Shika-shikan addini


::.

1. Kadaita Allah Madaukaki

::

Allah Madaukaki Da Siffofin Kamala

::

Allah da siffofin jalala

::.

2. Adalcin Allah

::.

3. Annabci (Jakadanci da Wakilinc Ubangiji)

::

Annabin Karshe (S.A.W)

::

Aiko Annabi Mai Daraja (S.A.W)

::

Tafiya (Mutuwa) Mai Zafin Gaske

::

Kur'ani Mu'ujizar Manzo Ce Madawwamiya

::

Falalar Koyon Kur'ani Da Koyar Da Shi

::

Mumini Da Kur'ani

::

Kur'ani Mai Ceto Ne

::

Annabi (S.A.W) Da Kur'ani

::

Ma'abota Kur'ani Da Falalarsu

::

Saurayi Da Kur'ani

::

Masu Dauke (Hardace) Da Kur'ani Da Siffofinsu

::

Masanin Kur'ani Da Ba Ya Aiki Da Shi

::

Karanta Kur'ani A Kodayaushe

::

Wanda Ya Saurari Karatun Kur'ani

::

Surar Fatiha Da Falalarta

::

Wanda Ya Karanta Kur'ani Sai Ya Manta Shi…

::

Daga Ladubban Karanta Kur'ani

::

Kur'ani Alkawarin Allah Ne To Kiyaye Alkawarinsa

::

Tajiri Da Kur'ani

::

Karanta Kur'ani Da Duba Littafin Kur'ani

::

Karanta Kur'ani

::

Bayyana Karatun Kur'ani Da Boye Shi

::

Kur'ani Da Ladubban Karanta Shi Da Kuma Sauraronsa

::.

4. Imamanci (Jagorancin al'umma)

::

'Yar Annabi (S.A.W) Fadima Zahara (A.S)

::

Imami Na Farko Imam Ali (A.S)

::

Imami Na Biyu: Imam Hasan Mujtaba (A.S)

::

Imami Na Uku: Imam Husain Shahidi (A.S)

::

Imami Na Hudu: Imam Ali Sajjad (A.S)

::

Imami Na Biyar: Imam Muhammad Bakir (A.S)

::

Imami Na Shida: Imam Ja'afar Sadik (A.S)

::

Imami Na Bakwai: Imam Musa Kazim (A.S)

::

Imami Na Takwas: Imam Ali Rida (A.S)

::

Imami Na Tara: Imam Muhammad Jawad (A.S)

::

Imami Na Goma; Imam Ali Hadi (A.S)

::

Imami Na Goma Sha Daya: Imam Hasan Askari (A.S)

::

Imami Na Goma Sha Biyu: Imam Mahadi (A.S)

::.

5. Tashin Kiyama (Rayuwa Bayan Mutuwa)


1. Kadaita Allah Madaukaki

Shi ne mutum ya sani cewa yana da mahalicci da ya samar da shi daga rashi kuma a hannunsa akwai komai …halittawa da arzutawa da bayarwa da hanawa da kashewa da rayawa da lafiya da rashin lafiya duk suna hannuna, "kawai al'amarinsa idan ya yi nufin wani abu sai ya ce da shi: kasance sai ya kasance"(1).
Dalilin kuwa samuwar Allah shi ne abin da muka gani na daga sama da abin da yake cikinta na rana mai haske da wata da taurari da gajimare da iska da ruwan sama.
Da kuma kasa da abin da yake cikinta na koguna da koramau da 'ya'yan itaciya da shuke-shuke, da ma'adinai daban-daban kamar zinare da azurfa da zumurrudu da sauransu.
Da kuma nau'o'in dabbobi; tsuntsaye a sama da masu iyo a ruwa da masu tafiya a kan kasa, kala-kala da sauti daban-daban da kuma girma mabambanci.
Da kuma mutum mai ban mamaki da yake dauke da siffofi mabambanta; na ji da gani da shaka da dandano da tabawa, da kuma gabobi masu yawa; kamar kunne da idanu da harshe da zuciya da hannu da kafa da lafiya da rashin lafiya da yarda da fushi da bakin ciki da farin ciki, da sauransu. Dukka wannan dalili ne a kan samuwar Ubangiji mai hikima masani da muke imani da shi muna bauta masa, kuma muna neman taimakonsa kuma muna dogaro da shi.

Allah Madaukaki Da Siffofin Kamala

Allah yana da siffofi masu yawa, kamar haka:
Ilimi: ya san komai babba ne ko karami kuma ya san abin da yake cikin zukata.
Iko: Yana da iko a kan komai akan halittawa da arzutawa dakashewa da rayawa da sauransu.
Da rayuwa: shi rayayye ne ba ya mutuwa.
Nufi: shi mai nufin ne wanda yake ya san maslaha kuma ba ya nufin abin da yake barna ne.
Kuma mai riska ne: shi yana ganin komai yana jin kowane sauti koda kuwa na zuci ne.
Rashin farko: shi kadi yake tun azal kuma har abada, wato shi saramadan yana nan tun faufau tun tuni kafin samuwarkomai sannan sai ya yi halitta kuma yana nan bayan komai kuma dukkan halitta tasa ce mai bukatuwa zuwa gareshi, ba kawai a samuwarsu ba har ma a wanzuwarsu, dukkan abin halittawa shi fararre ne kuma babu wani kadimi maras farko sai Allah.
Magana: shi mai magana ne ga wanda ya so na bayinsa na gari, da kuma annabawansa da mala'ikunsa.
Gaskiya: shi mai gaskiya ne cikin dukkan abin da yake cewa kuma ba ya saba alkawari.
Kamar yadda shi madaukaki ne: mai halittawa, mai arzutawa, kuma mai rayawa, mai bayarwa, mai hanawa, mai rahama, mai jin kai, mai gafara, mabuwayi, madaukaki, mai baiwa …

Allah da siffofin jalala

Allah ya tsarkaka daga dukkan tawaya:
Shi ba jiki ba ne.
Ba mai cin wuri ba ne.
Ba zai yiwu a gan shi ba, ko a duniya ko a lahira.
Ba shi da wajen da masu bujurowa zasu bujuro masa, kamar kishirwa ko yunwa, ko tsufa ko karewa, kuma ba ya gafala ba ya bacci.
Ba shi da abokin tarayya, ba shi da kishiya, shi kadai yake ba shi da mata ko da.
Siffofinsa ainihin zatinsa babu biyuntaka a cikisu tsakaninsu da shi, shi masani ne ta fuskacin da yake mai iko. Siffofinsa na kamala tun azal suke, ba kamar mu ba ne da muke da jahilai sai kuma muka zama masana, kuma dukkaninmu masu gajiyawa sai muka zama masu iko.
Mawadaci ne daga dukkan komai da ga dukkan kowa, ba ya bukatar shawara ko mataimaki ko waziri ko runduna.

2. Adalcin Allah

Yana nufin: Allah adali ne baya zaluntar wani kuma ba ya aikata abin da yake kore hikimar, dukkan halittawa da arzutawa da bayarwa da hanawa dukkansu daga gareshi domin maslaha ne koda kuwa mu ba mu san ta ba, kamar yadda likita idan ya yi magani to sai mu san cewa akwai maslaha koda kuwa bamu san fuskancin maslahar wannan magani ba.
Idan muka ga Allah madaukaki ya wadata bwani ko ya talauta wani, ko ya sanya wani maduakaki wani kuma makaskanci, ko kuma ya sanya rashin lafiya ga wani wani kuwa ba haka ba, to sai mu yi imani da cewa dukkan wannan akwai hikima da gyara da mu ba mu sani ba ne.
Ya zo a cikin hadisi cewa; Musa (A.S) ya nema daga Allah ya nuna masa wani daga cikin adalcinsa, sai Allah ya umarce shi da ya tafi wajen wani idanuwar ruwa a sahara, domin ya ga me zai faru. Yayin da ya fita (A.S) sai ya ga wani mahayin doki ya sauka wajan idanuwan ruwa ya biya bukatarsa sannan sai ya tafi ya manta da kudinsa a wurin sai wani yaro mai datawa ya zo ya ga wannan jakar kudin an yar da ita a wajen idanuwar ruwa, sai ya tsinta ya yi farin ciki ya tafi da sauri ya koma inda ya futo. Sannan sai wani makaho ya zo wajen domin ya yi alwala, sai ya ga mahayin doki ya dawo sai yana binciken jakar kudinsa amma da bai ga jakar ba sai ya tuhumi makaho cewa shi ya dauka kuma suka yi rigima har ta kai ga kashe wannan makahon sannan sai mahanyin ya tafi, sai Annabi Musa (A.S) ya yi mammaki mamaki mai tsanani. Sai Allah ya yi masa wahayin abin da ya kawar da mamakinsa, ya ce da shi: mahayin nan ya taba sacewa baban yaron nan kudi sai muka dawo da su ga magadinsa, shi ne wannan yaron da kake gani, shi kuwa makaho ya taba kashe baban wannan mahayin doki don haka sai ya yi masa kisasi(2).
Wannan shi ne hukunci Allah da adalci duk da a fili ana ganin wannan al'amari kamar yana nesa da doka.

3. Annabci (Jakadanci da Wakilinc Ubangiji)

Yayin da Allah ya halicci mutum ya yin nufin alheri da rabarutar duniya da ni'imar lahira da aljanna gareshi amma wannan duk bai yi samuwa sai idan mutum ya yi amfani da hankalinsa da kuma abin da ya dace da ruhinsa dajikinsa, wannan kuwa yana bukatara abin da zai dauke wadannan bukatu wadanda ba wanda zai iya samar da dukkan wannan sai mahaliccin mutum din da ya san shi kuma ya san bukatunsa.
Tun da Allah yana son rabauta ne ga mutam shi ya sa halicce shi, don haka ne sai ya samar masa da hanya kamila da zai bi domin samun rabatau ta hanyar wasu amintattn bayi nasa da suke ma'asumai daga dukkan kuskere da mantuwa kuma tsarkaka daga dukan aibobi dazubunbai wadannan su ne annabawa da manzanni.
Don haka ne: Annabi shi mutum ne da Allah ya yi masa wahayi ya zabe shi a cikin mutane kuma sun kasu gida biyu:
Annabi dan sako: shi ne wanda aka aiko domin ya tseratar da mutane daga duhu zuwa haske daga barna zuwa gaskiya daga camfi zuwa gaskiya daga jahilic zuwa ilmi.
Annabi ba dan sako ba: shi ne wanda aka yi masa wahayi zuwa ga kansa kuma ba a umarce shi ya isar da sakon ga mutane ba.
Adadin annabawa: 124 000, amma manzanni wato; 'yan sako a cikinsu kadan ne.
Farkon annabawa Adam (A.S) na karshensu kuma Muhammad (S.A.W).
Manzanni sun kasu gida biyu:
Na farko: Ulul Azmi
Na biyu: Wadanda ba Ulul Azmi ba
Ulul Azmi su ne wadanda Allah ya aika su gabashin duniya da yammacinta zuwa ga mutane gaba daya wadanda su biyar ne:
Ibrahim (A.S)
Nuhu (A.S)
Musa (A.S)
Isa (A.S)
Muhammad (S.A.W).
Yahudawa suna bin Annabi Musa (A.S) kiristoci kuma Annabi Isa (A.S) musulmi kuma Muhammad (S.A.W).
Sai dai musulunci ya shafe sauran addinai da suka rigaya, bai halatta ba ma'abotansu su wanzu a kansu, dole ne a kan kowa ne mutum ya bi koyarwar musulucnci. Ubangiji yana cewa: "wanda ya yi riko da wani addini ba musulunci ba to ba za a karba daga gareshi ba, kuma shi a lahira yana daga cikin masu hasara"(3).
Don haka yahudanci da kiristanci barna ne da aka shafe su, amma musulunci mai wanzuwa ne har zuwa ranar kiyama.
Wadanda ba Ulul Azmi ba: su ne wadanda Allah ya aika su wasu kebantattun yankuna na musamman zuwa ga wasu garuruwa ko mutane na daban.

Annabin Karshe (S.A.W)

Ka sani cewa Muhammad (S.A.W) shi ne karshen annabawa kuma addininsa shi ne musulunci mai shafe duk wani addini kuma shari'arsa zata wanzu har zuwa alkyama kuma ita kadai ce shari'ar da zata arzuta mutum da tabbatar masa da burinsa da amincinsa har zuwa karshen rayuwar duniya da lahira. Kamar yadda shi kadai ne mutum abin koyi ga dukkan duniya baki daya, su musulmin da dukkan duniya idan suna son alheri ga kawukansu to dole ne su bi tarfarkinsa su yi koyi da kyawawan halyensa (S.A.W) da kuma sanin sashen tarihinsa da bamakawa mu kawo wasu daga siffofinsa (S.A.W):
Shi ne Muhammad dan Abdullah (S.A.W) kuma babarsa ita ce Aminatu 'yar Wahab. An haife shi a Makka ranar juma'a goma sha bakwai ga watan Rabi'ul awwal bayan bollolwar alfijir a shekarar giwa, a zamanin sarki mai adalci Kisra(4). (wato idan an kwatanta shi da ire-irensa).

Aiko Annabi Mai Daraja (S.A.W)

An aiko Annabi da sako 27 ga Rajab bayan yana dan shekara 40 yayin da Jibrilu ya sauka gareshi daga wajen Allah (S.W.T) yana kogon Hira wanda yake dutse ne a Makka ya ce masa ka karanta kuma ya saukar masa da ayoyi biyar na surar Alaki(5).
Sai ya zo ya tsaya a kan dutsen Safa a masallaci mai alfarma na Makka a lokcin akwai jama'a masu yawa a wurin da ake taruwa ya isar da sakon Allah na shiryar da mutane zuwa ga imani da shi yana cewa da su: "Ku ce babu abin bauta sai Allah kwa rabauta"(6).
A lokacin tunda mutanen Makka mushrikai ne, kuma suna ganin maslaharsu ita ce shirka kuma suna tsoron maslaharsu sai suka rika yi masa isgili suna yi masa dariya suna cutar da shi. Kuma duk sa'adda ya dage wajen shiryar da su sai su dage wajen cutare da shi har yace: "Ba a cutar da wani Annabi ba kamar yadda aka cutar da ni"(7).
Ba wanda suka yi imani da shi sai mutane kalilan, na farkonsu imam Ali sannan sai matarsa Hadiza (A.S) sannan sai wasu mutane.
Farkon wanda ya yi imani da shi daga maza imam Ali sannan daga mata sai Hadiza (A.S).
Yayin da takurarwar mushrikai ta yi yawa sai ya yi hijira zuwa Madina wannan kuwa ita ce hijirar farko a tarihin Muslim, yayin da suka yi yawa sai karfinsu ya dadu kuma suka samu koyarwa daga Manzon Allah da shari'arsa mai sauki mai hikima, da kuma misali na kyawawan halaye da mutumtaka da wayewa da cigaba a Madina har suka fi dukkan duniya da addini na sama da wadanda ba na sama ba.
Kuma an samu yakoki masu yawa a Madina kuma dukkanninsu sun zama domin kare kai ne daga makiyar mushrikai da yahudawa da kiristoci da suke kai hari kan musulmi, kuma Annabi a kowne lokaci yana zabar bangaren sulhu da zaman lafiya ne da rangwame, don haka ne ma adadin wadanda ake kashewa daga bangarorin biyu ba su da yawa a dukkan yakokinsa tamanin da wani abu, wato; wadanda aka kashe na musulmi da kafirai duka ba su kai sama da dubu daya da dari hudu ba.

Tafiya (Mutuwa) Mai Zafin Gaske

Tun lokacin da aka aiko Annabi da sako har ya tafi daga duniya wahayi yana sauka gareshi kuma Jibrilu shi ne ake aiko masa daga wajen Ubangiji (S.W.T) a hankali a hankali har littafin Kur'ani ya ciki a cikin shekaru ishirin da uku, sai Manzo (S.A.W) ya yi umarni da a hada shi kamar yadda yake a yau din nan.
Manzo (S.A.W) ya kasance yana tsara wa musulmi duniyarsu da addininsu, yana sanar da su littafi da hikima kuma yana yi musu bayanin dokokin ibada da biyayya da mu'amala da zamantakewa da siyasa da tattalin arziki da sauransu.
Bayan cikar addini da kafa Ali dan Abu Dalib (A.S) shugaba na al'umma kuma halifa bayan Annabi wannan kuwa ya faru a ranar Gadir ne goma sha takwas ga zulhajji a shekarar hajjin bankwana sai Allah ya saukar da ayar: "A yau ne na kammala muku addininku, na cika ni'imata gareku kuma na yardar muku da musulunci shi ne addini" . Sai Annabi ya yi rashin lafiya mai sauki, sai dai ya yi tsanani har sai da ya hadu da ubangijinsa a 18 ga watan safar na 11H.
Kuma wasiyyinsa halifansa imam Ali (A.S) shi ne ya yi masa wanka da salla da binne shi a dakinsa a Madina inda kabarinsa yake yanzu.
Ya kansace misali ne shi na amana da ikhlasi da gaskiya da cika alkawari da kyawawan halaye, da girma, da kyawawna dabi'u, da baiwa, da ilmi, da hakuri, da rangawame, da afuwa, da saudakntaka, da tsentseni, da takawa, da zuhudu, da baiwa, da adalci, da kaskan da kai, da jihadi.
Jikinsa ya kasance kololuwa wajen kyau da kuma daidaito da dacewa, kuma fuskarsa kamar wata ne mai haske da ya cika, kuma zuciyarsa da ruhinsa sun kai matuka wajen kamala, mafi kamalar halaye da ladabi da dabi'a kuma sunnarsa tana haske kamar rana a tsaka-tsakinta.
Atakaice, ya tattara dukkan wata dabi'a mai kyau da girma da daukaka da kuma ilimi da adalci da takawa da kuma iya tafiyar da al'amura duniya da na lahira, wadanda babu wani da yake da irinsu kuma wani ba shi da irinsu.
Wannan shi ne annabin musulmi kuma wannan shi ne addinin musulunci, kuma addininsa shi ne mafificin addinai, littafinsa shi ne mafifcin littattafai domin shi:"Barna ba ta iya zo masa ta gabansa da ta bayansa, abin saukarwa ne daga mai hikima abin yabo"(9).

Kur'ani Mu'ujizar Manzo Ce Madawwamiya

Kur'ani mu'ujiza ce rayayyiya madawwamiya domin shi littafi ne na sama (saukakke daga Allah) wanda shi kadai ne guda daya wanda Allah ya so ya wanzu cikin kariya daga dadi da ragi da canji duk da yawan masu neman gurbata shi da karya, domin ya kasance kundin tsari dawwamamme ga rayuwar 'yan'Adam har tashin kiyama matukar mutum yana rayuwa a bayan kasa, wannan kuwa saboda abin da yake dauke da shi ne na manyan koyarwa madaukaka wanda aiwatar da su yake samar da rabautar dan Adam da cigabansa.
Kur'ani littafi ne na ilimi da hukunce-hukunce da hakkoki da dokoki da kyawawan halaye daaladubba da siyasa da tattalin arziki kuma shi mu'ujiza ce madawwamaiya kuma shi fasaha ne da ya keta fasahar larabawa masu manya kasidu bakwai da aka rayata su a Ka'aba, ya yi musu kalubale amma suka kasa da zuwa da koda kwatankwacin sura daya ne, sai suka koma suna cire abin da suka rayata a Ka'aba saboda kunya da faduwa kasa warwas da gajiyawarsu a gaban Kur'ani mai girma. Da sun iya zuwa da koda sura daya da ba su dauki makamin yaki ba da zubar da jini wacce ta kashe mutaneensu ta kuma rusa girmmansu, ta kawo musu yunwa da firgici da tsoro da kaskanci.
Wannan Kur'ani shi ne mu'ujiza ne mai game da dukkan abin da yake rabauta da jin dadin rayuwa da alheri da albarka, da yada aminci a duniya, kuma da yawa ruwayoyi sun zo game da falalar saninsa da koyonsa da kiyaye shi da aiki da shi da sauransu na daga abubuwan da suke kwadaitar da himmantuwa da shi, kuma mu a nan zamu yi nuni da wasu daga ciki in Allah ya so.

Falalar Koyon Kur'ani Da Koyar Da Shi

Akwai ruwayoyi masu yawa da suka zo a littafin wasa'il: da zamu kawo wasu a nan don neman albarka da kuma fa'ida(10):
Daga Sa'adul khifaf daga Abu Ja'afar (A.S) ya ce: "ya Sa'ad ku koyi Kur'ani hakika shi zai zo ranar alkiyama cikin mafi kyawun sura da dan Adam yake iya gani (har ya ce): har sai ya je wajen Ubangiji mai izza sai Ubangiji ya kira shi da cewa; ya kai hujjata a duniya kuma zancena mai gaskiya daga kanka ka kuma tambaya za a ba ka, ka nemi ceto za a ba ka, yaya ka ga bayina? Sai ya ce: ya Ubangiji a cikinsu akwai wanda ya kiyaye ni ya kuma hardace ni bai tozartani ba, daga cikinsu kuma akwai wanda ya tozarta ni, ya wulakanta ni, ya karyata ni, kuma ni ne hujjarka a kan halittarka gaba daya.
Sai Allah ya ce: na rantse da grimana da daukakata da kuma daukakar matsayina yau zan saka wa mutane game da kai da mafi kyawun sakamako, kuma zan yi ukuba saboda kai da mai zafin azaba. (har ya ce): sai ka ga mutum daga shi'armu ya zo yana cewa da shi: ba ka san ni ba? Ni ne kura'anin da ya sanya ka rashin baccin dare da kuma wahalar rayuwa, sai ya tafi da shi wajen Ubangiji ya ce: ya Ubangiji! Bawanka wannan ya wahala saboda ni, ya kiyaye ni, ana gaba da shi saboda ni, kuma yana so kuma yana ki saboda ni, sai Ubangiji ya ce: ku shigar da bawana aljannata, ku tufatar da shi kayan ado na aljanna kuma ku sanya masa hular ado, idan aka yi masa haka sai akawoshi wajen Kur'ani sai ya a ce da shi: shin ka yarda da abin da ubangijinka ya yi wa masoyinka? Sai (Kur'ani) ya ce: ya Ubangiji wannan kadan ne, ka dada masa alheri dukkaninsa, sai ya Ubangiji ya ce: na rantse da girmana zan dada masa da shi da wadanda suke tare da shi irinsa abubuwa biyar: (su ne) su samari ne kuma ba zasu taba tsufa ba, kuma masu lafiya ba zasu taba yin rashin lafiya ba, kuma masu wadata ba zasu taba talauci ba, kuma masu farin ciki ba zasu taba bakin ciki ba, masu rayuwa ne ba zasu taba mutuwa ba… hadisi"(11).
Daga Yunus dan Ammar ya ce: Abu Abdullahi (A.S) ya ce: "za a kira mumini a yi masa hisabi, sai Kur'ani ya zo gabansa a sura mafi kyau ya ce: ya Ubangiji ni ne Kur'ani kuma wannan bawanka ne mumini da yake wahalar da kansa da karanta shi kuma yake tsawaita darensa da karanta shi, kuma idannuwansa suke rasa bacci, sai ka yardar da shikamar yadda ya yardar da ni, ya ce: sai Ubangiji madaukaki ya ce: Bawana shimfida damarka, sai ya cika ta da yardar Allah a kuma cika hagunsa da rahamar Allah sannan ya ce: Wannan aljannar ta halatta gareka sai ka karanta ka kuma daukaka idan ya karanta wata aya sai ya dada daraja"(12).

Mumini Da Kur'ani

Daga Abu Abdullahi (A.S) ya ce: "Bai kamata ba mumini ya mutu har sai ya koyi Kur'ani ko ya kasance a kan hanyar koyar da shi(13).
Daga Walidi dan Muslim daga Abdullahi dan Hahi'a daga Musraj, daga Ukuba dan Ammar ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "Allah ba ya azabtar da zuciyar da ta hardace Kur'ani"(14).
Daga Nu'uman dan Sa'ad daga Ali (A.S): Annabi (S.A.W) ya ce: mafificinku wanda ya san Kur'ani kuma ya koyar da shi"(15).
A Nahajul balaga imam Ali (A.S) ya ce: 'ku koyi Kur'ani domin shi ne kakan zukata kuma ku nemi ceto da haskensa domn shi ne warkar zukata, ku kyautata karanta shi domin shi na mafi amfanin kissoshi, domin masani mai aiki ba da ilmiminsa ba, kamar jahili ne mai dimuwa dab a ya farkawa daga jahilcinsa, hujja a kan sa ma tafi girma kuma hasara gareshi tafi lizimta kuma ya fi zama abin zargi wajen Allah"(16).
Daga ma'azu ya ce: Na ji Manzon Allah (S.A.W) yana cewa: "Babu wani mutum da zai sanar da dansa Kur'ani sai Allah ya daura wa iyayensa hular sarauta a alkiyama kuma an sanya musu kayan ado da mutane ba su taba ganin irinsu ba"(17).
Daga Annabi (S.A.W) cewa; ma'abota Kur'ani su ne mutanen Allah kuma kebantattunsa"(18).
Daga gareshi: "Mafificiyar ibada ita ce karanta Kur'ani"(19).
Kur'ani wadata ce babu wata wadata bayansa, kuma babu talauci bayansa"(20).
Daga gareshi: "mafificiyar al'umma ita ce masu hardacekuran'ani kuma ma'abota dare"(21).
Daga gareshi: "Kur'ani walimar Allah ce, kuma ku koyi walimarsa yadda zaku iya, wannan Kur'ani igiyar Allah ce kuma haske bayyananne kuma waraka mai amfani, kuma kariya ga wanda ya yi riko da shi kuma tsria ga wanda ya bi shi"(22). har zuwa karshen hadisi.
Daga gareshi: wanda ya karanta Kur'ani har ya bayyana shi, ya kuma kyaye shi, Allah zai shigar da shi aljanna kuma ya ba shi ceton mutane goma daga ahlin gidansa dukkaninsu kuma wutar jahannama da ta riga ta wajaba a kansu"(23).
Daga gareshi: "Masu dauke da Kur'ani a duniya su ne masanan malaman aljanna a ranar kiyama"(24).
Daga gareshi: "idan malami ya ce da yaro:ce ne: Bismillahir rahamanir rahim, sai yaro ya fada to Allah zai rubuta wa yaro da iyayen yaro da malaminsa kubuta daga wuta"(25).

Kur'ani Mai Ceto Ne

Daga Ishaka dan Galibi(26) ya ce: Abu Abdullah (A.S) ya ce: idan Allah ya tara mutanen farko da na karshe sai ga wani mutum ya zo bai kaywaonsa fuska sai muminai su duba ashe Kur'ani ne, sai su ce wannan namu ne, shi ne mafi kyawun abu da muka again, idanya je wajen sa sai ya tsayana a daman al'arshi saiubangiji ya ce: na rantse dagirmana da daukakata! Zai girmama wanda ya girmama ka, kuma in wulakanta wanda ya wulakanta ka"(27).
Daga abil Jarud ya ce: "Abu Ja'afar ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: ni ne farkon wanda zai zo wajen Allah (S.W.T) ranar kiyama da littafinsa da Ahlina (A.S) sannan sai al'ummata, sannan sai a tambaye su me suka yi da littafin Allah da Ahlina (A.S)"(28).
Daga Annabin karshe (S.A.W) ya ce: "wanda ya karanta Kur'ani sai ya yi tsammanin za a ba wa wani mutum fiye da abin da za a ba shi to hakika ya wulakanta abin da Allah ya girmama kuma ya girmama abin da Allah ya wulakanta"(29).
Daga Dalha dan Zaid daga Abu Abdullahi ya ce: "Wannan Kur'ani shi ne manarar shiriya kuma fitilar dare, sai mai neman yayewa ya yaye ganinsa kuma ya bude kallonsa da gani, domin tunani shi ne rayuwar zuciyar mai gani kamar yadda mai neman haskakawa yake haskakawa a cikin duhu"(30).
Daga Sama'ata ya ce: "Abu Abdullah (A.S) ya ce: ya kamata ga wanda ya karanta Kur'ani idan ya wuce wata aya mai wata mas'ala ko tsoratarwa ya roki Allah alherin da yake nema kuma ya roki lafiya da kubuta daga wuta da azaba"(31).
Daga Sakuni daga Abu Abdullah (A.S), daga iyayensa (A.S) ya ce: 'Manzon Allah (S.A.W) ya ce: idan fitinun suka babaye ku kamar yankin dare mai duhu to sai ku yi riko da Kur'ani domin shi ne mai ceto kuma abin ba wa ceto, wanda ya sanya shi gabansa zai jagorance shi, wanda kuma ya sanya shi a bayansa zai kora shi wuta, kuma shi ne jagora da yake siryarwa zuwa ga alheri kuma littafi ne shi wanda a cikinsa akwai bayanin komai kuma shi ne rarrabewa ba wasa ba ne, kuma yana da zahiri da badini, zahirinsahukunci nekuma badininsa sani ne, kuma zahirinsa yana da zurfi kuma badinsa yana da zurfi, yana da taurari kuma a kan taurarinsa akwai wasu taurarin, kuma ba a iya kirge abubuwan mamakinsa kuma mamakinsa ba ya tsufa.
To sai mai wartsake ganinsa ya bude ganinsa sosai, wanda ya gajiya -da shi ne- zai kubuta, kuma wanda ya wahala -da shi ne- zai tsira, hakika tunani hasken gani ne kamar yadda haske yake haskakawa a duhu, sai ku yi riko da kyakkyawan mafita da kuma karancin dako"(32).

Annabi (S.A.W) Da Kur'ani

Daga maimunul kaddah(33) daga Abu Ja'afar a wani hadisi ya ce: "Manzon Allah (S.A.W) ya ce: ni ina mamakin yadda nakansance ba na yin furfura idan na karanta Kur'ani".
Daga Ja'afar dan Muhammad daga babansa daga imam Ali (A.S) a wata magana mai tsayi yana mai siffanta masu tsoron Allah ya ce: "amma da dare suna masu daidaita kafafunsu suna masu karanta Kur'ani karantawa suna masu bakin ciki kuma suna masu ishara da shi domin tayar da bakin cikinsu a kan zunubansu, da kuma jin ciwonsu, idan suka wuce wata aya mai ban tsoro sai su karkata zukantansu da jinsu da ganinsu zuwa gareta, kuma fatar jikinsu tana tashi sai su ga kamar suna cikin karar jahannama ne kuma kukanta yana isa kunnuwansu, idan suka wuce wata aya ta kwadaitarwa sai su yi kwadayi kuma rayukansu su tsinkaya zuwa gareta domin bege, kuma su yi tsammanin cewa kamar tana gabansu ne"(34).
Daga Abu Hamza assumali daga Abu Ja'afar ya ce: "imam Ali ya ce: bana ba ku labarin masani na gaskiya ba? Shi ne wanda bai sanya mutane sun yanke kauna daga rahamar Allah ba, kuma bai sanya su sun amintu daga samun azabar Allah ba, kuma bai sanya su sun yanke kauna daga rahamar Allah ba, kuma bai ba su damar saba wa Allah ba, kuma bai bar Kur'ani ba domin kwadiatuwa zuwa ga waninsa. Kuma ku sani cewa: babu wani amfani ga ilimin da ba shi da wata fahimta cikinsa, kuma babu alheri ga karatun da babu tadabburi a cikinsa, kuma babu wani amfani ga ibada da ba bisa ilimi take ba"(35).

Ma'abota Kur'ani Da Falalarsu

Daga Sakuni(36) daga Abu Abdullah (A.S) ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: ma'abota Kur'ani suna cikin darajoji madaukaka kan dukkan mutane banda annabawa da manzanni, kada ku danne wa ma'abota Kur'ani hakkokinsu, ku sani suna da wani matsayi mai girma a wajen Allah madaukaki".
Daga Abdullah dan Abbas daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: madaukakan al'ummata su ne masu dauke (hardace) da Kur'ani kuma masu raya dare"(37).
Daga abu Sa'idul khuduri, ya ce: "Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "masu dauke da (hardace) Kur'ani su ne malaman 'yan aljanna"(38).
Daga imam Hasan Askari (A.S) a tafsirinsa, daga iyayensa daga Annabi (S.A.W) ya ce: masu hardace Kur'ani sun kebanta da rahamar Allah musamman, masu sanye da hasken Allah, masana zancen Allah, masu kusanci da Allah, wanda ya so su ya so Allah, wanda kuma ya ki su to hakika ya ki Allah, kuma Allah yana kare wa mai jin karatun Kur'ani da albarkacinsu, dukkan bala'o'in duniya kuma yana kare mai karanta shi daga bala'o'in lahira, na rantse da wanda ran Muhammad (S.A.W) yake hannunsa! mai jin karatun Kur'ani yana mai imani da shi ladansa ya fi na wanda ya yi sadaka da zainare mai girman Sabir, kuma mai karanta Kur'ani yana imani da shi ya fi ladan abin da yake daga al'arshi zuwa karkashin kasa"(39).
Daga Fudail dan yassar daga Abu Abdullahi (A.S) ya ce: mai hardace Kur'ani mai aiki da shi yana are da safatatul kiram madaukakan mala'iku"(40).
Daga Abu Abdullah (A.S) ya ce: na ji shi yana cewa: "wanda yake karanta Kur'ani da kyar yana kiyaye shi da wahala da kuma karancin hardarsa, to yana da lada biyu"(41).

Saurayi Da Kur'ani

Daga minhal alkassab(42) , daga Abu Abdullah (A.S) ya ce: "wanda ya karanta Kur'ani yana saurayi mumini kuma ya cakuda Kur'ani da namansa da jininsa Allah zai sanya shi tare da safatul kiram masu daraja na mala'uku, kuma Kur'ani zai kasance mai kariya gareshi a ranar kiyama, yana cewa: ya Ubangiji duk mai aiki ya samu ladaban da mai aikina, ka a shi mafi girman kyautarka, ya ce: sai a tufatar da shi tufafin ado guda biyu na aljanna, kuma a sanya masa hular girma a kansa sannan ya ce da shi: shin ka yarda da abin da muka yi masa, sai Kur'ani ya ce ni na yi masa fatan sama da hakan sai a ba shi aminci a hannun damansa da dawwama a hagunsa, sannan sai ya shiga aljanna sai ya ce karanta aya sai ya karanta ya sake dauakak daraja, sanan sai a ce da Kur'ani yanzu ka yarda da abin da muka yi masa, sai ya ce na'am. ya ce: wanda ya karanta shi da yawa ya saba da karanta shi da kyar da wahala Allah zai ba shi lada biyu ne"(43).
Daga Aban dan Taglib daga Abu Abdullah ya ce "wanda ya samu Kur'ani ya yi imani da shi to kamarsa kamar doddoya (lemon masar) ce da take da kamshi kuma cikinta mai dadi, amma wanda bai samu Kur'ani ba kuma bai yi imani da shi ba kamar kubaku ne da dandanonsa mai daci kuma ba ta da wani kamshi(44).
Daga Fudail dan yassar daga Abu Abdullahi (A.S) ya ce: "Manzon Allah (S.A.W) ya ce: ku koyi Kur'ani, domin shi zai zo ranar kiyama ga ma'abocinsa a surar saurayi mai kyau, yana mai launi mai ado, sai ya ce da shi: ni ne kur'anin da ka kasance ka raya darenka ka yi kishirwantar da makogwaronka, ka busar da yawunka ka kuma zubar da hawayenka (har ya ce) ka yi murna, sai a zo da wata hula sai da dora a kansa sai a ba shi aminci a damansa dawwama kuma a aljanna a hagunsa, kuma a tufatar da shi kayan ado biyu sannan sai a ce da shi: ka karanta ka samu daukakar daraja, kuma duk sa'adda ya karanta aya sai ya daukaka da daraja kuma a tufatar da iyayensa kayana ado biyu idan muminai ne, sannan sai a ce da su wannan saboda kun koya masa Kur'ani ne"(45).
Daga Asbag dan Nabata ya ce: "imam Ali (A.S) ya ce: Allah yakan so ya azabtar da mutanen duniya gaba daya, ta yadda babu wanda zai tsira daga cikinsu idan suka yi aiki da sabo kuma suka yi miyagun laifuffuka, amma idan ya duba ma'abota furfura masu taka kafafunsu zuwa salloli da kuma yara masu koyon karatun Kur'ani sai ya tausaya musu ya jinkirta wannan daga garesu"(46).

Masu Dauke (Hardace) Da Kur'ani Da Siffofinsu

Daga Amru dan Jami'i(47) daga Abu Abdullah ya ce: Manzo Allah (S.A.W) ya ce: mafifinnci mutane da ya cancanci tsoro a fili da a boye, shi ne; mai hardace Kur'ani, kuma wanda ya fi cancantar salla da azumi a boye da fili shi ne mai hardce kura'ni sannan sai ya yi kira da sauti madaukaki ya kai mai hardace da kur'ani kakaskantar da kai, Allah zai daukaka ka, kada ka yi izza da shi, sai Allah ya kaskantar da kai, ya kai mahardacin Kur'ani ka yi ado da shi saboda Allah sai Allah ya yi maka ado da shi, kada ka yi ado da shi ga mutane sai Allah ya aibata ka, wanda a cika Kur'ani to yana kansa ne kada ya yi jahilci tare da masu jahilci kuma kada ya yi fushi cikin masu fushi kuma ya yi rangwame ya yi hakuri don girman Kur'ani, wanda aka ba wa Kur'ani sai ya yi tsammanin an ba wa wani abin da ya fi nasa to ya wulakanta abin da Allah ya girmama kuma ya girmama abin da Allah ya wulakanta(48).
Daga Abu Ja'afar (A.S) ya ce: masu karanta Kur'ani mutum uku ne, mutumin da ya karanta Kur'ani sai ya rike shi kayan hajarsa kuma ya nemi abin da yake hannun sarakuna da shi kuma ya daga wa mutane kai da shi, da mutumin da ya karanta Kur'ani sai ya hardace harruffansa ya tozarta dokikinsa ya kuma munana kiyaye shi, to kada Allah ya yawaita wadannan daga cikin masu hardar Kur'ani. Da mutumin da ya karanta Kur'ani sai ya sanya maganin Kur'ani inda cutarsa take sai ya raya darensa da shi kuma ya ji yunwar ranarsa (azumi) da shi kuma ya tsayar da sallolinsa da shi, ya kuma nisanci shimfidarsa da shi, da wadannan ne Allah ya kare bala'ai daga mutane kuma da su ne Allah yake maganin makiya, da su ne Allah ya ke saukar da ruwan sama, wallahi! Wadannan a cikin mahardata Kur'ani su suka fi karanci daga jan kibrit(49).
Daga Husain dan yazid daga Ja'afar Sadik daga kakanninsa (A.S) a cikn hadisin da yake magana kan abubuwan da aka hana ya ce: "wanda ya karanta Kur'ani sannan sai ya sha haram da shi ko ya zabi son duniya da kawarta a kansa to ya samu fushin Allah sai dai idan ya tuba, ku sani wanda ya mutu ba tare da tuba ba to Allah zai yi masa hisabi, kuma ba zai gushe ba sai abin rusawa"(50).
Daga Isma'il dan abu ziyad daga Ja'afar Sadik daga kakanninsa (A.S) ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "mutum biyu daga al'ummata idan suka gyaru al'ummata ta gyaru idan suka lalace al'ummata ta lalace: sarakuna da makaranta"(51).
Daga Sakuni daga abu Abdullahi daga babansa daga iyayensa (A.S) ya ce: "wanda ya karanta Kur'ani yana cin hakkin mutane da shi to zai zo ranar lahira babu wata tsoka ko kashi a fuskarsa(52).

Masanin Kur'ani Da Ba Ya Aiki Da Shi

Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce : wanda ya koyi Kur'ani bai yi aiki da shi kuma ya zabi son duniya da kawarta to ya cancancin fushi Allah kuma yana daraja daya da Yahudu da Nasara wadanda suka wurgar da littafin Allah a bayansu kuma wanda ya karanta Kur'ani yana neman suna da duniya da shi to zai hadu da Allah fuskrasa babu tsoka ko daya kuma a kur'ani ya tura keyarsa har sai ya shigar da shi wuta, kuma ya fada cikinta tare da wanda ya fada, wanda ya karanta Kur'ani bai yi aiki da shi ba to Allah zai tashe shi ranar kiyama makaho sai ya ce: "ya Ubangiji me ya sa ka tashe ni makaho alhalin ina mai gani da can" . sai ya ce: "haka nan ne muka zo maka ayoyinmu sai ka manta ta, kuma haka nan ne a yau za a manta da kai" . Sai a yi umarni da shi zuwa wuta, kuma wanda ya karanta Kur'ani domin neman ladan Allah da ilimin addini yana da lada kamar na dukkan abin da aka ba wa mala'iku da annabawa da manzanni, kuma wanda ya koyi Kur'ani yana son riya da neman suna da shi domin ya yi jayayya da wawaye kuma ya yi alfahari ga malamai ya kuma nemi duniya da shi to Allah zai daidaita kashinsa ranar kiyama kuma babu wata wuta da ta fi azabar tasa, kuma babu wata na'uin azaba sai an yi masa ita saboda tsananin fushin Allah a kansa kuma wanda ya koyi Kur'ani ya kaskantar da kai a neman ilmi kuma ya sanar da bayin Allah yana neman abin da yake wajan Allah to babu wani wanda ya fi shi lada ko matsayi, kuma babu wata daraja madaukakiya ko matsayi sai ya samu rabo mafi girma da matsayi mafi daukaka daga gareta"(56).
Daga Annabi (S.A.W) ya ce: "hakika akwai wani wuri a jahannama da 'yan wuta suke neman tsari da shi kullum sau dubu saba'in (har ya ce) sai aka tambaye shi wannan azabar wa kenan? Ya ce: ga mai shan giya daga masu karatun Kur'ani masu barin salla"(57).
Daga Abul ash'hab annakha'i ya ce: Ali dan Abi Dalib ya ce: "wanda ya shiga musulunci yana mai biyayya kuma ya karanta Kur'ani a zahiri to yana da dinare dari biyu daga Baitulmalin musulmi idan aka hana shi a duniya to zai karba a lahira a lokacin da yake mafi bukata gareta"(58).
Daga Muhammad dan Ali dan Husain ya ce: Abu Abdullahi (A.S) ya ce:"kada ku sanya mata a dakuna kuma kada ku koya musu rubutu (kawai) kada ku koya musu surar Yusuf, ku koya musu saka da surar Nur…(59)" hanin abin da ake nufi da shi wato rubutu da karatu na fitina.

Karanta Kur'ani A Kodayaushe

Daga Mu'awiya dan Ammar(60) daga Abu Abdullahi a cikin wasiyyar Annabi ga Ali (A.S) ya ce: "ka yi riko da karanta Kur'ani a kodayaushe".
Daga Zuhuri ya ce: na ce da Ali dan Husain (A.S) wane aiki ne ya fi? Ya ce: mai zuwa mai tafiya. Sai na ce: menene mai zuwa mai tafiya? Sai ya ce: karanta farkon Kur'ani har zuwa karshensa, duk sadda farkonsa ya zo sai ya tafi karsensa"(61).
Daga Hafsu ya ce na ji Musa dan Ja'afar (A.S) yana cewa darajojin aljanna daidai gwargwadon ayoyin Kur'ani ne sai a ce: karanta ka yi sama sai ya karanta ya yi sama"(62).
Daga Abdullahi dan Sulaiman daga Abu Ja'afar (A.S) ya ce: "wanda ya karanta Kur'ani yana tsaye a sallarsa Allah zai rubuta masa kyakkyawa dari a kan kowne harafi kuma wanda ya karanta shi a zaune a cikin sallarsa to Allah zai rubuta masa kyakkyawa hamsin a kan kowane harafi, kuma wanda ya karanta ba a sallarsa ba to Allah zai rubuta masa kyakkyawa goma a kan kowane harafi"(63).
Daga bashir dan Galib al'asadi daga Husain dan Ali (A.S) ya ce: wanda ya karanta aya daga littafin Allah madaukaki yana tsaye to za a rubuta masa kyakkyawa dari a kan kowane harafi, idan kuwa ba a salla ba ne to za a rubuta masa kyakkyawa goma, kuma idan ya saurari Kur'ani to Allah zai rubuta masa kyakkyawa da kowane harafi, idan kuwa ya kammala Kur'ani a dare to mala'iku zasu ya yi masa addu'a har safiya, idan kuwa ya kammala shi da rana to mala'iku masu kiyayewa zasu yi masa addu'a har maraice, kuma yana da addu'a da za a amsa masa kuma wannan ya fi masa abin da yake tsakanin sama da kasa. Sai na ce: wannan ga wanda ya karanta Kur'ani kenan, wanda bai karanta ba fa? Sai ya ce: ya kai dan'uwan bani Asad Allah mai baiwa ne mai karimci idan ya karanta abin da ya sani Allah zai ba shi wannan"(64).

Wanda Ya Saurari Karatun Kur'ani

Daga Muhammad dan Bashir(65) daga Ali dan Husain (A.S) hakika an ruwaito wannan hadisi daga Abu Abdullahi (A.S) ya ce: 'wanda ya saruari harafi daya daga littafin Allah ba tare da ya karanta ba to Allah zai rubuta masa kyakkyawa (lada) kuma ya shafe masa mummuna (zunubi) kuma ya daukaka shi daraja, kuma wanda ya koyi harafi Allah zai rubuta masa lada goma ya shafe masa zunubi goma kuma ya duaka shi daraja goma. ya ce: ba na cewa: kowace aya, abin da nake nufi harafi kamar 'b', ko 't', da makamantansu, ya ce: wanda ya karanta harafi yana zauni toallah zai rubuta masa lada hamsin ya shafe masa zunubi hmasri kuma ya daga masa daraja hamsin kuma wanda ya karanta harafi yana tsaye a salla to Allah zai rubuta masa lada dari kuma ya shafe masa zunubi dari kuma ya daukaka shi daraja dari, kuma wanda ya kammala shi to yana da addu'a da za a amsa masa da gaggawa da kuma ta jinkiri, ya ce: sai na ce: ina fansarka! kammala shi dukkansa? Ya ce: kammala shi dukkansa"(66).
Daga Ishak dan Ammar daga bu Abdullahi (A.S) ya ce: "Wanda ya karanta aya takur'ani yana salla da ita a kowane dare to Allah zai rubuta masa kunutin (ibadar) dare daya, wanda ya karanta ayoyi dari ba a sallar dare ba to Allah zai rubuta masa sisin lada a lauhil mahafuz, sisi yana nufin; ukiyya dubu da dari biyu, kowace ukiyya tafi dutsen uhudu girma(67).
Daga Anas ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "wanda ya karanta aya dari ba za a rubuta shi daga masu gafala ba, kuma wanda ya karanta aya dari biyu to za a rubuta shi cikin masu ibada, kuma wanda ya karanta ayoyi dari uku to Kur'ani ba zai kai kararsa ba". Yana nufin wanda ya hardace shi kamar kwatankwacin hakan, masu magana suka ce: yaron ya karance Kur'ani idan ya hardace shi(68).

Surar Fatiha Da Falalarta

Daga Hasan dan Ali Askari (A.S) daga iyayensa (A.S) ya ce: "Fatiha ita ce mafi daukakar abin da yake cikin taskokin al'arshi (har dai ya ce:) wanda ya karanta ta yana mai imani da wilayar Muhammad da alayensa to Allah zai ba shi lada a kan kowane harafi kowanne daga ciki ya fi duniya da duk abin da yake cikinta na dukiya da alhairai, wanda kuwa ya ji mai karanta ta to yana da girman abin da yake ga mai karantawa, don haka kowannenku ya yawaita wannan alheri"(69).
Daga Fadl dan Hasan Dabarasi (majma'al bayan) daga Annabi (S.A.W) ya ce:"mafificiyar ibada ita ce karanta Kur'ani"(70).
Daga gareshi ya ce: "wannan Kur'ani shi ne igiyar Allah kuma haske mabayyani, kuma sheto mai amfani (har ya ce) ku karanta shi, ku sani Allah yana saka wa da lada goma akan karanta shi da kowane harafi na karanta shi, ku sani ni ba na cewa:"A L M, goma kenan, sai dai A goma, L goma, M goma(71).
Daga gareshi (A.S) yana cewa: "ana cewa da mai karanta Kur'ani karanta ka yi sama karanta kamar yadda kake karantawa a duniya ka sani matsayinka in da ka tsaya ne"(72).
Daga gareshi (A.S): "wanda ya karanta Kur'ani kamar an sanya annabta ne a goshensa sai dai shi ba a yi masa wahayi"(73).
Daga Ahmad dan Fahad (a littafin Iddatud'da'i) daga Annabi sawa ya ce: "Ubangiji madaukaki ya ce: wanda ya shagaltu da karanta Kur'ani yana barin rokona to zan ba shi mafificin abin da nake ba wa masu godiya"(74).

Wanda Ya Karanta Kur'ani Sai Ya Manta Shi…

Daga abu Basir(75) ya ce: Abu Abdullahi (A.S) ya ce: wanda ya mance surar Kur'ani to za a nana masa ita a cikin sura mai kyau, idan ya gan ta sai ya ce: ke wacece? Kina da kyau sosai! Ina ma dai ke tawa ce! Sai ta ce: ba ka sanni ba ne? ni ce sura kaza da kaza da ba ka manta da ni ba da na daukaka ka zuwa wannan wuri".
Daga Ya'akubul Ahmar ya ce: na ce da Abu Abdullahi (A.S): ina da bashi a kaina mai yawa kuma Kur'ani ya kusa kubuce mini, sai Abu Abdullahi (A.S) ya ce: Kur'ani! Kur'ani! Ka sani sura aya ko sura daya a Kur'ani takan zo ranar kiyama har sai ta daukaka ka daraja wacce da ka kiyayeta da ta kai ka can"(76).
Daga Ya'akubul Ahmar ya ce: na ce da Abu Abdullahi (A.S) in fansarka da raina bakin cikin ya same ni kuma ba a bin da ya rage mini na alheri sai da wani abu ya kubuce mini daga gareshi har Kur'ani wani abu ya kubue ce mini daga gareshi. Sai hankalisa ya tashi da na ambaci Kur'ani sannan sai ya ce: mutum yakan manta da surar Kur'ani sai ta zo masa ranar kiyama har sai ta yi sama da shi da wasu darajoji sannan sai ta ce: aminci ya tabbata gareka, sai ya ce: aminci ya tabbata gareki ke wacece? Sai ta ce: ni ce sura kaza da kaza ka tozarta ni ka bar ni, amma da ka yi riko da ni da na kai ka wannan daraja, sannan sai ya yi nuni da dan yatsansa sannan sai ya ce: ina umartar ku da karanta Kur'ani ku nemi saninsa ku sani daga mutane akwai wanda yake neman sanin Kur'ani don a ce masa wane mai karatu ne, daga cikinsu akwai wanda yake neman saninsa domin ya nemi suna da shi, sai a ce wane yana da murya mai kyau wadannan ba su da wani alheri. Daga cikinsu akwai wanda yake neman saninsa sai ya tsayar da shi dare da ranar ba ruwansa mutane sun sani ko kuwa ba su sani ba"(77).
Daga Sa'id dan Abdullahil A'araj ya ce: na tambayi Abu Abdullahi (A.S) game da mutumin da yake karanta Kur'ani sannan sai ya manta shi, shin yana da laifi? Sai ya ce: A'a(78).
Da kuma abin da yazo daga Husain dan Zaid daga Ja'afar Sadik (A.S) daga iyayensa (A.S) a wani hadisi (game da abubuwan da aka hana) cewa Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "ku sani wanda ya koyi Kur'ani sannan sai ya manta shi to zai hadu da Allah ranar kiyama abin yi wa kukumi kuma a sallada masa maciji sakamakon kowace aya da ya manta ta ya kasance mai tafiay tare da shi zuwa wuta sai dai idan an gafarta masa". Wannan yana nufin wanda ya bar hukunce-hukuncensa ne.

Daga Ladubban Karanta Kur'ani

Daga Muhammad dan Fudail(79) daga Abul Hasan (A.S) ya ce: "Na tambaye shi: ina karanta Kur'ani sai fitsari ya kama ni sai in tashi in yi fitsari sannan in yi tsarki in wanke hannuna sannan sai in koma wa littafi sai in karanta shi? Sai ya ce: A'a, har sai ka yi alwalar salla".
Daga littafin hisal da sanadinsa daga Ali dan Abu Dalib (A.S) a wani hadisi guda dari hudu ya ce: bawa ba ya kanta Kur'ani idan ya kasance ba bisa tsarki ba har sai ya yi tsarki"(80).
Daga Ahmad dan Fahad ya ce: imam (A.S) ya ce: "mai karanta Kur'ani yana da a cikin salla yana da lada dari ga dukkan harafi da yake karantawa a salla a tsarye, a zaune kuwa lada hamsin kuma yana mai tsarki, ba a salla ba lada ishirin da biyar idan ba shi da tsarki lada goma, kuma ba na cewa: "A L M R" goma. Sai dai A lada goma kenan, L lada goma, M lada goma, R lada goma.
Daga Hasan dan Ali Askari (A.S) a tafsirinsa ya ce: Amma fadinsa wanda ya soyar da kai zuwa gareshi kuma ya umarce ka da karanta shi ya yin karanta Kur'ani shi ne: "ina neman tsarin Allah mai ji masani daga shedan jefaffe, hakika imam Ali (A.S) ya ce: ina neman tsari ai ina neman kariyar Allah –har ya ce- neman tsari shi ne abin Allah ya umarci bayi da shi gun karantawarsu ga Kur'ani, don haka idan ka karanta Kur'ani to ka nemi tsarin Allah daga shedan abin jefewa(81). kuma wanda ya ladabtu da ladubba nallah zai kai shi zuwa ga shiriya madawwamiya sannan sai ya ambaci hadisin da tsayinsa daga Manzon Allah yana cewa: Idan ka son kada sharrinsu ya same ka kuma makircinsu kada ya zo maka to ka fada idan ka wayi gari " Ina neman tsarin Allah daga shedan jefaffe to Allah zai kare ka sharrinsu.

Kur'ani Alkawarin Allah Ne To Kiyaye Alkawarinsa

Daga Hariz daga Abu Abdullahi (A.S) ya ce: "Kur'ani alkawarin Allah ne kan halittarsa don haka ya kamata ga mutum musulmi ya duba alkawarinsa, kuma ya karanta ayoyi hamsin daga gareshi kowace rana"(82).
Daga zuhuri ya ce: na ji Ali dan Husain (A.S) yana cewa: ayoyin Kur'ani taskoki ne kuma duk sadda aka bude wata taska ya kamata ka duba a bin da yake cikinta"(83).
Daga Mu'ammar dan khallad daga Ali Rida (A.S) ya ce: na ji shi yana cewa: ya kamata ga mutum idan ya wayi gari ya karanta ayoyi hamsin bayan addu'ar salla"(84).
Daga Abdul'a'ala bawan aali Samu daga Abu Abdullahi (A.S) ya ce: "idan akwai musulmi a gida da yake karanta Kur'ani to yana bayyana ga mutanen da suke sama kamar yadda taurari suke bayyana ga mutanen duniya"(85).
Daga abul kadah daga Abu Abdullah (A.S) ya ce: "imam Ali (A.S) ya ce: gidan da ake karanta Kur'ani kuma ake ambaton Allah mai girma a cikinsa to albarkarsa zata yi yawa kuma shedanu su guje shi kuma ya haskaka ga mutane sama kamar yadda taurari suke ga mutane kasa, kuma gidan da ba a karanta Kur'ani a cikinsa kuma ba a ambaton Allah to albarka zai ta yi karanci kuma mala'iku su kaurace masa, shedanu su zo masa"(86).
Daga Abu Abdullah (A.S) daga babansa ya ce: "ya kasance yana hada mu sai ya umarce mu da ambaton Allah har sai rana ta bullo, sannan sai ya umarce mu da karatun Kur'ani, daga cikinmu akwai mai karantawa, wanda ba ya (iya) karantawa sai ya umarce si da ambaton Allah, kuma duk gidan da ake karanta akur'ani a cikisa kuma ake ambaton Allah a cikinsa to albarkarsa zata yi yawa"(87).
Daga Lais dan Abu sulaim (ya daga hadisin) ya ce: Annabi (S.A.W) ya ce: Ku haskaka gidajenku da karanta Kur'ani kada ku rike su kaburbura kamar yadda Yahudu da Nasara suka yi, suka yi salla a coci da wajen bauta suka bar gidajensu, ku sani idan aka yawaita karanta Kur'ani ga cikin gida sai alherinsa ya yawaita kuma ma'abotansa su yalwata kuma ya haskaka ga mutane sama kamar yadda taurari suke haskaka ga mutane duniya"(88).
A cikin Iddatud'da'i ya zo daga imam Ali Rida (A.S) zuwa ga Annabi (S.A.W) ya ce: "ku sanya wa gidajenku wani kaso na Kur'ani ku sani gidan da ake karanta Kur'ani ma'abotansa zasu yalwata kuma alherinsa zai yawaita kuma mazauna zasu dadu, idan kuwa ba a karanta Kur'ani ba sai ya kuntata ga ahlinsa, kuma alherinsa ya karanta, kuma mazaunansa su tawaya"(89).

Tajiri Da Kur'ani

Daga Fudail dan Yassar(90) daga Abu Abdullah (A.S) ya ce: me zai hana tajiri a cikinku mai shagaltuwa a kasuwancinsa idan ya koma gidansa kada ya yi bacci har sai ya karanta sura ta Kur'ani, sai a rubuta masa kowace aya da yake karantawa lada goma kuma a shafe masa zunubi goma".
Daga Sa'ad dan Darif, daga Abu Ja'afar Bakir (A.S) ya ce: "Manzon Allah (S.A.W) ya ce: wanda ya karanta ayoyi goma a kowane dare ba za a rubuta shi daga masu gafala ba, wanda kuma ya karanta ayoyi hamsin za a rubuta shi daga masu ambaton Allah da yawa, wanda ya karanta ayoyi dari za a rubuta shi daga masu ibada, wanda ya karanta ayoyi dari biyu za a rubuta shi cikin masu khushu'I, wanda ya karanta ayoyin dau uku za a rubuta shi cikin masu rabauta, wanda ya karanta ayoyi dari biyar za a rubuta shi cikin masu ijtihadi, wanda ya karanta ayoyi dubu to za a rubuta masa sisi, sisi kuwa shi ne awo dubu goma sha biyar na awon zinare… mafi karanci kamar girman uhud, mafi girmansa kamar tsakanin sama da kasa.
Daga Abu Hamza assumali daga Abu Ja'afar (A.S) ya ce: wanda ya kammala Kur'ani a Makka daga juma'a zuwa wata juma'a ko kasa da hakan ko sama da haka to Allah zai ba shi lada daga farkon juma'a ta duniya zuwa ta karshe ta duniya, kuma haka nan ma sauran ranaku"(91).
Daga Jabir, daga Abu Ja'afar (A.S) ya ce: "Kowane abu yana da kaka, ku sani kakar Kur'ani shi ne watan Ramadan"(92).

Karanta Kur'ani Da Duba Littafin Kur'ani

Daga Ya'akubu dan yazid(93) (ya daga shi zuwa) ga Abu Abdullahi (A.S) ya ce: "wanda ya karanta Kur'ani da duban mushafi to ganinsa ya dadada kuma za a rangwama wa iyayensa koda kuwa sun kasance kafirai ne".
Daga Annabi (S.A.W) ya ce: "Babu abin da ya fi yi wa shedan tsanani kamar karanta Kur'ani ta hanyar duban littafi"(94).
Daga Ishak dan Ammar, daga Abu Abdullahi (A.S) ya ce: ina fansarka da raina! Ni na hardace Kur'ani a zuciyata, shin in karanta shi da ka ko da duba littafi wanne ne ya fi? Sai ya ce: ka karanta da duba littafi shi ya fi, ba ka san duba cikin littafi ibada ba ne(95).
Daga Abuzar ya ce: "Na ji Manzon Allah (S.A.W) yana cewa: Duba zuwa ga Ali (A.S) ibada ce, duba zuwa ga iyaye da tausayawa da jin kai ibada ne, duba zuwa ga littafin Kur'ani shi ma ibada ne, haka nan duban Ka'aba ibada ne".
Daga Hammad dan Isa, daga Abu Abdullahi (A.S) daga babansa ya ce: "yana burge ni ya kasance akwai littafin Kur'ani a cikin gida da Allah yake kore shedanu da shi"(96).
Daga Abu Abdullah ya ce: "Uku suna kai kuka wajen Allah madaukaki "Masallaci da aka kauracewa, mutane ba sa salla a ciki, da malami tsakanin jahilai, da littafi da aka rataye har kura ta hau kansa ba a karanta shi"(97).

Karanta Kur'ani

Daga Abdullahi dan Sulaiman(98) ya ce: "na tambayi Abu Abdullahi (A.S) game da fadin Ubangiji "ka karanta Kur'ani karantawa"(99). Sai ya ce: imam Ali (A.S) ya ce: ka bayyana shi a fili kada ka rera shi kamar waka, kuma kada ka daidaita shi kamar yashi, sai dia ku kwankwasa zukata kekasassu da shi, kuma kada hadafin dayanku ya zam shi ne ya kai karshen sura".
Daga salim alfarra'u daga wanda ya ba shi labari, daga Abu Abdullahi (A.S) ya ce: "Ka bayyana Kur'ani domin shi balarabe ne"(100).
Daga muhamad an Fudail ya ce: Abu Abdullahi (A.S) ya ce: "An karhanta karanta kulhuwal-Lahau da lumfashi daya"(101).
Daga abu Basir, daga Abu Abdullahi ya ce: Fadinsa madaukaki: "Ka karanta Kur'ani karantawa". Ya ce: shi ne ka zauna a cikinsa ka kuma kyautata sautinka da shi"(102).
Daga Ummu Salama ta ce: "Manzon Allah (S.A.W) yana yanka karatunsa aya aya".
Daga ibn Abu umair, da wanda ya ambata, daga imam Ja'afar Sadik (A.S) ya ce: "Kur'ani ya sauka da bakin ciki, ku karanta shi da bakin ciki"(103).
Daga Abdullahi dan Sinan daga Abu Abdullahi (imam Ja'afar Sadik) (A.S) ya ce: "Allah ya yi wahayi ga Musa dan Imran (A.S) da cewa; idan ka tsaya a gabana, to ka tsaya matsayin mai kaskan da kai mabukaci, idan ka karanta Attaura to ka jiyar da ni da sauti mai bakin ciki"(104).
Daga Hafsu, ya ce: Ban ga wani mutum ba mafi tsananin tsoronsa a kan kansa daga Musa dan Ja'afar (A.S) ba, kuma ban ga wani mafi kauna daga gareshi ba, karatunsa ya kasance na mai bakin ciki ne, idan ya karanta to kamar yana magana da wani mutum ne"(105).

Bayyana Karatun Kur'ani Da Boye Shi

Daga Saifu dan Umaira(106) daga wani mutum, daga Abu Ja'afar (A.S) ya ce: "wanda ya karanta "inna anzalnahu" yana mai bayyanar da sautinsa, to kamar mai zare takobinsa yana yaki a tafarkin Allah ne, wanda ya karanta ta a boye to kamar mai cakuda jininsa ne a tafarkin Allah, wanda ya karanta ta sau goma to za a shafe masa zunubai dubu".
Daga Mu'awiya dan Ammar ya ce: "Na ce da Abu Abdullah (A.S) mutmin da yake ganin yana wani abu na addu'a kuma yana karatu har sai ya daga sautinsa, sai ya ce: babu laifi, Ali dan Husain (A.S) ya kasance mafi kyawun sauti da Kur'ani, ya kasance idan ya daga sautinsa har sai mutanen gida sun ji sautinsa, kuma Abu Ja'afar ya kasance mafi kyawun mutane sauti da Kur'ani idan ya tsaya da dare yana karatu sai ya daga sautinsa sai masu wucewa na daga masu lambu da wasunsu su tsaya suna jin karatunsa"(107).
Daga Abuzar, daga Annabi (S.A.W) a wasiyyarsa ya ce: "ya Abuzar! Ka yi kasa da muryarka gun jana'iza da gun yaki da gun karatun Kur'ani"(108).
Daga Abdullahi dan Sinan, daga Abu Abdullahi (A.S) ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: ku kranta Kur'ani da muryar larabawa da sautinsu kada ku yi sautin ma'abota fasikanci da masu ashararanci, ku sani masu mutane zasu zo bayana suna kokkomawa da kur';ani kamar rerawar waka da kuma ihu, da rahbaniyanci, alhalin ba ya wuce makogaronsu, zukatansu a juye suke haka nan zukatan wanda suke burge shi"(109).
Daga Ali dan Muhammad Nufali, daga abul Hasan (A.S) ya ce: na ambaci murya gunsa sai ya ce: hakika Ali dan Husain (A.S) ya kasance yana karanta Kur'ani da yawa masu wucewa sukan tsaya sai ya kusa suma saboda kyawun sautinsa"(110).
Daga Abdullahi dan Sinan, daga Abu Abdullahi (A.S) ya ce Annabi (S.A.W) ya ce da ni komai yana da ado kuma adon Kur'ani shi ne sauti mai kyau"(111).
Daga Hasan dan Abdullahi tamimi daga babansa daga Ali Rida (A.S) ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "ku kyautata Kur'ani da sautinku ku sani sauti mai kyau yana dada wa Kur'ani kyau"(112).

Kur'ani Da Ladubban Karanta Shi Da Kuma Sauraronsa

Daga Jabir(113), daga Abu Ja'afar (A.S) ya ce: "Na ce: wasu mutane suna suma idan aka ambaci wani abu na Kur'ani ko ka fade shi sai su fadi kamar da za a yanke hannunsu ko kafarsu ba zasu iya ji ba, sai ya ce: subhanallah! Wannan daga shedan ne, ba da wannan ake siffanta su ba, shi bai komai ba ne sai taushi da hawaye da tsoro"(114).
Daga Abdullahi dan Abu ya'afur, daga Abu Abdullahi (A.S) ya ce: "na ce masa: mutumin da yake karanta Kur'ani, shin wajibi ne a kan wanda ya ji shi ya saurara kuma ya saurare shi? Sai ya ce: na'am idan ya karanta Kur'ani gunka to wajibi ne a kanka ka saurara kuma ka saurare shi(115).
Daga Ali dan Mugira daga Abul Hasan (A.S) ya ce: Na ce masa: babana ya tambayi kakanka game da kammala Kur'ani a kowane dare, sai kakanka ya ce masa a kowane dare ne, sai ya ce masa: a watan Ramadan, sai kakanka ya ce masa: a watan Ramadan, sai babana ya ce masa haka ne daidai yadda zaka iya. Babana ya kasance yana kammala Kur'ani sau arba'in a watan Ramadan, sannan nima na sauke shi bayan babana. Saudayawa na kasa daga hakan ko kuma in dada sama da hakan, sannan sai na sanya ladan sauka daya ga Manzo (S.A.W) wata kuma saukar ga imam Ali (A.S) wata kuma ga Fadima (A.S) sanan sai ga imamai daya bayan daya har na kawo kanka, sai na ba ka ladan sauka daya. To me nake da shi da wannan? Sai ya ce: zaka kasance tare da su a ranar kiyama. sai na ce: Allah mai girma ina da wannan?! Sai ya ce: E, har sau uku(116).
Daga Sulaiman dan khalid, daga imam Ja'afar Sadik (A.S) ya ce: manzon Allah (S.A.W) ya zo wa wani saurayi daga Ansar sai ya ce: ni ina son in karanta muku wanda ya yi kuka yana da aljanna, sai ya karanta karshen surar Zumur: "aka kora wadanda suka kafirta zuwa jahannama gargadawa" zuwa karshen sura, sai kowa ya yi kuka banda wannan saurayin, sai ya ce: ya Manzon Allah (S.A.W) na nemi yin kuka amma idanuwana ba su zubo ba, sai ya ce: ni zan sake muku wanda ya nemi yin kuka to yana da aljanna, sai ya koma maimaitawa, sai mutane suka yi kuka, kuma shi ma wannan saurayi ya kirkiri kuka sai suka shiga aljanna gaba daya"(117).
Daga Ja'afar dan Muhammad daga babansa, daga iyayensa (A.S) ya ce: "ku koyi Kur'ani da larabcinsa…"(118).
Daga Sulami daga babansa, daga Abu Abdullahi (A.S) ya ce: "ku koyi larabci domin shi ne zancen Allah da ya yi bayinsa magana da shi kuma magabata suka yi magana da shi"(119).
A littafin Iddatud'da'i daga Abu Ja'afar Jawad (A.S) ya ce: mutane biyu ba su yi daidai ba a addini da nasara sai wanda ya fi su a wajen Allah (S.A.W) ya kasance shi ne wanda ya fi su ladabi, sai na ce: na san fifikonsa a wajen mutane a majalisi, to menene fifikonsa a wajen Allah (S.W.T)? Sai ya ce da karanta Kur'ani kamar yadda ya sauka da kuma karanta shi ba lahani, domin addu'a mai lahani ba ta hawa zuwa ga Allah".
Daga Sakuni daga Abu Abdullahi (A.S) ya ce: Annabi (S.A.W) ya ce: mutum ba'ajame daga al'ummata yakan karanta Kur'ani da ajaminsa sai mala'iku su daukaka shi sama waje Allah da larabcinsa".


1. Yasin aya: 82.
2. Biharul anwar; j 61, shafi: 117, babi 2. bugun Bairut.
3. Ali imrana: aya: 85.
4. Duba tarihul alam mujalladi na 1-2. Da Muhammad wal Kur'ani. Da Bakatun adira fi ahwali khatimin nabiyyin. Da siratul fawaha.
5. Alaki, aya: 1-5.
6. Manakib, mujalladi 1, shafi na 56.
7. Kashful gumma, mujalladi 2, shafi: 537, fasali 4, babi 5.
8. Kashful gumma, mujalladi 2, shafi: 537, fasali 4, babi 5, surar ma'ida: aya: 3.
9. Fusilat, aya: 42.
10. Wasa'ilusshi'a, kitabussalat, babi 1, abwabu kira'tul Kur'ani walau fi gairissalati, hadisi 1-3.
11. Kafi: mujalladi na biyu: shafi: 598.
12. Kafi: mujalladi na biyu: shafi: 602.
13. Kafi mulladi na biyu: shafi na 602.
14. Wasa'ilusshi'a, kitabussalat, babi 1, abwabu kira'tul Kur'ani, hadisi 4-16.
15. Mustadrik, mujalladi 4, shafi: 245. Wasa'ilusshi'a, mujalladi 6, shafi: 167.
16. Wasa'ilusshi'a, mujalladi 6, shafi: 167.
17. Attahazib, mujalladi 7, shafi: 199.
18. Attahazib, mujalladi, 2, shafi; 234.
19. Wasa'ilusshi'a, mujalladi 5, shafi: 294.
20. Wasa'ilusshi'a, mujalladi 6, shafi: 168.
21. Man la yahaduruhul fakih: mujalladi 4, shafi: 399.
22. Wasa'ilusshi'a, mujalladi 6, shafi: 168.
23. Wasa'ilusshi'a, mujalladi 6, shafi: 169.
24. Wasa'ilusshi'a, mujalladi 6, shafi: 169.
25. Wasa'ilusshi'a, mujalladi 6, shafi: 169.
26. Wasa'ilusshi'a, kitabussala, abwabu kira'atul kur'an, babi 2, h 1, babi 3 h 1-3.
27. Kafi: mujalladi 2, shafi: 602.
28. Kafi: mujallafi 2, shafi: 600.
29. Wasa'ilusshi'a, mujalladi 6, shafi: 170.
30. Wasa'ilusshi'a, mujalladi 2, shafi: 600.
31. Wasa'ilusshi'a, mujalladi 6, shafi: 301.
32. Kafi: mujalladi 2, shafi: 598.
33. Wasa'ilusshi'a, kitabussala, abwabu kira'atul kur'an, babi 3, h 4-8.
34. Wasa'ilusshi'a: mujalladi 6, shafi: 172.
35. Wasa'ilusshi'a: mujalladi 6, shafi: 173.
36. Wasa'ilusshi'a, kitabussala, abwabu kira'atul kur'an, babi 4, h 1-4.
37. Manla yahaduruhul fakih: mujalladi 4, shafi: 399.
38. Kafi: mujalladi 2, shaif: 606.
39. Wasa'ilusshi'a, mujalladi 6, shaif: 675.
40. Kafi: mujalladi 2, shafi: 603.
41. Kafi: mujalladi 2, shafi: 606.
42. Wasa'ilus Shi'a, kitabussalat, abwabu kira'atil kur'an, babi 6, h 1-2.
43. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 6, shafi: 178.
44. Kafi, mujalladi 2, shafi: 604.
45. Kafi, mujalladi 2, shafi: 603.
46. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 6, shafi: 680.
47. Wasa'ilus Shi'a, abwabu kira'atil kur'an, babi 8, h 1-7.
48. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 2, shafi: 181.
49. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 6, shafi: 183.
50. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 6, shafi: 183.
51. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 6, shafi: 183.
52. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 6, shafi: 183.
53. Wasa'ilus Shi'a, babi 8, h 8-9.
54. Surar daha, aya: 125.
55. Surar daha: aya: 126.
56. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 6, shafi: 184.
57. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 6, shafi: 184.
58. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 6, shafi: 185.
59. Manlayahaduruhul fakih: mujalladi 1 shafi: 374.
60. Wasa'ilus Shi'a, babi 11, h: 1-5.
61. Kafi, mujalladi 2, shafi: 605.
62. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 6, shafi: 187.
63. Kafi, mujalladi 2, shafi: 611.
64. Kafi, mujalladi 2, shafi: 611.
65. Wasa'ilus Shi'a, babi 11, hadisi: 6-12.
66. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 6, shafi: 188.
67. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 6, shafi: 138.
68. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 6, shafi: 190.
69. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 6, shafi: 190.
70. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 6, shafi: 168.
71. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 6, shafi: 191.
72. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 6, shafi: 191.
73. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 6, shafi: 191.
74. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 6, shafi: 191.
75. Wasa'ilus Shi'a, babi 16, h: 2-8.
76. Kafi, mujalladi 2, shafi: 608.
77. Kafi, mujalladi 2, shafi: 608.
78. Kafi, mujalladi 2, shafi: 633.
79. Wasa'ilus Shi'a, babi 13, 14, shafi: 1-3.
80. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 6, shafi: 196.
81. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 6, shafi: 197.
82. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 6, shafi: 198.
83. Kafi, mujalladi 2, shafi: 609.
84. Tahzib, mujalladi 2, shafi: 138.
85. Iddatud'da'i: shafi: 287.
86. Kafi, mujalladi 2, shafi: 610.
87. Kafi, mujalladi 2, shafi: 498.
88. Kafi, mujalladi 2, shafi: 610.
89. Bihrul anwar: mujalladi 89, shafi: 200.
90. Wasa'ilus Shi'a, babi 17, h: 1-2.
91. Kafi, mujalladi 2, shafi: 612.
92. Kafi, mujalladi 2, shafi: 603.
93. Wasa'ilus Shi'a, babi 19, h 1- 4.
94. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 6, shafi: 204.
95. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 6, shafi: 205.
96. Kafi, mujalladi 2, shafi: 613.
97. Kafi, mujalladi 2, shafi: 613.
98. Wasa'ilus Shi'a, babi 21, h 1-5.
99. Muzammil: aya: 4.
100. Kafi, mujalladi 2, shafi: 610.
101. Kafi, mujalladi 2, shafi: 616.
102. Kafi, mujalladi 2, shafi: 207.
103. Kafi, mujalladi 2, shafi: 614.
104. Kafi, mujalladi 2, shafi: 606.
105. Kafi, mujalladi 2, shafi: 606.
106. Wasa'ilus Shi'a, babi 23, h: 1-3.
107. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 6, shafi: 209.
108. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 6, shafi: 210.
109. Kafi, mujalladi 2, shafi: 614.
110. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 6, shafi: 211.
111. Kafi, mujalladi 2, shafi: 615.
112. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 6, shafi: 612.
113. Wasa'ilus Shi'a, babi 25, h: 1.
114. Kafi, mujalladi 2, shafi: 616.
115. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 6, shafi: 614.
116. Kafi, mujalladi 2, shafi: 618.
117. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 6, shafi: 219.
118. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 6, shafi: 220.
119. Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 5, shafi: 84.