Rayuwarsa

Rayuwar Ayatullahi Mai Girma Sayyid Sadik Shirazi Allah Ya Ja Zamaninsa
Ta Wata Mahanga
Ayatullah mai girma Sayyid Sadik Shirazi an haife shi a Karbala a hijira 20 Julhajji 1360. kuma ya karanta ilimin addini wajan manyan malamai na hauza har ya samu darajar ijtihadi.
Malamansa sun yaba shi a matsayin malami masanin fikihu da usul da kuma ilmin hankali da na nakali kuma mai takawa da zuhudu da tsentseni da kyawawan halaye.
Ya taso a gidan ilimi da takawa na mujaddadi Shirazi (R.A) kuma ya girma da ilimi da ijtihadi a ilimomin musulunci.
Shi yana da alaka mai karfi da manyan malamai maraji'ai da kuma manyan mutane ma'abota addini da kuma tattaunawa tare da su a fagage daban-daban da mas'alolin ilimi komai kuwa kankantar alakarsu da al'amuran shi'ar duniya kuma ya shahara da wannan.
Yana da littattafai masu yawa daban-daban kuma da suka dace da mutane masu mustawa daban-daban kuma wannan yana daga cikin abin da ya kebanta da shi wadanda daga karshe zamu kawo su a nan.
Kuma yana da bahasosi da yake yi wa malamai da mujtahidai da darussa a fikihu da usul da dalili na ilimi da zurfafawa da kuma hanya mai karfi mai kyau da kayatarwa ta ilimi.
Kuma sama da shekaru 20 kenan manyan malamai da masana da masu ilimi suke halartar bahasinsa na "bahasul khariji" kuma da yawa daga manyan malamai da suke a kasashe kamar birnin Kum da Siriya da masu tabligi a yankunan duniya daban-daban duk daga dalibansa ne.

Girma Da Tasowa

Ayatullahi mai girma Sayyid Sadik Husaini Shirazi yana daga jikokin Zaid bn Ali bin Husain bn Ali (A.S) ne.
Kuma shi yana daga gidan da aka san su da ilimi da marja'anci a tsawon shekaru dari da hamsin na wannan zamanin wadanda zamu yin nuni da wasunsu kamar haka:
1 Marja'in duniya na shi'a Ayatullahi mai girma Haji Sayyid Muhammad Hasan Shirazi wanda aka san shi da mujaddaddi Shirazi mai juyin nan na Tambako (al'amarin nan da ya shafi tabar kamfanin faransa) da ya shahara a Iran (a wancan lokacin), wanda ya mutu a shekara ta 1312 hijira kamariyya.
2 Marja'in addini Ayatullahi mai girma mirza Muhammad taki Shirazi shugaban juyin nan na 1920 miladiyya a Iraki wanda ya rasu a 1338 hijira kamariyya.
3 Mai girma marja'ain Shi'a Ayatullahi mai girma hajji Sayyid Ali Shirazi dan mujaddadi Shirazi daga manyan malaman Shi'a a Najaf wanda ya rasu a 1355 hijira kamariyya.
4 Ayatullahi mai girma Sayyid Isma'ila Shirazi wanda ya rasu a shekara ta 1305 hijira kamariyya.
5 Mai girma marja'in shi'ar duniya Ayatullahi mai girma Sayyid Abdulhadi Shirazi wanda ya rasu a watan safar 11 1382 hijira kamariyya.
6 Mai girma Ayatullahi mai girma Sayyid mirza Mahadi Shirazi daga manyan marja'an Shi'a a Karbala wanda ya mutu a 28 ga sha'aban shekara ta 1380 hijira kamariyya.
7 Marja'in duniya na Shi'a mai girma Ayatul-lahi mai girma Sayyid Muhammad Husain Shirazi dan'uwan Ayatullahi mai girma Sayyid Sadik Husain Shirazi wanda ya rasu a shawwala 2 1422.
8 Ayatullahi shahid Sayyid Hasan Shirazi dan'uwansa mai assasa hauzar nan ta ilimi a gefen kabarin (haramin nan) na sayyida Zainba Kubura (A.S) a 16/jimada2/shekarar 1400 hijira kamariyya a birnin Bairut, kuma an kashe shi ne kuma ya yi shahada ta hannun kuniyar Ba'as ta Saddam shugaban Iraki.

Malamansa

Ayatullahi mai girma Sayyid Sadik Husaini Shirazi an haife shi a Karbala a 20 ga watan zulhajji 1360, kuma ya yi karatu a matakai masu yawa daban-daban a hannun manya malaman hauza da maraji'ai a hauzar Karbala. Har ya samu darajar nan ta ijtihadi, daga cikin malamansa akwai:
1 Babansa Ayatullahi Mirza Mahadi Husaini Shirazi.
2 Dan'uwansa Ayatullahi mai girma Haji Sayyid Muhammad Husaini Shirazi.
3 Ayatullahi mai girma Sayyid Hadi milani.
4 Ayatullahi mai girma sheikh Muhammad Rida Isfahani.
5 Ayatullahi sheikh Muhammad shahrudi.
6 Ayatullahi Haji sheikh Muhammad Sadiki Mazandarani.
7 Ayatullahi Haji sheikh Ja'afar Rashti.
8 Ayatullahi Sayyid Kazim Madrasi.
Da kuma sauran malamai masu girma na hauzar Karbala da Najaf madaukakiya.

Mu'assasoshi

Daga cikin abin da ya himmantau da shi, shi ne kokarin muhimmantar da al'amarin mu'assaso-shin addini da mutane, da kuma al'adu da kuma hidima da taimakon jama'a, da kafa da yawa daga kungiyoyin addini da Husainiyyoyi da masallatai da makarantu da laburarruka, da kuma gidan buga littattafai da wajen shan magani da sauransu ta hanyar shiryarwarsa, da kuma sauran ayyuka.

Tarbiyyantarwa

Mai girma shi mutum ne na ilimi da kyawawan halaye da tarbiyya ta ilimi da kuma kyawawan halayen dalibai da malamai da muhimmantar-wa mai girma. Ta yadda darussansa na kyawawan halaye sun samu karbuwa mai fadi mai yawa a Iraki da Kuwet da Iran a wajen mutane masu yawa da manyan malamai, da kuma amfanuwa daga wadannan darussa nasa na kyawawan dabi'u, kuma an buga darussan nasa masu yawa a matsayin jazawa ko littattafai da aka buga a lokuta masu yawa.

Kyawawan Halaye

Kyawawan halayen musulunci suna daga cikin abubuwan da suka kawata shakhsiyyar daukakar ilimi na wannan malami mai girma a cikin shekaru 50. kuma duk wani mutum da ya zauna ya yi rayuwa tare da shi to zai ga wadannan kyawawan halaye na 'yan'adamtaka da kyawawan halayen mutane masu daraja da sakin fuska da yake da shi zasu kasance farkon halaye da zasu iya jan hankalinsa zuwa gareshi.
Yana da nisanta daga kyalekyalin duniya da kuma takawa da tsentseni da dogaro ga Allah da kaskan da kai mai yawa ga mutane, da kuma kyawawan halaye da girmama babba da karami, da hakuri, da dagewa, da tabbatar dugadugai, da kuma tsayawa kyam kan tafarki madaidaci, da kuma juriya mai yawa ga matsaloli da suke fuskantar shi a tafarkin daukaka kalmar dan Adam ta gaskiya, da kuma yada ilimi na ilimi da al'adu da wayewar Ahlul Bait (A.S), da aminci da kaunar juna saboda Allah, da kuma hidima ga mutane da zama tare da su, da kuma yi wa kai hisabi da yake da shi, kuma duk abin da zai yi umarni da shi yana fara aikatawa sannan sai ya kira wasu da su aikata shi.

Wallafe Wallafensa

Ya fara wallafa littattafai tun yana da shekarun samartaka kuma har zuwa yanzu yana bin wannan, kuma ya yi rubutu a ilimomi daban-daban kamar fikihu, da usul, da akida, da al'adun musulunci, da tarihi, don haka a nan zamu kawo wasu daga talifofinsa kamar haka:
-Sharhin Urwatul Wuska: an rubuta shi a mujalladai wanda na farko ya kunshi babin ijtihadi da takalidi (koyi da biyayya ga fatawar mujtahidi) mujalladi na farko yana da mas'aloli 72 ne da ya kunshi babin ijtihadi da takalidi, kuma yana da shafi 700, kuma an buga shi a Labanon, wannan littafin yana daga littattafan da ya rubuta su a Karbala, kuma bayan kokkoma masa da kare-kare ya koma kusan shafi 1000 yanzu da yake za a buga shi.
-Bayanil usul (mujalladi goma): hudu daga ciki game da babin ka'idar nan ta babu cuta babu cutarwa da kuma istishabi kuma an buga shi. Wannan littafi ne na bahasin ilmi mai zurfi da kuma kafa dalili da bayanai dalla dalla a cikin ilimin usul, kuma yana daga wallafarsa da ya yi a garin Kum, kuma zuwa yanzu an buga shi a marhaloli masu yawa, kuma karhsen bugunsa shi ne na shekarar hijira kamariyya 1424 a Kum.
-Taudihi shara'i'ul islam mujalladi hudu: sharhi ne na bayani kan littafin nan na shara'i'ul islam wanda muhakkikul hilli ya wallafa, wanda yake da ta'aliki masu yawa (sama da dubunnai) da bayanai a fagage daban-daban na fikihu tun daga ibadoji, da mu'amaloli (kamar cinikayya) da sauransu. wannan littafi ya ja hankalin masu karatu a hauza da jami'a kuma saudayawa akan sanya (an ayyana) shi a matsayin littafin darasi.
-Sharhin tabsiratul muta'allimin (mujalladi biyu) a cikin hukunce-hukuncen addini na Allama Hilli kuma a game da babobi daban-daban yake na fakihu tun daga tsarki har zuwa diyya.
Mujalladi na farko an rubuta shi ne a Karbala da tarihin shekara 1382, wanda ya ke da shafi 468 kuma an buga shi, amma mujalladi na biyu yana da shafuka 534 ne wanda zuwa yanzu an buga shi saudayawa, kuma da farko an buga shi a Najaf ne a shekara 1382 hijara kamariyya.
-Sharhin littafin suyudi (mujalladi biyu): sharhi ne na ta'aliki a game da littafin "albahajatul mardiyya fi sharhil alfiyya" wallafar suyudi, kuma wannan littafi ne na ilimi da darasin hauza kuma yana daga littattafan da ya wallafa a Karbala a 15 sha'aban 1386 hijira kamariyya, mujalladi na farko yana da shafuka 454, kuma mujalladi na biyu yana da shafuka 444, kuma saboda karbarsa da yawa da dalibai suka yi ne aka buga shi a lokuta masu yawa.
-Sharhin lum'a demishkiyya (mujalladi goma): sharhi ne wanda yake hadadde cikakke na luma' wacce take wallafar shahidus sani ne kuma daga mafi muhimmancin littafin darasi na hauza wanda za a buga shi nan gaba kadan.
-Takaitaccen mantik: wanda yake game da asasin ilimin mantik da bayani mai sauki dalla-dalla, kuma ya zama wani bangare na koyarwa a wasu hauzozi. Wannan littafin ya wallafa shi ne a Karbala a 2 Muharram 1384 hijira kamariyya.

Littattafan Akida:

Daga littattafai masu muhimmanci wajen kare mazhabar Ahlul Bait (A.S) akwai wasu littattafai na wannan malami kuma marja'I mai daraja da ya rubuta su da zamu yi nuni da su a nan:
Ali (A.S) a Kur'ani (mujalladi biyu): ayoyi ne guda 711 na kur'ani mai girma game da bayanin falala da girman imam Ali (A.S) dan Abu Dalib, da suka sauka game da falalolinsa da aka dauko daga littattafan Ahlussunna wanda ya fara tun daga Fatiha har zuwa surar ikhlas, kuma ya hada shi a garin Karbala, mujalladi na farko yana da shafuka 404, na biyu kuma yana da shafuka 528, kuma bugun karshe ya kasnce an buga shi a Bairut ne Labanon a Darul ulum.
-Fadima Zahra (A.S) a Kur'ani: wanda yake dauke kuma kunshe da wasu bayanai game da sayyida Zahara (A.S) daga littattafan Ahlussu-nna da ya rubuta shi a birnin Kum a ranar 17 Rajab 1408, wannan littafi yana da shafuka 360, kuma an buga shi a lokuta masu yawa.
-Ahlul Bait (A.S) a Kur'ani: wannan ma yana kunshe da matsayi mai girma na Ahlul Bait (A.S) ne, kuma an ciro shi daga littattafan Ahlussunna tun daga Fatiha har zuwa surar Kausar a gomomin ayoyi masu albarka, kuma an rubuta shi a Kuwet ne da yake da shafuka 407.
-Shi'a a Kur'ani: wannan ma an rubuta shi da kunshe da bayanai daga ayoyin kur'ani da suka yi magana game da shi'ar Ali dan Abu Dalib (A.S) wanda wannan malami mai girma da daraja madaukakiya ya hada duk abin da aka fada game da sha'anin saukar aya ko tawilinta ko tafsirinta daga littattafan Ahlussunna.
-Imam Mahadi (A.S) a littattafan Ahlussunna: wannan littafin yana kunshe da wasu ruwayoyi masu yawa game da imam Mahadi (A.S) da aka karbo daga Manzon Allah (S.A.W) a littattafan Ahlussunna, kuma ya rubuta shi a Karbala, yana da shafuka 126, kuma an buga shi a lokuta masu yawa, kuma bugun fakro ya kasance a shekara ta 1400 ne hijira a mu'assassar alwafa ta Labanon, a Bairut.
-Haka'ik anish Shi'a: wannan littafin ya rubuta shi domin tabbatar da akidu na Shi'a da kuma kore wasu shubuhohi da makiya suke jifan mazhabar Ahlul Bait (A.S) da su ne. kuma an rubuta su da bayani mai fadi mai kyau dalla-dalla.
Wannan littafin ya rubuta shi ne a Karbala da shafuka 80 kuma an buga shi a lokuta daban-daban.

Littattafan Al'adun Musulunci:

A wannan bangare zamu kawo wasu daga littattafan da suka shafi tunani da shiryarwa ga al'ummar musulmi ne da ya rubuta su.
-Kiyasi a shari'ar musulunci: wannan littafin an yi bincike ne a cikinsa mai zurfi game da mas'alar nan ce mai muhimmanci ta kiyasi da hukuncinsa a shari'ar musulunci, kuma ya rubuta shi a Karbala ne.
-Matsayin sallar jam'i a musulunci: wannan littafin yana kushe da hadisai ne madaukaka game da falalar sallar jam'i da kuma bayanin hikima da hukunce-hukuncenta, kuma ya rubuta shi a Kuwet ne.
-Azumi: wannan yana bayani game da hikimar azumi da hukunce-hukuncensa ne wanda aka rubuta shi cikin sauki, kuma ya rubuta shi ne a Karbala, da kuma garin Najaf mai girma da daraja.
Hajji:
Mukaddimomi game da tattalin arzikin musulunci: wannan littafi ne da aka buga shi a Kuwet.
-Tattalin arziki da matsalar riba: wannan littafi ne da yake bayanin munin riba a tattalin arzikin duniya da kuma hanyoyin warwareta wanda aka buga shi a Kuwet.
-Siyasa a mahangar musulunci: wannan yana bayanin mecece siyasa a musulunci, kuma da bayinin siyasar Manzon Allah (S.A.W) da ta imam Ali (A.S) da sauran imamai (A.S) game da mas'alolin siyasa, kuma an yi bayani a wannan littafi da ya rubuta shi a Karbala, kuma yana da shafuka 414, ne kuma daga karshe an buga shi a Darul ulumi.
-Giya da al'umma: wannan yana bayanin munin giya da barnarta a cikin al'umma ne, kuma ya rubuta wannan littafin a Karbala, sannan kuma an buga shi a lokuta masu yawa a Najaf da Kum.
-Munin rashin sanya hijabi: wannan ma yana bayani game da hijabi da matsalolin rashin sanya shi da barnar rashin sanya hijabi, kuma ya rubuta shi a Karbala ne.
Kissoshi masu darussa: wannan littafi ne da ya tattara wasu labaru da kissoshi masu koyarwa masu hadafi, kuma ya rubuta shi a karbala, an buga shi a Najaf a shekara ta 1378 hijira kamariyya.
-Haddodi a musulunci: wannan yana bayanin hikimar haddi a musulunci da bayanin sharudda da hukunce-hukuncensa, kuma ya rubuta shi a Karbala ne, kuma an buga shi a Bairut.
-Tafarki zuwa ga bankin musulunci: wannan littafi ne da aka yi kokarin bayani cikakke da warwarewa game da bankin musulunci, da mas'aloli da kuma batun matsalar dauke riba daga tsarin banki, kuma da bayanin mas'aloli da ayyuka muhimmai na bankin musulunci a nazarin ra'ayin karshe da ake da shi kan dokar tattalin arziki na duniya, kuma yana da shafuka 104, kuma an wallafa shi a Karbala a shekara ta 1392, kuma Darus Sadik suka buga shi a shekara ta 1972 a Labanon.

Mazaje da shahsiyyoyi masu kima:

-Maliku ashtar nakha'i: wannan littafi yana kunshe da bayanin kwamandar musulunci Malik ashatar nakha'I, kuma ya rubuta shi ne a Karbala, kuma an buga shi a Najaf a shekara ta 1387 hijira a gidan buga littattafai na "Algariyyil hadisa".
-Shahidi na farko: wannan littafin yana bayani takaitacce game da shahid awwal "shahidi na farko" sheikh shamsuddin Abu Abdullahi Muhammad dan Jamaluddin Makki, dan Shamsuddin Muhammad Madlabi Demishki Amuli Jazini Hamdani, wannan littafin an rubuta shi a karbala kuma an buga shi a Najaf.
-Shahid na biyu: shi ma bayani ne game da shahidi na biyu " shahid sani " wanda yake shi ne sheikh Zainuddin Ali dan Ahmad Aljabal Amuli, kuma ya rubuta shi a karbala, kuma an buga shi a Najaf mai tsarki.
-Uba "Pedar": wannan littafin littafi ne na da yake bayanin rayuwar Ayatullahi Haji Sayyid Mirza Mahadi Shirazi kuma an rubuta shi ne saboda juyayin tunawa da shekaru arba'in da wafatinsa.
Muna iya tuni da cewa wasu daga littattafansa da muka ambata an fassara su da yarurruka kamar; Farsi, da Ingilishi, da Urdu, da Hausa, da Azari, da Kurdi, da Bangali, da Suwahili, da Indiyanci, da kuma wasu yarurrukan.

Shaidar Ijtiahdinsa Da Marja'ancinsa

Izinin ijtihadi da kuma marja'anci da Ayatullahi mai girma Sayyid Sadik Husaini Shirazi ya samu na halaccin takalidi da shi daga marigayi Ayatullahi mai girma Haji Sayyid Muhammad Husaini Shirazi.
((Fassarar Matanin))
Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jin Kai
Godiya tatabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da aminci su tabbata ga Muhammad da alayensa tsarkaka (A.S).
Bayan haka: tabbas mai girma Ayatullahi Sayyid Sadik shrazi Allah ya ja zamaninsa ya kai matsayi babba na ijtihadi kamar yadda na sani, kuma ya kai kololuwar matsayi na takawa da adalci, kuma yana da matsayi da ya dace na ya bayar da fatawa kuma a yi koyi da shi, kuma na sani yana da duk wani abu da malami mai adalci yake da shi.
Don haka ne yin takalidi (koyi) da shi ka koma masa wajen mas'alolin da aka shardantakoma wa marja'i mai adalci ya halatta, kuma ni ina yi masa wasiyya da takawa da kuma kiyayewa al'amuran da suke su ne hanyar tsira a dukkan yanayoyi da halaye, kamar yadda kuma ina nasiha ga dukkan 'yan'uwa da suka taru a nan da su amfana a kowane fage daga gareshi. Ubangiji shi ne mai datarwa mai shiryarwa, kuma shi kadai ne mai taimako.
Muhammad Shirazi
Watan Mihir mai albarka

Halaccin Wanzuwa Kan Takalidi Da Marigayi

Fatawar Ayatullahi mai girma Haji Sayyid Sadik Husaini Shirazi na halarcin wanzuwa kan takalidi (koyi) da mamaci marigayi Ayatullahi Haji Sayyid Muhammad Husaini Shirazi.
((Fassarar Matanin))
Da Sunan Allah
Mai daraja Ayatullahi mai girma Haji Sayyid Sadik Shirazi
Assalamu alaikum warahmatul-Lahi wa barakatuh
Duba zuwa ga alakar mas'alar wanzuwa kan takalidi (koyi) da mamaci, muna neman wani bayani ga masu takalidi da marigayi mai girma Ayatullahi Sayyid Muhammad Husaini Shirazi.
Mun gode
Wasu daga masu takalidi da marigayin
Uku ga shawwal 1422
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Wanzuwa kan takalidi da shi Allah ya ji kansa ya halatta.
Sadik Husaini Shirazi

Sayet din Ayatullahi mai girma Sayyid Sadik Shirazi Allah ya kara masa tsawon rayuwa
1. Amsa tambayoyin shari'a
2. Darussan bahasul hariji (marhala ta koli) na fikihu da usul da kuma laccocin kyawawan halaye
3. Yada labarai da kuma shiryarwa (nasihohi)
4. Laburare
5. Saututtuka