Samarra

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Ina Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!

Harin rashin tausayi da 'yan mamaya masu wuce gona da iri suka kai wa al'ummar garin Samarra (na kasar Iraki) da kuma keta hurumin haramin Imam al-Hadi da Askari (a.s) masu tsarki da ya yi sanadiyyar kashe sama da mutane 50 da suka hada da maza, mata, kananan yara da kuma raunana wasu da dama abu ne mai tada hankali.
A wannan karon ma, 'yan mamayan ma'abuta girman kai sun sake tabbatar da cewa ba su damu da rayukan al'umma ko kuma wuraren masu tsarkinsu ba, suna so ne su yi amfani da karfi da tursasawa. Wawayen 'yan siyasar Amurka ma'abuta girman kai suna rudin kansu da tunanin cewa zasu iya sanya al'ummar Iraki ma'abuta imani da daukaka su mika musu kai da karfin cin tuwo. To sai dai babu shakka wannan wauta da jahilci na su shi ne zai kawo karshensu ba da jimawa ba.
Ina mika sakon ta'aziyyata ga Imam Mahdi (a.s), al'ummar musulmi musamman al'ummar Iraki da ake zalunta da kuma makarantun Hawzah sannan kuma ina rokon Allah Madaukakin Sarki da ya ba wa Musulunci da musulmi nasara (akan abokan gabansu) da kuma rokonSa da ya kare su daga sharrin 'yan mamaya masu wuce gona da iri.

Ina Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!

A wani karon ma na biyu na bayan nan da ya gudana, hannayen makirai (makiya) masu son haifar da fitina sun sake nufo al'ummar musulmi da kuma aikata irin wannan danyen aiki.
Hakika wannan danyen aiki na tada bama-bamai a haramin Samarra da keta hurumin hubbaren Imamain al-Askariyayn (Imam al-Hadi da Askari) amincin Allah Ya tabbata a gare su ba wai kawai zukatan 'yan shi'a ne ya sosa ba face dai dukkanin al'ummar musulmi masoya zuriyar Ma'aikin Allah (s). Wannan wani makirci ne ga duniyar Musulmi da manufar hakan ita ce haifar da yakin basasa a kasar Iraki da fitinar mazhaba da rarrabuwa tsakanin Musulmi.
Ko shakka babu kungiyoyin leken asirin 'yan mamaya da yahudawan sahyoniya su ne suka tsara wannan danyen aiki ko da kuwa sauran gyauron 'yan jam'iyyar Ba'ath na Saddam (Husain) ne ko kuma 'yan kungiyar wahabiyawa ko Salafawa wadanda aka ruda ne suka aikata sahihi a zahiri.
A kokarin da suke yi na cin kafafun gwamnatin da al'ummar (Iraki) suka zaba da kuma samar wa mamayan da suke yi halalci ya sanya 'yan mamayan share hanya ga 'yan ta'adda wajen aiwatar da ayyukan ta'addancinsu da rura wutar fitina tsakanin musulmi.
Shekara da shekaru wannan harami mai tsarki ya yi a garin Samarra tsakankanin 'yan Ahlussunna, babu wani lokaci da wani ya taba keta hurumin wannan waje mai tsarki. Amma a halin yanzu a lokacin 'yan mamaya wannan shi ne karo na biyu da aka aikata wannan danyen aiki ga wannan waje mai tsarki. Babu yadda 'yan mamaya za su iya wanke kansu daga wannan danyen aiki.
Don haka dole ne 'yan'uwa 'yan Ahlussunna da 'yan Shi'a su yi hankali kada su fada tarkon wannan makirci na makiya. Dole ne dukkan al'ummar Musulmi a duk inda suke a duniyar Musulmi su yi taka tsantsan kan wannan bakar siyasa ta rarraba kansu da makiya suke gudanarwa.
A halin yanzu a kasashen Iraki, Palastinu, Labanon da sauran kasashen musulmi makiya na nan na kokarin haifar da fitina da rikici na mazhaba, kabilanci da kungiyanci tsakanin Musulmi da kokarin sanya su fada tsakaninsu. Bai kamata musulmi su taimaka musu wajen cimma wannan bakar manufa tasu ba.
Dole ne malaman Ahlusunna su yi Allah wadai da wannan danyen aiki da barranta daga wadanda suka aikata wannan danyen aiki, su kuma malaman Shi'a dole ne su kirayi mabiya Ahlulbaiti (a.s) da su kwantar da hankulansu, dukkanin malaman musulmi su kirayi mabiyansu zuwa ga so da kaunar sauran 'yan'uwansu.
Ina taya mai girma Baqiyatullah, rayukanmu su zamanto fansa gare shi, juyayin wannan babbar musiba da sauran musibun al'ummar musulmi.
Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya kare al'ummar musulmi daga sharrin azzalumai ma'abuta girman kai da kafiran duniya.

Ina Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!!

Musulmi a duk inda suke a duniya sun girgiza, hankalinsu ya tashi, sun shiga cikin rudani da rashin sanin dalilin sake kai wa masallacin da ke Samarra hari ranar Laraba 13/6/2007, muhallin da aka rufe Jikokin Manzon Allah (S) biyu, Imam Ali al-Hadi da Imam Hasan Askari. Wannan shi ne hari na biyu a cikin watannin 15.
Duk da yake wannan masallacin yana da tsohon tarihi da kuma matsayi a wajen al’ummar Musulmi, amma ya samu daukaka ne sakamakon zamowarsa makwancin Imaman Shiriya na 10 da 11 - Imam al-Hadi da ya rasu a 868, da Imam Hasan Hasan Askari da ya rasu 874 (AS). Kamar yadda kuma wajen yake kusa da inda Imami na 12, Imam Muhammad Mahdi ya shiga gaiba, kuma da da jikan Imaman da ke kwance a wajen.
Kodayake ran al’ummar Musulmi ya baci sakamakon harin kamar yadda wadanda suka kai shi suka so, amma abin farin ciki da yawansu hankalinsu bai bace ba, sun kalli abin da ya faru da idon basira, cikin tsanaki suka dora alhakin harin a wuyan wadanda ya kamata. Sai dai duk da haka wasu da ba a rasa ba, sun ce wasu Musulmi ne.
Gidan talabijin din AL-ALAM ya nuna yadda musulmi a sassa daban-daban na duniya suka nuna fusatarsu da tagawayen hare-haren da suka lalata hasumiyar zinaren da aka lalata a shekarar da ta gabata sakamakon wani hari makamancin wannan da aka kai a wajen.
’Yan mintoci bayan kai harin, Amurka da gwamnati Iraki, karkashin Nouri al-Maliki suna yi wuf sun dora alhakin harin a kan Musulmi masu tsattsauran ra’ayin addinin Musulunci, ko kuma Alka’ida. Suka ce harin ’yan ta’addan Alka’ida ne. Sun ce maharan sun kai hari wajen ‘ibadar ’yan Shi’a’ ne, don su kawo rigama a tsakanin al’ummar kasar.
Sai dai a sarari yake cewa wadanda suka kai wannan harin sun kai shi ne da niyyar kara harzuka al’ummar Iraki da suka jima suna tare da juna.
Kamar yadda aka kai wannan harin, haka kuma suka kai hari wasu masallatai uku da suka ce na Ahlus Sunna ne. Lokaci da yanayin da aka kai harin da ma makaman da aka yi amfani da su iri daya ne, wanda ke kara tabbatar da cewa maharin ‘masallacin ’yan Shi’a,’ shi ne kuma maharin ‘masallacin ’yan Sunna.’
Wani da aka yi hira da shi a gidan talabijin din AL-ALAM ya bayyana cewa an kai wannan harin ne domin a dakushe sabon shirin da Sayyid Mukhtada Sadr ya zo da shi na hada kan ’yan Shi’a da Sunna waje daya don fuskantar masu mamaya.
Kuma alamu sun nuna wannan shirin na Shehin Malamin ya fara aiki, don kuwa kamar yadda rahotanni suke fitowa, jama’ar Iraki sun fara dawowa daga rigimar da ake ta neman dasawa a tsakaninsu. Hatta kafofin yada labaran Yammacin sun ce wannan harin da aka kai bai yi tasirin haifar da rigima a tsakanin jama’ar kasar ba kamar yadda ya faru a baya.
’Yan sanda sun ce: wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun kai hare-hare a wasu masallatai shida na Ahlus Sunna da suka hada da al-Mustafa, al-Ashrah, al-Mubashra, Huteen da al-Bashir Mosque a kudancin Bagadaza da Basra.
Wani magidanci a Bagadaza, Malam Noor ya shaida wa gidan talabijin na Aljazeera cewa, “Ba na zargin Ahlus Sunna da laifin kai wannan harin. Domin Sunna suna girmama wurare masu tsarki na Shi’a, musamman ma da yake Samarra ma yankin Sunna ne.”
Da yawan mutanen da aka zanta da su a Iraki sun yarda, kuma sun amince da bayanin da Sayyid Mukhtada Sadr ya yi na cewa duk wata tuhuma game da wannan harin yana wuyan Amurka, “Duk abin da aka yi a birinin Samarra yana wuyan masu mamaya ne, wato Amurka. Lokacin da aka kai hari a wannan wajen a baya Amurka shiru ta yi, sun bar ayyukan ta’addanci na ci gaba da bunkasa. Don haka a sarari ko a fakaice su ke da alhakin kai wannan harin.”
Shi kuwa Malam Ahmad, wani magidanci a Karbala cewa ya yi, “ina ganin wadannan mutanen masu ilimi ne, kuma suna kokarin ganin sun raba kan al’ummar Shi’a da Sunna ne a Iraki.”
Shi ma wani mai magana da yawun Sayyid Mukhda Sadr, ya tabbatar da cewa manufar kai wannan harin shi ne a sake hada Irakawa rigima a tsakaninsu. Ya ce amma su sun ce masu mamaya da kuma gwamnatin Iraki ce a sahun farko na wadanda za a zarga da laifin kai wannan harin.
Don ma su nuna da gaske suke yi, nan da nan ma wasu magoya bayan Sayyid Sadr din 30 da ke cikin Majalisar kasar suka ayyana ficewarsu daga Majalisar.
Duk da yake an kama ’yan sanda da ke gadin tsohon masallacin mai dimbin tarihi ga al’ummar Musulmi, amma da yawan masu zanga-zangar sun zargi Amurka da gwamnatin Nouri al-Maliki ne da sakaci, musamman da yake sune ke da alhakin kula a duk wani wuri a kasar da ke karkashin mamaya.
Jim kadan bayan harin, Nouri al-Maliki ya ce ya gana da Kwamandan Amurka a Iraki, Janar David Petraeus, da Jakadan Amurka Ryan Crocker a game da karin matakan tsaro a Samarra da ke da nisan kilomita 60 daga Bagadaza.
Wani abu ma da yake kara tabbatar da hannun mamaya a wadannan hare-haren shi ne; harin da aka kai wa wasu masallatan da ake kira na Ahlus Sunna a wasu yankuna, duk da dokar hana fitowar jama’a da aka sanya a unguwannin.
Shi ma Shugaban Iran, Dakta Ahmadnajad, a wata ganawa da ya yi da gidan talabijin din kasar game da wannan hari, ya dora alhakinsa kacokaf a kan Amurka. Ya ce sun yi haka ne da nufin kara harzuka jama’ar Iraki su ci gaba da kai wa juna hare-hare. “Masu mamaya sune kawai makiyan Iraki. Don haka kowa yake neman su fice daga kasar. Ko kuma su ayyana wata rana da za su fice daga kasar,” in ji shi.
Yayin zaman makoki na kwanaki uku da Sayyid Mukhtada Sadr ya ayyana, da kuma muzaharar nuna Allah wadai da almajiransa suka yi a Najaf, duk sun nuna a shirye suke su ba da jinainansu don kare wurare masu tsarki da kuma fatattakar masu mamaya.
Wani abin mamaki da wasu manema labarai suka bayyana shi ne; yadda aka kai wannan harin duk da jami’an tsaro na musamman (Federal Protection Service Forces) 60 da kuma ’yan sanda 25 da ke wajen, amma kuma aka iya ratsa su aka kai wannan harin a wajen.
Wani abu da ke kara sa shakku game da maharan da kuma manufar harin shi ne yadda ’yan kwanaki kafin kai shi aka yi kutun-kutun din da aka tashi wasu sojan sa-kai na Jaishu Mahdi da suka tare a wurin suna sa idon kai-komon jama’a a wajen.
An kai harin farko ne a ranar 22 ga Fabarairu 2006, Amurka da wasu kungiyoyi, gami da wasu masu hannu da shuni sun yi alkawarin taimakawa wajen sake gina masallacin, wanda aka gina shi tun a 1905. Sai dai kuma ga shi ba a kammala gyaran ba an sake lalata shi.
Wani masanin harkokin leken asirin ya shaida wa jaridar Jordan Times cewa zai wahala wannan wajen ya tsira daga hare-hare a yanzu da kuma nan gaba, musamman da yake masu mamaya sun ga irin tasirin da harin da aka kai a baya ya jawo wajen neman jefa kasar cikin yakin basasa, (ba don an kai zuciya nesa ba) duk da yake a wannan karon hakarsu ba ta cimma ruwa ba.