sosai a farkon faruwarsu, kuma an fadi wannan a cikin littafin "Dibbun nabiyyi, da kuma Dibbul ayimma", da sauransu.
3-Kula da kai da kuma lafiyar waje, da hana waje lalacewa da gurbata da kuma kula da lafiyar mutum da kare shi daga fadawa annoba da kwalara, kamar yadda ya wajaba kan likitoci su kula sosai wajen maganin maras lafiya kuma su sani Allah yana ganinsu a ayyukansu, su kuma kula da tausayawa da tausasawa, kuma ya zo a hadisi cewa: "Likita mai ramawa ne koda kuwa kwararre ne". -wato; shi mai biya ne ga abin da ya lalata-.
Wannan kuwa yana iya sanya likita taka tsantsan dalura wajen yin magani kuma ya hana shi sakaci da yin magani, ko kuma ya ki bayar da magani na gaskiya, kuma wannan yana iya samar da karfin gasa wajen yin magani da kuma gano rashin lafiya da cuta.

Magani A Wannan Zamani

T: Shin ba kwa ganin cigaba sosai a maganin zamani?
A: Ba kokwanto cewa an samu ci gaba a wannan zamani sai wadancan abubuwan da muka ambata su ne kashin bayan samar da lafiya ta gaba daya wannan kuwa an rasa ta, shi ya sa muka ga cututtuka sun mamaye dan Adam da ban mamaki. Hatta yawan likitoci na wannan zamani da ake da shi da kuma kemist da wuraren bayar da magani da ake da su, ba su isar da bayar da lafiya ta gama gari ga mutane ba.
Muna iya ganin kakanninmu da suka rayu suna cikin koshin lafiya saboda kare tsarin musulunci da lafiyar da ta wuce misali cikakkiya har mutuwarsu.
Yayin da a yau muna iya ganin babu wani gida da ba shi da maras lafiya ko maras lafiya wadanda suke fama da wasu cututtuka ko wata cuta.
T: menene magani kenan?
A: Magani shi ne mutum ya yi kokarin ganin ya dawo da ka'idoji da dokoki na samun lafiya na musulunci a rayuwarsa da kuma aiwatar da shi a cikin al'ummarmu da kuma yin amfani da maganin wannan zamani namu saboda kuma fitar da abubuwan haramun da masu cutarwa daga al'umma, da kuma bude hanya sabuwa domin rige wajan yin magani, saboda a cakuda sabon magana na zamani da na da can, to haka ne 'yan Adam zasu kubuta daga rashin lafiya da cututtuka kuma a yi maganin miyagun cututtuka masu kashe garkuwar dan Adam.

Al'adun Musulunci

T: Shin a musulunci akwai tsarin wayewa da al'adu?
A: Na'am musulunci yana da mafi kyawun tsari na wayewa.
T: Menene shi?
A: Na farko ya wajebta neman ilimi ga musulmi maza da mata(26), kuma ya sanar da ilimin da yake nemansa wajibi ne ga mutane, kuma ya kasa shi gida uku: ilimin jiga-jigan addini da ilimin rassan hukunce-hukuncen addini da kuma ilimin kyawawan halaye. Kuma ya kwadaitar da neman sauran ilimomi kuma ya sanya shi saukakka ga mutum, kuma ya kwadaitar da aiwatar da ilimi a aiki kuma ya tanadar masa dukkan hanyoyi kuma ya lizimtawa daula taimakonsa.
T: Wannan duk abin da kuka fada zai kai ga cigaban musulmi ne, da daukakarsu, amma ya kuma muka gan su masu ci baya?
A: Sun ci baya ne saboda ba su yi aiki da musuluncin ba a ilimance tun ranar da suka bar tafarkin musulunci a wayewarasa da al'adunsa.
Amma a lokacin da suka yi aiki da shi to sun fi kasasehn yamma ci gaba, babban misali kan hakan shi ne; furucin da yamma suka yi su da kansu da wannan, kuma laburare da littattafai da makarantu da musulmi suka yi a da ya fi nasu da suke a yau a wannan zamani nesa ba kusa ba, duk da kuwa a yau akwai kayan zamani na cigaba.

Kayan Wayewa Na Zamani Na Cigaba

T: Menene matsayin musulunci game da kayan sadarwa na wannan zamani, wato; shin musulunci ya haramta makarantu, da cibiyoyi, da littattafai, da mujallu, da radio, da talebijin, da sinima, da majigi, da intanet, da setalayet da sauransu?
A: Musulunci yana karfafa dukkan wani abu da yake kaiwa ga yada wayewa tsakanin mutane kuma yake yada wayewar mutumtaka ta al'ummu, sai dai ya haramta fasadi da yada shi ta wannan hanya ne, idan babu wannan to musulunci shi ya fi kowa karbar wannan.
T: Menene bambanci tsakanin tsarin al'ada na musulunci da na yamma?
A; Bambancin shi ne: musulunci ya cakuda ilimi da imani ne da kuma ala'adar kyawawan halaye da dabi'u madaukaka, yayin da muka ga al'adun yammacin duniya a yau babu batun imani ko kyawawan halaye a cikinsu, don haka ne ilimi da yake mafificiyar hanyar yada cigaba da daukakar dan Adam, da yada aminci da zaman lafiya tsakanin mutane, sai ga shi ya koma babbar hanyar faduwar kyawawan halaye da tsoro da firgici da rikici da rashin zaman lafiya, da yaki da rusawa a cikin al'umma dukkaninta a duniya.

Aminci Da Tsaro Da Zaman Lafiya A Musulunci

T: shin musulunci addin ne na yaki ko na zaman lafiya?
A: Musulunci addini ne zaman lafiya, Allah yana cewa: "ya ku wadanda kuka yi imani ku shiga cikin aminci gaba daya"(27). Amma idan wani ya kawo hari a kan wani, ko ya kai hari da farmaki kan musulmi, to musulunci bai ce a tsaya haka nan ba a daure ko a kame hannaye, dole ne a yi kariya saboda adalci da gaskiya da kuma kawar da keta haddi da dauke zalunci.
T: Yaya musulunci yake taimakon zaman lafiya?
A: Musulunci yana ganin wajabcin aminci a ciki da waje; a ciki yana hana barna da laifi, a wajen kuma yana hana keta haddin wani kuma yana maganin masu keta haddi kan wasu.
T: yaye musulunci yake kawar da laifuffuka?
A: Yana kawar da su ne daga tushe, kuma ya na maganin abubuwan da suke kawo laifuffuka kamar, talauci, fasadi, jahilci, gaba, matsaloli, da sauransu kuma yana yakarsu har sai ya kawar da su gaba daya, sai laifuffuka su kawu da kansu.
Misali: talauci yana kawo sata, domin biyan bukatar barawo, giya da gidan karuwai suna kawo zina da maye da suke kawo laifuffuka, jahilci kuwa yana kawo gaba da jayayya da yaki da matsalolin iyali da dangi da laifuffuka.
A sakamakon tsarin musulunci mai karfi da kuma hanyarsa mai kyau yana kawar da talauci yana wadatar da talakawa kuma yana sanar da mutane cututtukan gidajen banza da giya sai su bar gidajen giya da wuraren holewa sai kuma ilimi ya mamaye al'umma kuma a kawar da gaba, kuma a warware matsaloli ta hanyar yin hukunci mai sauki a lokaci kankani, ta haka ne za a iya kawar da tushen laifuffuka da barna da kafa asasin kauna da soyayya da 'yan'uwantaka da hadin kai da aminci a tsakanin al'umma a duniya baki daya.

Yi Wa Masu Laifi Ukuba Da Kuma Kama Su

T: wanda ya yi lafi a musulunci yaya ake saka masa?
A: musulunci bayan ya samar da yanayi mai kyau da kuma kawar da abubuwan a suke kawo laifi a al'umma to ya sanya ukuba a kan mai laifi, domin ya san cewa wanda ya yi laifi yanzu to ya yi ne saboda muninsa da karkacewarsa da kuma gabarsa ga al'umma da 'ya'yanta amintattu, don haka mai laifi yana muzanta al'umma ne kuma yana gurbata fuskar jama'a kuma yana rushe zaman lafiyarsa ne, kuma yana hana su nutsuwa, sai musulunci ya tanadi ukuba ta gaggawa domin kawar da wannan da samar da yanayi mai kyau domin kada laifi ya maimaitu.
Kuma ba ya boyuwa cewa musulunci bai bayar da damar aiwatar da hukuncin doka ta ukuba ba kawai da barin sauran hukunce-hukunce kamar yadda muke ganin a kasashen musulmi a yau, wannan kuwa shisshigi ne ga musulunci shi kansa, domin gurbata sunansa ne kuma hanya ce ta ba shi sunan mugunta da kekasar zuciya.

Ukubar (Horon) Kurkuku

T: Me musulunci yake yi da kurkuku?
A: musulunci yana ganin dokokin kasashe ba su da amfani, a wajen sa dokokin Allah su kadai ne suke da kima, saboda haka ne mafi yawancin laifuffuka da muke ganin a doka a yau da yawansu a musulunci ba laifi ba ne, balle a sanya mutane kurkuku domin sun aikata su. Amma abin da musulunci yake ganinsa laifi kamar sata da zina ya riga ya ayyana musu ukuba wacce ba kurkuku ba ne.
Sai dai akwai wasu na'uin laifuffuka kadan da musulunci ya sanya musu hukuncin tsarewa kamar mai taurin bashi, kuma kurkuku a musulunci yana nufin alkali ya mika mai taurin bashi hannun mai binsa bashi domin ya tsare shi a daya daga gidajen makusantansa, don haka babu kurkuku a musulunci da wannan ma'anar da muke gani a yau a kasashen musulmi gaba daya, idan ma an bukaci kurkuku to bai wuce wani gini ba da zai zama kamar makaranta ce ga mai laifi domin koyar da shi al'adu na musulunci na gari.

Samar Da Aminci Ga Kowa

T: Yaya musulunci yake samar da zaman lafiya a waje da kuma ga kowa?
A: Musulunci ba ya ketare iyakar kowa, kuma duk wata daula da ta nemi zaman lafiya da musulmi to su ma yana kansu su zauna lafiya da ita, Allah (S.W.T) yana cewa: "idan suka karkata ga zaman lafiya to sai ka karkata zuwa ga hakan"(28). idan kuwa aka ketare iyakar daula to dole ne musulmi su kare kansu da mafi kyawun hanya da tarihin dan Adam bai taba ganin irinsa ba.
T: Yaya musulunci yake kiyaye aminci tsakanin hukuma da jama'a?
A: Hukuma a musulunci ta mutane ce, don haka ba abin da mutane suke so sai tarayya wajen bayar da ra'ayi, da wadata da ilimi da 'yanci da aminci da lafiya da daukaka, da duk wani abu da zai kai ga yalwatawa. Don haka ne muka ga hukumomi na gari na musulunci suna dadewa sosai, wannan kuwa saboda kauna da take tsaknin hukuma da al'umma ne, kuma shugaba zaka ga ba ya bukatar wasu masu kariya ko kungiyar leken asiri ko masu gadi da zasu kare shi daga mutane.

Musulunci Da Gina Iyali

T: Yaya musulunci yake ganin tsarin iyali?
A: Musulunci yana ganin yin iyali -bayan daidaiku- su ne asasi na farko don gina jama'a ta gari, don haka ne yake kwadaitarwa domin gyara al'umma, sai ya wajabta hijabi ga mace yana mai cewa: "idan zaku tambaye su wani abu, to ku tambaye su ta bayan hijabi"(29). Ta wannan hanyar ne munanan zasu yi karanci kuma alakar namiji da matarsa ta yi karfi sosai, sai iyali su rayu cikin yanayi mai kyau, mai arzuta, mai yalwa da so da kauna. Mu sani cewa: hijabi shi ne; mace kada ta bayyanar da gashinta da jikinta ga wani mutum daban.
T: shin muuslunci ya hana mace ilimi da aiki?
A: Ba haka ba ne, musulunci bai haramta wa mace ilimi ba ko aiki, ya ma wajabta mata wannan wani lokaci, kuma ya so mata su wani lokaci. Abin da ya haramta mata shi ne: fita da tsaraici kamar yadda ya haramta mata aikin da zai hana ta kamewa.

Ra'ayin Musulunci Game Da Mace

T: Menene ra'ayin musulunci game da mace?
A: Musulunci shi ne addinin da ya fi kowanne tausaya wa mace a tarihin dan Adam, kuma yana ganin rayuwar iyali ba ta cika sai da wahala a wajen gida, da kuma zama a cikin gida, don haka ne ma ya raba rayuwar gida biyu domin ya karfafi soyayya da kaunar juna ta taimakekeniya, don haka sai ya ba wa namiji aikin wajen, ya kuma ba wa mace aikin cikin gida.
Ya sanya aikin cikin gida a hannun mace, domin mace ta fi namiji iya tafiyar da al'amuran cikin gida musamman tarbiyyar yara da kuma kula da lafiyarsu. Ita ce ta fi cancanta da yanayin tarbiyyar yara ta fuskacin tunani da tausayi. Addinin musulunci mai hikima yana ganin da an ba ta aikin namiji da yake wajen gida da wannan yana nufin a dora aikinta da yake cikin gida a kan namiji kenan, don haka ne sai ya bar aikin wahala na wajen gida a kan namiji ita kuma ya ba ta aikin cikin gida(30), ba don haka ba da an samu sakamako maras kyau.

Aure A Mahangar Musulunci

T: Menene ra'ayin musulunci game da aure?
A: musulunci yana ganin halaccin aure kuma yana karfafawa kan hakan, kuma yana umarni da shi kuma yana murna da aure da wuri, wannan kuwa yayin da kowanne mace da namiji ya cika shekarun kamalarsa, ga mace shekaru tara tare da girmanta da cikarta, namiji kuwa ya kai kamalarsa shekaru goma sha biyar tare da girmansa da cikarsa, a lokacin ne yake karfafa yin aure domin kada alfasha ta wakana.
T: menene ra'ayin musulunci game da cakudar samari da 'yan mata a kowane janibi na rayuwa?
A: duk wata cakuda da zata kawo rushewar al'umma gaba daya ba ta halatta; koda a makaranta ne ko wajan iyo a ruwa, ko sinima ko ma'aikata, ko zamantakewa, ko wurin taro ko makamancin wannan, don haka ne musulunci ya hana hakan sai dai idan cakuda wacce take akwai cikakkiyar kiyayewa da hijabi da kamewa kamar cakuda a hajjin da wuraren ziyara.
T: menene ya hau kan ma'aurata game da rayuwar iyali a mahangar musulunci?
A: ciyarwa cikakkiya tana kan namiji da kuma biyan bukatar mace ta jiki, amma ita kuwa ya hau kanta kada ta fita daga gida sai da izinin mijinta, kuma ta bi shi a cikin abin da ya shafi biyan bukatarsa ta sha'awa. Amma al'amuran da suka shafi gida to ba wajibi ba ne a kan mace sai dai an so mata wannan domin kare taimakekeniya tsakninsu, sannan musulunci ya sanya aure ba ya kulluwa sai da yardar su biyu, amma saki ya sanya shi a hannun miji saboda maslahar zamantakewar tare, sai dai idan yayin aure an shardanta cewa saki yana hannunta.
T: menene ra'ayin musulunci game da auren mace fiye da daya?
A: musulunci yana ganin halaccin auren mata har hudu a aure na da'imi, sai dai da sharadin adalci tsakninsu, da wannan ne musulunci ya warware matsalar mata marasa aure da zaurawa, kuma abin da aka sani a cikin al'umma wanda ya tabbata a ilmance shi ne cewa; mata sun fi maza yawa, idan da babu wannan doka, to wannan yana nufin mata da yawa su zama ba su da ma'aurata.

1. Kafi, mujalladi 2, shafi: 17.
2. Daha: 125.
3. Ba laifi a kafa kungiyoyin da suke raya kasa matukar ba su sabawa shari'a ba.
4. Kamar humusi da zakka d.s.s.
5. Da sharadin kada wasu su cinye hakkin wasu.
6. Da yawa an samu kasashe da saka sam fama da talauci sakamakon yawan albashin ma'aikata da suke fada da shi, sai suka samu warware matsalar da ci gabata ta hanyar rage ma'aikata, karancin ma'aikata yana daga cikin abin da musulunci ya kwadaitar da shi, amma abin takaici wasu kasashe suna amfani da wannan yayin da musulmi suka yi jifa da shi.
7. Kamar ciniki na halal, ko sharadi cikin ciniki.
8. Littafin Addamanul ijtima'I fil islam, na Ayatul-Lahi Sayyid Sayyid Ja'afar Sadik shiraz.
9. Tafsiri nurus sakalain: mujalladi 4, shafi: 240.
10. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 13, shafi: 151.
11. Mustadrikul wasa'il, mujalladi 2, shafi: 490.
12. Mustadrikul wasa'il, mujalladi 4, shafi: 490.
13. Mustadrikul wasa'il, mujalladi 4, shafi: 492.
14. Wasa'ilus Shi'a.
15. Biharul anwar, mujalladi 32, shafi: 214. Da Mustadrikul wasa'il, mujalladi 17, shafi: 446.
16. Manla yahaduruhul fakih, mujalladi 4, shafi: 100.
17. Aiwatar da wannan yana hannun majalisar shura.
18. Abin da ya kamata tarbiyyantar da yara da manya duka kan wannan.
19. Ya kamata han dan Adam kera makamin kare dangi wacce take cutar da dan Adam, don ya zo a hadisi cewa: "Babu cutuwa babu cutarwa". Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 17, shafi: 376, babi 1, hadisi 11.
20. Anfali: 60.
21. Bakara: 208.
22. Anfali: 61.
23. Tahzibul ahkam: mujalladi 7, shafi: 152, hadisi 22.
24. Wani daga masu tabligin musulunci ya ziyarci wata kasa ta turai sai ya ga sun warware matsalar gidajen zama ta hanyar gina su da tsara komai a kowane yanki na abin da ake bukata na makaranta da kasuwa da laburare, da wajen wasa, da asibiti da wajen iyon ruwa, da kuma wajen hutawa da kemis da duk wani abu da ake bukata, wanda tsari ne da musulunci ya zo da shi, sai su gina su sayar da gidajen da kudi mai arha ga al'umma: da haka ne suka warware matsalar mazauni, da matsugunin al'umma. Ya ce: wannan ne aikin injiniyoyinsu dare da rana.
25. Shekaru hamsin da suka gabata duk wannan ana yin sa a gidan malami daya a cikin gari, kuma sitam dinsa ba yadda za a yi wani ya iya yin na jabu.
26. Biharul anwar, mujalladi 1, shafi: 171, babi 1, hadisi 23, da sauran littattafai masu yawa.
27. Bakara: 208.
28. Anfal: 61.
29. Ahzab: 53.
30. Duk da kuwa bai hana ta aikin waje ba bisa sharudda.